← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 66

Sashe 12

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Babu 6ata lokaci komai yagama kammala, aka kai su Ammi cikin Ambulance, dukda itad'in ta rasu, amma doctor Joshua yakasa fad'ama Uncle M.A d'in.
Amatallah kan a motar Uncle M.A aka sakata, haka sukatafi zuciyar uncle cikeda rauni, lokaci-lokaci yakan juya ya kalli Amatallah dake kwance a baya tamkar gawa....
*************
Tafiyar Awa 3
ce ta kaisu garin Kano, kai tsaye asibitin Aminu Kano suka wuce.
A cikin gaggawa kuwa aka kar6esu, saboda ansan da zuwansu, tunkan subaro jos Uncle M.A yakira doctor Shu'aibu ya sanar masa zuwansu. Wannan yasaka suka Tatar da komai a ready, su kad'ai ake jira.
Amatallah ma anbata gado, Dan har zuwa yanzun batasan ina kanta yakeba.
Sai da Uncle M.A yaga komai ya dai-daita sannan yatafi gidansu danya sanarma iyayensa.
Yana shirin shiga mota doctor shu'aibu yafito da sauri yana nemansa. hangosa dayayi yana shirin shiga mota yasashi fara kwala masa kira.
"Alhaji Muhammad! Alhaji Muhammad!!".
Harya saka k'afarsa d'aya ya fito, ganin doctor shu'aibu Na tunkaroshi da sauri sai gabansa yashiga fad'uwa.
Doctor shu'aibu yak'araso, "sorry Alhaji Muhammad Labbo! na tsaidaka, so dama.......
Sai kuma yay shiru.
"Ina jinka doctor, mike faruwane?".
Tsayuwa doctor ya gyara, sannan cikin damuwa yace, " sorry Alhaji Muhammad, ko kasan macen tarasu?, kamarma tun kusan a wanni 22 dasuka wuce".
A sanyaye Uncle M.A ke kallon doctor shu'aibu, ya dafe kansa dayaji yafara sara masa.
Hak'uri doctor yafara bashi, tareda lallashi da masa Nasiha.
Uncle M.A baice komaiba yashiga motar, kansa ya kifa a sitiyarin motar yafara hawaye. Kusan mintuna 7 sannan yad'ago, motar ya tada yabar asibitin.
______________________________

Tunda yashigo gidan Innani dake tsakar gida tana alwalar magriba kebinsa da kallo.
Jingina yayi da bango, batareda ya saniba hawaye suka fara bin kumatunsa.
Da sauri Innani ta k'arasa alwalar, "kai lafiyarka kuwa? Da girmanka kake kuka? Miya faru, yaushe kadawo ma?".
Yanda Ammi ta jero masa tambayoyin saiya samu kansa dakuma fashewa da kukan.
Shiru Ammi tayi tana kallonsa, jikinta sai rawa yakeyi.
Cikin d'an daka tsawa tace, " wai baka jinane?".
Share hawensa yayi, sannan yashiga bata labari.
Innalillahi ...... Kawai Innani ke iya ambata.
Baba na daga d'aki duk yanajinsu, saidai baya iya fitowa sai an fiddoshi, maganar Uncle M.A bak'aramin girgizashi tayiba kuwa.
Ana cikin haka saiga Jabeer yashigo shima, nan suka had'u sunata jimamin abin, jabeer ma harda kukansa rurus.
Bayan Uncle M.A yashiga sun gaisa da baba, shima yak'ara masa bayani sannan yatafi gidansa danya d'an kimtsa sannan yakoma kar Amatallah ta farfad'o babu kowa a kusa.......
.....
_Dan ALLAH ina rok'onku Ku ringa turama masu cigiya, saboda ALLAH banida time d'in turama kowa ta PC, amin afuwa saboda uzurina, hakanne zaisa nasan kuna k'aunata
One luv my fans
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_*
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
*_Duk naga comments naku, kuma sun k'ayatar dani gaskiga.
sai dai wani Abu yasakani dariya matuk'a, kunsan minene?. Masu cewa Uncle M.A yama Amatallah tsufa
*_Wai miyasa abinda zai iya kasancewa gaske Reader's ba kuson ganinshi a Novel's? Abinda na sani kuka sanine, ko a zahiri mai shekarun uncle M.A ba tsoho baneba, kisamu wani a anguwarku mai d'iyar dazata iya kaiwa 18years, tazam kuma itace d'iyarsa ta Fari ki k'iyasta dashi, ko Wanda yakai shekara 60 yana auren budurwa ai, balle 47years, kuma ko a cikinmu a kwai wad'anda mazajensu suka kai wad'an nan shekarun, my Abdull ma shekarunsa kenan
_mu rubuta abinda azahiri zai iya zama gaske kuce bai daceba, muyi Wanda mu da Ku kunsan bazai yiwuba Ku zagemu kuce muncika k'arya ko
_koma Yaya dai ALLAH yabar zuminci, Dan mu daku duk munacin amfanin junane, inba mai karatu babu abinda zaisa Marubuci 6ata lokacinsa, hakama inba Marubuci mai karatu bazai samuba littafinba, mun gode sosai, irin Trillion's d'innan
____________________
*_Number 10_*
____________________
An gudanar da zana'idar iyayen Amatallah a gidan mahaifan Uncle M.A, Innani tasha kuka lokacinda taga gawar Isma'il da matarsa a shinfid'e, lallai duniya batada tabbas ko kad'an.
Wandama ya d'aura d'ammara da ita saiya kwance.
Babama yashiga rud'ani sosai, dan sai da ciwonsa yayi tamkar zai motsa, sai allurar barci akai masa.
Har aka binne su Uncle M.A na kuka, koda suka dawo daga mak'abarta d'akin Jabeer yashige ya kwanta, kuka yake tamkar ransa zai fita.
Dolene ka gansa kaji tausayinsa. shima dai daga k'arshe dole allurar barcin Jabeer yasaka akai masa.
*_Two days later_*
Alhmdllh yau kwanakinsu Baban Ama biyu a k'asa, amma Ammi kwananta uku da rasuwa.
Duk da 'Yar Nutsuwa tazoma su Uncle M.A hakan bai hanashi warewa gefe yasha kukaba wani lokacin, musamman inyaje asibiti duba Amatallah da Nazeefa ke zaune da ita, dawata k'anwar Innani, gwaggo Rakiya.
Har yanzu Amatallah bata farfad'iba, dan doguwar suma tayi, amma tana samun kulawa daga likitoci sosai.
_______________________________
*_Jos_*
A jos kam lamari yayi k'amari, k'ank'anin Abu yajawo mutuwar d'aruruwan al'umma da asarar dukiyoyi, abinda yafaru akan SIYASA dalilin wasu marasa jin magana ya rikid'e yazama fad'an k'abilanci da addini.
'Yan jaridu da kafafan yad'a labarai na social media sai baza rahotannin k'arya sukeyi, anrasa jin jinar magana akan dalilin wannan rikici na *SIYASA KO K'ABILANCI!?*.
A dalilin hakan kuma wasu gur6atattun matasa masu ruguza zaman lafiya suka kuma tada rikici a KADUNA, ik'irari sukeyi wai ankashe 'yan uwansu dake jihar Jos, dolene suma su d'auki fansa.
Ba'awani ja danisaba Kano ta d'auka, babu gaira babu sabar nanma wasu bara gurbin matasan suka haikema wasu k'abilu dake killace awata anguwa da ik'irarin d'aukar fansar abinda akaima 'ya uwansu a Kaduna da jos.
Abinda yafaru a kano yabama k'abilun kudancin k'asar suma tada tasu husumar, suka fara kisan 'yan arewacin k'asar a nufin d'aukar fansa
_hum wane irin tunanine da matasan k'asarmune? Mike shiga kanmune? Muke za6ama kammu da k'asarmu irin wannan rayuwar? Wace riba mukeci ko nasara idan mun girmama irin wannan rikice-rikicen dabumuma San tushensuba, karfa Ku manta idan ta rikice da kai da ni duk bazamu shaba, ahalinka da nawa babu Wanda zai tsira, dukiyar k'asarmu zata ruguje, karatunka danawa Dana 'ya'yanmu duk zai zama labari, watak'ilma kaida kazama jagoran fad'ad'a tashin hankalin kaine zaka fara mutuwa ko ahalinka, Ku kalli gagis, zike, k show, dasu aka fara, an tarwatsa ahalinsu da basujiba basu ganiba, Amatallah dabatasan tushen rikicinba an rabata da iyayenta, an tarwatsa mata family saboda son zuciya irinna gur6atattun matasanmu, wad'anda mugun tunaninsu bayasa mu d'aukesu a jerin masu amfani da amfanar da k'asarmu, basuda buri saina haddasa rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI!?* Saboda son zuciyarsu, kullum zuciyarsu na karanta musu AMUTU KO AYI RAI ba damuwarsu baceba, da ance an kad'a tambarin SIYASA saikaga jikkunan matasan k'asarmu na rawar Mazarin shirye-shiryen duk yanda takama, basuda zuciyar k'yak'yk'awan fata wa k'asarsu ko nagartar ginata ta hanyar zarran mazatankar samartaka na k'uruciya da ALLAH yabasu. miye ribarka idan an siyeka dawasu 'yan kud'ad'e dankayi jagoranci wajen hallaka ahalinka da k'asarka? Wadda bakada kamarta, bakada Inda yafita, duk Inda zakaje saikazama abin tsangwama da gudu , watak'ilma akiraka d'an ta'adda mai lasisi, bakada damar shan ruwan wata k'asa cikin salama tunda ba k'asarka baceba._
Yanzu haka wad'anda suka baka kud'in duk 'ya'yensu basa k'asarma, sannan su sunada tsaronda babu wani mahalukin daya Isa ya tunkari gefen anguwanninsu ballema yasamu ganin su, amma kai anbaka kud'in siyen ahalinka batareda kayi dogon tunaninaba, basuda Matsala da watsewa ko tarwatsewar k'asar, dan sunada isassun kud'ad'e a ciki da wajen k'asar, sunada lasisin zuwa kowacce k'asa su warwasa batareda an tsangwamesu ba kamarkai daza'a kafama tantin d'akunan tamfol ko buhu ko katako a filin ALLAH ana kiranku da suma *'YAN GUDUN HIJIRA*
Abincinma dazakaci ko ruwa saiya gagareka, ballantana maganar lafiyarka ko akasinta.
Haba matasanmu, kudawo cikin hankalinkufa, kubar yadda da 'yan jari hujja masu amfani daku wajen amfanuwarsu suna haddasa fad'ace-fad'acen addini ko SIYASA da K'ABILANCI ta sanadinku, ni da ku damuke a arewaci da kudanci duk munada ikon canja mummuna zuwa k'yak'yk'yawa, duk Wanda kagani Asama mune muka kaishi, kuma munada ikon ingizoshi k'asa ayayinda muka fuskanci d'an wawasone akan abinda yake mallakinmu, da wahalhalinmu suke tak'ama da baza riguna da cin zarafinmu suna zare idanu, to muma saimu gyara domun gyaro abinda ke cin dunduniyarmu, mukiyayi saidai RAYUWARMU akan rikicin SIYASA KO K'ABILANCI da wasu tsiraru ke jagorancin haddasa mana domin cimma wani burinsu akanmu, sai matasanmu sunyi gyaran halayensu sannan madafun iko da ragamar k'asarmu zata iya dawowa hannunsu
Wannan k'alubalen nakune matasanmu
Amma ta sanadin zaman lafiya a k'asarmu da muhimmin sanin darajar kawunanku, kuyi fatali da duk wani banbancin addini ko k'abila kuzo mu rungumi juna domin kawo sauyi wajen tankad'e da rairayar duk wasu masu rusamu ta k'ark'ashin k'asa, karike na rike ki rike mu rike hannun juna domin maida matasanmu jagorori akan madafun ikonmu
. Ta hanyar zaman lafiya da k'aunar junanmu cikin zarrar amsa suna 'yan *NIGERIA* k'asa d'aya, uwa d'aya uba d'aya.
Karmu bari mu ruguje daga ansa sunanmu na 'yan k'asa d'aya dalilin *SIYASA KO K'ABILANCI*
Ko shed'ancin wasu jagorori masu nemawa Kansu mutunci kawai
a wannan ga6ar dolene masu karatu susojin dangan takar dake tsakanin Alhaji Isma'il Uba da Alhaji Muhammad.
Kubiyo bilyn Abdul domin jin tushen labarin.
____________________________
Alhaji Muhammad Ahmad Labbo, shine cikakken sunan Uncle M.A.
'Dane na farko daga Alhaji Ahmad Labbo.
Alhaji Ahmad Labbo cikakken basakwace ne d'an kasuwa, kasuwancine yakawoshi garin Kano, a da yakanzo ya sari atanfofi yakoma sokoto, sai dai daga lokacin da tafiya tafara nisa saiya dawo garin na Kano baki d'aya, yasamu shago a kasuwar kwari.
A nan Kano ALLAH yahad'ashi da matar aure Zainab (innani).
Shekararsu 1 da aure ALLAH ya albarkacesu da haihuwar d'a namiji, Wanda yaci sunan Muhammad (Uncle M.A kenan). bayan Muhammad innani tasake Maijiddah, sai Barirah, (amma ALLAH yay mata rasuwa), sai Jabeer,, Shehu, Nazeefa auta.
Gwargwadon iko 'ya'yansu sunsami tarbiyya, sannan sun tsaya tsayin daka domin ganin sun sami ilimin addini dana zamani.
Muhammad yarone dayataso k'ark'ashin kulawar mahaifi, dan innani tana kawaici sosai alamarinsa irinna 'ya'yan Fari, bata fad'ar sunansa, sannan kuma bakomaine take sakashi acikiba
Amma a k'asan zuciyarta tana matuk'ar k'aunarsa fiyema da sauran 'ya'yanta.
Bayan kammala primary d'in Muhammad yadage akan boarding yakeson zuwa, babu yanda iyayensa suka iya suka shiga cuku-cukun kaishi Government secondary school Bichi.
A canne ALLAH ya had'ashi da Isma'il Uba Salisu, Wanda rana d'aya aka kaisu makarantar, shi an kawoshine daga Kusada local government dake jihar Katsina. tun daga wannan ranar suka k'ulla alak'ar abota mai k'arfi, suna kiran junansu brothers.
Kowa a makarantar ya d'auka 'yan uwan junane makusanta saboda k'auna da tattali dasuke nunama juna.
Ko kad'an Muhammad baya k'aunar yaga anta6a Isma'il, haka shima Isma'il d'in, idan aka kama d'aya da laifi, akazo hukuntasa sai d'ayan yay tsale yace shine, dan bayaso ata6a lafiyar d'an uwansa. idan kuwa d'aya bashida lafiya ai saika d'auka dukansune suke jiya. gaskiya akwai k'auna mai k'arfi a tsakaninsu mai kuma ban mamaki.
Kafin kace mi duk families nasu sunsan da wannan k'auna tasu. har yazam Isma'il kanzo Kano Hutu gidansu Muhammad, haka shima Muhammad kanje jos ko kusada hutu........
Isma'il Uba salisu shine cikakken sunan Baban Ama, d'an asalin jihar jos ne, Dan anan yataso yaga iyayensa,
Su biyu iyayensu suka Haifa, Amina itace babba, sai Isma'il. tun suna k'ananu mahaifiyarsu ta rasu, babansu wanda suke kira da kawu yak'ara auren wata makirar mace mai suna Huzaiyya, takan nuna k'aunarta a garesu agaban mahaifinsu, amma dazarar bayanan tashiga gallaza musu kenan, makircinta yahana kawu fahimtar komai akansu. ana haka ALLAH ya fiddoma da Amina miji, amma fatauci yake zuwa jos shi d'an katsina ne a kusada L.G. wannan yasa koda akai aurenta sai aka kaita Kusada.
Tunda Amina tayi aure sai Isma'il yakuma shiga uk'ubar huzayya, wannan yasakashi tada hankalinsa akan shi akaisa wajen 'yar uwarsa Amina. Mahaifinsu bai fahimci komaiba, shi duk tunaninsa Isma'il na kewar Amina ne. Haka ya d'akko Isma'il da kansa yakawoma Amina danufin yayi hutu. Sai dai koda hutun Isma'il ya k'are saiya dage akan bazai komaba, kawu yay lalla6ar duniya Isma'il yace bai komawa. haka dole kawu yabar Isma'il awajen Amina.
Mijin Amina ne ya nemawa Isma'il makarantar boarding ta Bichi danya cigaba da karatunsa, tunda yagama primary a jos.
Daga wannan lokacinne kuma suka had'u da Muhammad labbo, Wanda yazame masa d'an uwa kuma aboki.
Idan anyi Hutu Isma'il yakan fara zuwa kusada ne yay kwana biyu sannan ya wuce jos. Wani lokacin kuma a kano yakeyi gidansu Muhammad, a wani karon kuma su wuce jos shida muhammad d'in suyi acan bayan sunje kano, kokuma kowa yatafi gida, sai bayan kwanki kamar uku zuwa hud'u saiya tafi gidansu d'an uwansa hutun. har lokacin kuma Amina bata haihuba.
Chapter 12 · 0% Book details