← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 66

Sashe 10

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abin mamaki washe gari da safe sai ga labarin kisan gagis yafito, anje har cikin asibiti da daddare anmasa yankan rago.
Kai tsaye kowa su zike aka zarga, musamman da akasan tushen abinda ya kwantar da gagis asibitin.
Humm, amma abin tsoro da ALLAH wadai sai aka nemi su zike aka rasa a cikin jos, Ashe suna gidan Mr Pam yabasu mafaka, bayan sungama tsara masa k'arya da gaskiya akan su gagis sunason 6ata siyasarsane shiyyasa suka kasheshi.
Sosai Mr Pam ke hura hanci da banbamin masifa akan k'are Duk wani dayace zai kawoma siyasarsa togaciya dolene a 6addashi, koda kuwa abokan takararsane.
A daren ranar yadank'ama su zike makamai masu had'ari sosai, wai surik'e domin kare kansu. sunyi farin ciki sosai da wannan k'yauta, dan aganinsu k'arin k'arfin guwwane agaresu.
Nidai nace, "hummm".
____________________________
Tunda sassafe Baban Ama yay shirin tahowa asibitin, danya kar6i Ammi taje tai musu girki.
Alhmdllh yatadda jikin Amatallah da sauk'i, jiya kuma firgitar kad'an tayi, sai dai zazza6i mai zafi data kwana dashi, dukda Magani da akabata bai saukaba, haka taita sambatu da kiran sunan Ammi da babanta.
Lokacin da babanta yake fitowa saiya ci karo da uncle M.A, babu irin rok'onsa dabaiyiba akan yay kwanciyarsa yak'ara hutawa zuwa anjima amma yak'i, yace suje tare kawai asibitin su kar6i Ammi.
Haka suka taho badan baban Ama yasoba.
Sun iso Amatallah Na barci, saboda batayi barcin dareba, bayan sun gaisa da Ammi tawuce gida sukuma suka zauna hira.
Kusan 9:30 Ammi takirasu akan sutaho tagama.
Har lokacin Amatallah Na barci.
Ammi tataho sukuma suka tafi,
Suna kammala cin abinci suka tafi k'auyen da zasu kar6o maganin baba.
Basu dawoba sai misalin 2:38pm. kai tsaye asibitin suka nufo.
Amattalah na zaune a kan gadon datake jiyya, abinci takeci tana hawaye, ga likita tsaye agefenta yana kallonta yana murmushi shida wata Nurse, Ammi kuma Na a bakin gadon zaune tahad'e fuska tana fuskantar Amatallah, da Alama itace ta tsareta takeci abincin.
Cikin gur6atacciyar hausar likitan yace, "Ametala please mana, stop crying, baka sen kai babba baniba? amma kinama common injection kuka? randa zakaje labour room kuma fa iye?......"
Banza Amatallah tamasa, jitake kamarma ta bugeshi dan haushi, shigowar su baba yasaka doctor da Ammi kallonsu, duk suka amsa sallamarsu.
Uncle M.A yak'araso da d'an sauri yana tambayar lafiya? Amatallah ke kuka?".
Doctor ne yamasa bayani akan sunason mata allurane saboda zazza6i yak'i sakinta, to gashi bataci komaiba kuma, shine yace tad'anci abinci kafin sumata. tace tak'oshi, Ammi ta tsareta saitaci, wannan ne dalilin kukan nata.
Babantama dariya abin yabashi, dan haka yay dariya kad'an, can k'asan ransa kuma yanamai jin tausayin d'iyar tasa tilo, sai dai bai San daliliba, tunda safe dasukazo ya kalleta yaji kwalla sun cika idonsa, haka kawai yau yawayi gari da k'ulafucin tunaninta da tausayi.....
Ajiyar zuciya yasaki, yayinda ya tsinkayo muryar uncle M.A Na lallashinta.
Bai ce komaiba, saima gefen Ammi daya koma ya zauna yana kallonsu cikin wani yanayi, ita kanta Ammi kallonsu takeyi a wani iri.
Da lalashin uncle M.A akasamu Amatallah taci abinci aka mata allura. tun tana hawaye har barci ya d'auketa, suduka ajiyar zuciya suka saki, kafin su tashi su fita zuwa gida cin abinci, sukabar Ammi Na gadinta, lokaci-lokaci masu dubiya k'awayen Amattalah da makwafta da 'yan uwan Ammi Na zuwa.
____________________________
Gab da magriba Baban Ama yakira Ammi akan tazo gida tabashi wasu takardu daya bata ajiya.
Tayi d'an Jimm kafin tace, "to Baban Ama wazai zauna da ita? gani nake bai dace nabarta ita kad'aiba anan.
Ajiyar zuciya Baban Ama ya dauke, kawai saiyaji idonsa yacika da k'walla, zuciyarsa tayi rauni, a sanyaye yace, " karki damu, ga Brother nan yataho wajenta, idan kika d'akkomin saimu koma asibitin tare ni da ke".
Kanta ta jinjina tamkar tana a gabansa, tace, "to ganina zuwa".
Amatallah na kwance tanajin Ammin ta, jitayi bata k'aunar tafiyar Ammin, bayan Ammi ta yanke wayar Amatallah ta kalleta, hawaye taf da idonta tace, " Ammi ki kwatantama baba inda takardun suke saiya d'auka basai kinjeba". tak'are maganar da zubda kwalla.
Kallonta Ammi tayi, tana mamakin miye abin kuka anan? daga dai zuwa d'akko takardu tadawo.
Matsowa tayi jikin gadon, ta dafa kan Amatallah tana murmushi, "haba Khadija miye abin kuka to? yanzufa zanje na d'auka masa mudawo, kiringa hak'uri da rayuwa Khadija, wannan k'ulafucin namu dakikeyi ki ragesa, karfa ki manta akwai mutuwa, kuma ke d'iya mace ce, wataran aure zakiyi kibarmu dole, kizama mai hak'uri kinji, komi kike tunani, koya cutar dake, koya sakaki rud'ani, to kisaka *HAK'URI* agabansa, insha ALLAH zaki zama mai riba a duniyarki da lahira..........
Sallamar Uncle M.A ce takatse Ammi........, shiru tayi tareda janye hannunta daga kan Amatallah, ta amsa sallamarsa, ya tambayi jikin Amatallah, tace da sauk'i sannan tafita.
Har taje k'ofa tajuyo takuma kallon Amatallah dake binta da kallo itama, jiki a sanyaye tafice zuciyarta na k'una.
Kawai sai Amatallah ta fashe da kuka.
da sauri Uncle M.A yak'arasa inda take yana fad'in " subahanallahi, My Best miya faru da kuka kuma?".
Kasa bashi amsa tayi, tacigaba da raira kukanta.
Kusada k'afafunta ya zauna yana lallashinta, shikansa gabansa sai fad'uwa yakeyi, gawata matsananciyar fargaba da yakeji tunda safe, harma zuciyarsa tana raya masa ko jikin babane?.
________________________________

"Ka tabbatar kayi kamar yanda nace, karka bari asamu kuskure fa".
"Oga karka damu kanka, kasaka aranka kawai sun wulla, itakuma bab.. d'in tana hospital, hawan k'awara yakamata mumata da daddare".
" karka damu, kaje afara wannan aikin first."
"Okey sir, babu damuwa".
_______________________________

Cikin mintuna k'alilan Ammi ta iso gida, a k'ofar gida sukayi kici6is da baba zaitafi salla, tashiga shikuma yanufi massalaci.
Ramzaki dake la6e bayan wani kwano da aka zagaye bishiyar mangwaro yafito, da sauri yashige cikin gidan, babu Wanda ya lura dashi saboda duhun magriba daya fara, gakuma garin da alamun hadari ma.
Ko kad'an Ammi bataji motsin shigowaba, tayi alwala tashige ciki. duk Ramzaki Na la6e yana kallonta. sai da yaga tashiga falon sannan shima yashigo cikin gidan sosai.
Bayan kamar mintuna biyu ya tabbatar Ammi ta kabbara salla. Sad'af-sad'af yashiga cikin falon.
Tabbas Ammi taga shigowar sa cikin falon, amma taza6i cigaba da sallarta, dan duk tunaninta 6arawone, hartayi raka'a d'aya yana tsaye a kanta, kallo yake k'are mata sama da k'asa, duk da gefen zuciyar Ammi ya tsorata, amma ta daure batabama shaid'an damar cin galaba akantaba bare ta sallame sallar.
Ramzaki sai da yabari tayi sujidar k'arshe sannan yazaro wuk'arsa daga k'ugunsa, dai-dai lokacin dazata d'ago ya soka mata wuk'ar a gefen cikinta na haggu.
Babu shiri Ammi takoma Sujudar datayi niyyar d'agowa, maimakin tayi ihu saita fara ambatar "La'ila ha illallah, muhammadarrasulullah, hazbinallahu wa ni'imal wakil". Wannan shine abinda keta fitowa daga harshenta, har Ramzaki ya zare wuk'ar, yadawo d'ayan gefenta yakuma sokawa.
Hawayene masu zafin gaske suka fara kwarara a idon Ammi dake a sujuda har yanzun, Ramzaki nakuma zare wuk'ar saita zube kawai awajen, la66anta dake motsawa suna kalmar shahada har yanzu nake kallo.
*_Masu karatu nikaina ina cikin rud'ani, wannan rashin imani har INA.
Ramzaki Na tsaye akan Ammi har tagama shure-shure, numfashinta yakoma fita a hankali.....
Dai-dainan baba yashigo gidan, da sauri Ramzaki yakoma bayan labule ya 6oye.
Baba yashigo cikin tsokana yana ambatar " Uwargida ran gida! kina ina? Zokiga angon gobe........
Maganarsa ta mak'ale a mak'oshi saboda ganin jini Na mamalowa daga inda Ammi ke kwance, kasa motsawa yayi inda take, yabi jinin da kallo kafin ya maida kallonsa ga Ammi, takawa yayi a hankali har inda take kwance.
Da sauri Ramzaki ya kwantar da gallon d'in fetur d'in daya shigo dashi, sad'af-sad'af yafice a falon.
Fetur d'in yafara malale falon.
Durk'ushewa baba yayi a gaban Ammi, yakama hannunta na haggu data dafe gefen cikinta na dama dashi, a hankali yad'aga hannun, soyake ya tabbatar daga nannne jinin ke zuba ko kuwa?.
Idanunsa yazaro, Dan ganin yanda jini ke 6ul-6ula, muryarsa na rawa yashiga kiran Saliha! Saliha!!, ke Saliha!!..........maganarsa mak'alewa tayi saboda ganin hasken huta, yajuyo a sanyaye.
Kasa motsawa yayi, yay sagade yana kallon wutar dakeci afalon, tanabin duk inda fetur d'in ya ta6a. ko kad'an baiyi yunk'urin motsawaba, saima matsawa dayayi jikin gawar Ammi ya kwantar da kansa bisa fuskarta ya fashe da kuka.
A hankali wutar tafara k'arfi, dan har kujeru sun fara kamawa, duk da zafin wutar na dukan baba yakasa tashi, motsin kirkima yakasayi awajen, jiyake tamkar an d'auresa da igiya. Sannu a hankali wutar ta iso inda yake, tuni numfashinsa yafara sark'ewa saboda hayak'in wutar.
Hankalin 'yan anguwa yafara dawowa gidan baba, saboda ganin hayak'i tasaman zinc.
Wanine ALLAH ya nuna masa fitowar Ramzaki daga gidan.
Ihu yafara yana nuna Ramzaki.
Ramzaki naganin haka yakwasa da gudu, hakanne ya tabbatarma da mutane baida gaskiya. nanfa wasu matasa suka rufa masa baya domin kamashi. wasu kuma suka afka gidansu Amatallah dan ganin mike faruwane?.
Lokacin dasuka fara shigowa baba harya suma, Dan numfashinsa ya gagara fita, hayak'i ya sark'eshi, wutarma tafara bin kayansa shida Ammi.
Ihu mutane suka fara tareda d'aukar botikan ruwan dake tsakar gidan suka fara watsawa k'ofar falon, amma wutarnan kamar sake izata akeyi.
Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un.
Wutarnan batada niyyar mutuwa ko kad'an, wannan yasaka wasu fara Neman 'yan kwana-kwana. duk da haka kuma anata watsa ruwa, makwafta sai kawo ruwa sukeyi.
Chapter 10 · 0% Book details