Sashe 33
Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amatallah tunda tafito wanka taji kamar k'amshin turaren Uncle, gabantane ya fad'i, cikin sand'a ta lek'a falo azatonta yana can, ganin wayam babu kowa tasaki ajiyar zuciya sannan tadawo. Zani ta d'aura tasaka hijjab tayi shafa'i da wutiri, idarwarta kenan tacire hijjabin ta d'ora saman gado, tabud'e Waldrop danufin Neman kayan barci yay sallama, ba k'aramin tsorota tayiba da ganinsa, taja hijjab d'in data cire tasaka da Sauri duk da yama Rigada ya shigo d'in, Yakuma ganta a yanda bata son. Murmushi kawai yayi, ya k'arasa bakin gadon ya zauna. Kanta a k'asa tamasa sannu da zuwa. Idonsa a kanta yace, "yauwa my best! Kin daina kukan tafiyarsu Nazeefa ne?". Kwallace tacika idonta, ta d'ago kad'an ta kalleshi ta duk'ar da da kanta. "Kukan dai kuma?". Girgiza kai tayi da sauri. Zamansa ya gyara yana nunu mata kusa dashi, " zoki zauna naji to". Dukda tanajin kunya haka ta zauna amma d'an Nesa dashi. Idonsa akan yatsun hannunta dake d'aukar hankalinsa yace, "to, ya school?". " Alhmdllh Uncle". "Masha ALLAH, babu dai wata Matsala ko?". Kanta ta girgiza masa da fad'in " eh uncle". "Alhmdllh ai haka akeso, zuwa da safe Na duba Nagani idan da gaskene, yanzu alfarma nazo nema". Cikeda mamaki ta kalleahi, " uncle! Alfarma kuma? a wajena?". Kansa a jinjina mata fuskarsa d'aukeda guntun murmushi. "Alfarmar kwananki nake nemama Aneesa". Ko kad'an Amatallah bata fuskanci inda maganarsa ta dosaba tace, Uncle ban ganeba ai". Shiru yayi yana nazarin tayaya yakamata yamata bayani, sai kuma yamatso kusada ita sosai, hakanne yad'an sakata jin tsoro heartbeat d'inta Na k'ara gudu, kamar zatayi magana saikuma tayi shiru. Duk da ya fuskanceta hakan bai hanashi kamo hannunta ba ya saka a nasa, " uhm INA nufin kibari yau Aneesa ta kwana d'akina". "Wayyo Uncle, ni mizai sakani Na hana Anty Aneesa kwana d'a......." Saikuma takasa k'arasawa saboda maganar Tamata nauyin fad'a. 'Dan murmushi yayi, aransa yace tunda kinsan ma'anar kwana d'akin nawa, a hankali abinda nake nufinma zaki gane ai. a fili kuma yace, "Nasani bazaki hanataba, amma hak'inkine ai". Zuwa yanzun kam Amatallah tagama fuskantar Inda Uncle d'inta ya dosa, amma nauyin maganar bazaisa ta ta6a nuna masa ta ganeba, saima mamakinsa take a zuciyarta dukda shima azancen NASA akwai salon alkunya tunda bai fito kaitsaye ya nuna mata manufarba....... Katseta yayi da fad'in "kinyi shiru Khadija". " Uncle nidai dukda bansan miyasa kake son hakanba Na amince ta kwana wlhy". Tayi maganar a kunyace. Murmushi yayi tareda sumbatar bayan hannunta, yace, "ALLAH yay mini albarka Khadija". Shi duk zatonsa Amatallah da gaske bata gane Inda ya dosaba, Dan kallonsa k'aramar yarinya shataf yake mata. Nidai nace, " hummm Uncle kenan, shekarar Amatallah 20 yanzu ace batasan miye aureba?, bayan yanzun yaramu sai dai addu'a, 'Yar shekara 15 saita baka labarin mi ake a gidan aure tsaf, in kayi wasa takuma fad'a maka komai dalla-dalla, ai waya babu masifar dabata kawo manaba a wannan zamanin, sai dai kawai wad'anda ALLAH ya tsare, amma jeka Facebook kawai kaga ta6ar6arewar tarbiyyar yaranmu. Kama godema ALLA daya baka Amatallah d'in mai kunya, yanda idanun 'yan matanmu ya bushe yanzu suka d'au kunya k'auyanci ai abin ba'a magana, ALLAH dai ka shiryamana zuri'a kawai. Mik'ewa yayi yana fad'in "tom tashi ki kwanta namiki addu'ar barci". Kanta a k'asa tana cigaba da wasa da yatsun hannunta tace, " Uncle ai bansa Sleeping dress". "Okay, to tashi kisa ka". Shiru tayi kamar bazata tashiba sai kuma ta mik'e ta koma wajen Waldrop d'inta ta ida zaro kayan data fara d'auka d'azun. duk Uncle yana tsaye yana kallonta. toilet d'inta tashiga dan ta Sanka. Murmushi yayi yana shafa gemunsa, a ransa yanajin k'aunar Amatallah da yanda take komanta a nutse, wani lokacin idan tayi Abu yakanga tamkar brother d'insa (to jini ba k'arya baneba aii Uncle). Yana nan tsaye harta fito, kallonta yayi, dukda tasaka Riga da wando na barcin, hakan bai hanata sanyo hijjabin ba a sama. Tsaye tayi a bakin k'ofar kanta a k'asa. Yace, " zoki kwanta mana, ko zakiyi wani abunne kuma?". Kanta ta jinjina masa alamar a'a. "Ta kowa yayi a hankali har inda take, ya kama hannunta batareda yace komaiba, har gaban gadon sukaje sannan ya saki hannunta yana nuna mata gadon da yatsa. Bata yarda ta kalleshiba ta hau gadon ta kwanta bayan ya gyara mata filon. bargo yaja ya lullu6a mata zuwa k'irjinta sannan ya rankwafo saitin kanta daf. ita dai Amatallah kallon ikon rabbani takeyi, da girmanta an maidata baby. Hannu yasa cikin bargon kad'an yafara tattara hijjabin jikinta, a hankali ya furta "d'aga my best a cire wannan hijjab d'in, babu k'yau kwanciya da hijjab, zai iya kawo matsala ga mai barci, kamar shak'e mutum da makamancin hakan". Kanta ta jinjina masa a hankali, Dan yanda ya rank'wafo kanta saitaji kamar zai fad'o mata, har saukar numfashinsa tanaji, taimaka masa tayi yacire hijjabin, kafin ya ida cirewa tayi saurin Jan bargon ta rufe k'irjinta. Yana kallonta, dan haka yay dariya a zuciyarsa kawai. yana gama cire mata hijjabin ya ajiye gefe ya zauna kusada ita a bakin gadon. addu'oi yamata kamar yanda yakema sauran matansa, ya tofa mata a hannu ta shafa itama da wanda tayi, mik'ewa yayi yasake rankwafowa ya gyara mata bargon, sannan yamatso da fuskarsa daf da tata, hakanne yasaka Amatallah saurin rintse ido dad'an k'ank'ame jikinta zuciyarta tana kuma bugawa da k'arfi saboda kusantowarsa garesa sosai. Kiss ya manna mata a goshi da kumatu, sai kuma ya dakata yana kallon fuskarta da yanda take k'ara k'ank'ame ido, yanda tayin saita bashi dariya harya murmusa, yace, " bud'e idon mana my beat ki kalleni". "Ya salam" tafad'a a zuciyarta tareda mamakin wannan lamari na Uncle, tana masa kallon salihi Ashe shima A ne na bugawa a jarida....... Batakai k'arshe. Tunanin taba taji saukar la66ansa akan nata. A zuciyarta tace na shiga tara ni Khadija, Uncle zaka kasheni da kunyarka wlhy. Saida ya sumbaci la66anta sau biyu sannan yamik'e tsaye sosai yana murmushi idonsa a kanta face d'inta. "Sai da safe my Heartbeat! ko kawai nashigo bargon mu kwanta abinmu, mu warware sadaukar da kwanan?". Bargon taja da sauri tarufe har kanta gaba d'aya. K'aramar dariya yayi yamatso kamar zai bud'e mata bargon, murya k'asa-k'asa cikin rad'a kamar mai tsoron ajisu yace, " Ina matuk'ar Sonki keda Salonki my best Darling. goodnight, zan kwana da mafarkinki". Bai jira cewar taba yakama hanyar fita, yamasan bazata ceba d'in, fitilar d'akin ya kashe ya fice, bayan ya kunna fitilar wayarsa. 6angaren Aneesa ya komai, tana nan kwance yanda ya barta, tayi kuka harta godema ALLAH, bai mata maganaba ya d'auki Saifudden ya fita, wajen Fateema ya kaisa, dukda barci takeyi abinta hankali kwance itada yara, haka ya shinfid'eshi kusada 'yan uwansa yamasa addu'a sannan ya koma wajen Aneesa. yanzuma yanda yabarta haka ya isketa, ya d'auke Siddiqa daga gabanta ya gyara mata kwanciya gefe saboda gadon babbane ba laifi. Duk abinda yakeyi Aneesa na jinsa, tun shigowarsa ta farko har d'aukar Saifudden ya fita dashi, ko kad'an batayi zaton Amatallah zata yarda ya dawo wajen taba, anya idan itace zata iya kuwa? sai taji Amatallah ta birgeta..... Ajiyar zuciya ta saki yayinda taji ya rungumeta. Hummm, nayi nan, Dan yau Uncle da neesarsa babu sauk'i. Tumda Uncle yafita Amatallah ta sauke ajiyar zuciya a fili tace, ''kai Namijima sai abarsa, duk yanda kake kallonta a nesa ba haka bane, saika zauna dashi kake gane Natural colour d'insa, wlhy a baya idan wani yacemin haka Uncle Muhammad yake saina k'aryatashi, humm Ashe ya wuce tsammanina ma". Hannu takai ta shafa bakinta, saikuma taja bargo da sauri takuma rufe fuskarta tana rintse ido da fad'in ''wayyo Uncle Muhammad ka kasheni wlhy, yanzu tayaya zan iya kallonka da safe?, shikenan na mutu ni Amatallahin Ammi da baba". Haka taita sambatunta ita kad'ai, hardai barci yazo mata, takuma 'yan addu'oi ta gyara kwanciya............. Ni dai mai d'aukar rahoto nayo waje ina dariya wa shirmen Amatallahin ku _Nasan saboda yawan page d'in nan yau har saikun kai jibi kuna karantawa , kusan Read more 7 fa , asha karatu lfylfy._ One Luv my sweet fan's *_ya ALLAH ka gafartama mahaifina._* [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing *_HASKE WRITER'S ASSO..._* _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce *_Hummm, jiyakam ai magana gagarata tayi a kowanne groups, dan jiya kad'an garage nasha Suburbud'a hannunta masoyan Amatallah , Aneesa zata jamin jaza'i, nibada laifiba Haba masoyan Ama..., karku damu zaku fanshe ne ____________________ *_Number 23_* ____________________ Koda Uncle ya koma gida ya taradda Fateema kawai a falo, Aneesa kam tana 6angarenta. Gaban Fateema ya k'arasa ya sumbaci Goshinta da cikinta, d'agowa yayi yana dariya da fad'in nabiya bashi my tee... Itama dariyar tayi tana fad'in kafita koba sabulu". zama yayi inda Aneesa ta had'a break fast, batareda ya nemetaba yazauna yaci kad'an kamar yanda ya saba. Fateema kam dad'ine ya kamata, tasan cin abincinnan dayayi bai nemi Aneesa ba saitayi tamkar ta fashe dan haushi. Yana hayewa samansa itama ta tashi tashige 6angarenta, dama da biyu ta zauna falon. ********* Amatallah bayan sun fito lecture suka nemi waje can gefe suka zauna suna sauraren ta. A nutse tabasu labari tana kuka, suma sunayi, aka rasa mai lallashin wani cikinsu, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru suna bama Amatallah hak'uri, sosai suka tausaya mata. Itama Rita tace zata basu labarinta gobe. Duk suka amsa da ALLAH ya kaimu. Amatallah tanason tambayarsu maganar da Aneesa ta mata da safe, amma tana ganin kamar suma bazasu fahimtaba, musammanma su Goodness, dan haka tayi shiru da nufin zata tambayi Fa'iza ita kad'ai. Suna fitowa lecture ta k'arshe Goodness da Rita suka nufi hostel, yau basu musu rakkiya ba saboda kowa yagaji. Da wannan damar Amatallah tayi amfani ta sanarma Fa'iza abinda yafaru tsakaninta da Aneesa, dakuma tambayar da Uncle yamata ta 6oye masa. Kallon mamaki sosai Fa'iza kema Amatallah, tace, "dama bakida wayo haka Amatallah?. Wace mace ke sadaukarma kishiya kwananta? Sai dai haihuwa ko lalura wlhy, Lallai bakisan miye kishiba Ashe. Wlhy duk da kike ganina k'aramarnan bana bari kishiya tasamu lagona, bazanyi kishin haukaba kuma bazan raga mata ba". " ban ganeba Fa'iza, kema kinada kishiyane?". Dariya Fa'iza ta mata, "lallaima Amatallah, koda yake duk yandafa muke dake