← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 66

Sashe 37

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tunda ta fito a motar wasu daga d'aliban suka saka mata idanu, hardasu Fa'iza.
K'arasowarta yasaka Rita fad'in "baby ke da waye yau? muntafi tarbanki mukaga ba ya Jabeer bane".
Da sauri Amatallah tace, " uncle d'inane".
Fa'iza dake zaune da tsohon cikinta tayi dariya, danta kuma gaskata Amatallah nada aure yanzun..... Kafin tayi magana Goodness tace, "Amatallah anya Uncle d'inan ba mijinki baneba?".
Harararta Amatallah tayi batareda tace komaiba.
Aiko suka saka mata dariya, Fa'iza ta yunk'ura ta tashi dagyar tana kallon Amatallah, " to 'yammata ai yanzu munsan komai, sai a daina raina mana wayo, aini wlhy tundaga yanda kike amsa masa waya nasan yawuce Uncle kawai, yaukuma munga zahiri, dan yanda yarik'e hannunki yana miki wani kallo kad'ai yabamu ams........"
Amatallah bata bari ta k'arasaba tarufe mata baki. Rita da goodness suka shek'e da dariya.
Sai kawai Amatallah ta fashe musu da kuka, dama ga abinda Aneesa ta mata yanata caccakar ranta. shiru sukayi, saikuma jikinsu yayi sanyi, nan suka shiga lallashinta, suna bata hak'uri.
Share hawayenta tayi tace, "kubar bani hak'uri, nifa bakune kuka sakani kukaba, kawai dai yanda auren namu ya kasance da Uncle na tuna.
Tabasu tausayi sosai. ganin time d'in lecture d'insu yayai tace Subari su fito zata basu labari.
A sanyaye suka jinjina mata kansu, sanan suka nufi lecture................
One luv my sweet Fan's
*_ALLAH ka gafarta ma iyayenmu_*
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_*
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
_Na gaisheku Aminan arzik'i, *Miss Xoxo and Ayusher Muh'd* kud'in na da banne a zuciyar Bilyn Abdull_
_i love you so much masoyan kwarai
____________________
*_Number 26_*
____________________

Dariya ce takusan kufcema Amatallah amma tayi k'ok'arin dannewa, dariyar tata tazone kam saboda ganin yanda Aneesa take sakkowa daga benen tamkar wadda aka biyo. tayi k'ok'arin kauda kanta gefe tana cigaba da jere kulolin abincin bisa tiren data d'akko.
Sai da Aneesa taimata wani kallo sannan ta shige 6angarenta tana murmushin muguntar data shiryama Amatallah itama.
Sarai Amatallah taga mugun kallon da Aneesa tamata, amma bai dametaba, tadai nemi tsarin ALLAH daga sharrinta a zuciya, Dan tasan tabbas wannan kallon bazai zamto Na alkairi bane.
gyara mayafinta tayi sannan ta d'auki tiren abincin tayi sama, komai cikeda dauriya takeyinsa, amma k'asan ranta ita kad'ai tasan a fargabar datake. Sallama tayi a k'ofar falon batareda ta shigaba.
Uncle dake kishingid'e har yanzun inda suka barsa ya amsa yana kallon k'ofar, "shigo mana". Yafad'a yana maida kallonsa ga TV.
Sai da tad'a sauke ajiyar zuciya kafin ta tura labulen da tiren tashigo.
Batareda ya kalletaba yace, " lafiya naga kin dad'e?".
Kanta ta kad'a masa kawai tana ajiye tiren bisa santa table d'in dake tsakkiyar falon.
Hakanne yasakashi juyowa ya kalleta, dai-dai itama ta d'ago zata cemasa ga abincin suka had'a ido. Da sauri ta sauke nata. shima janye nasa yayi yatashi zaune yana murmushi, k'arar TV ya rage yana fad'in "sauke k'asa ki janye table d'in, banacin abinci a sama".
Nanma batace komaiba ta sauke kamar yanda ya umarceta, k'asa yadawo ya zauna, itakuma ta durk'usa gabansa tana sauke kulolin daga tiren, harzata fara zubawa yace, " zauna da k'yau mana".
Still nanma dai bata tankaba ta gyara zamanta tareda tankwashe k'afafunta tafara zuba masa abincin. tuwon alkama ne miyar d'anyen ku6ewa, sai k'amshin kori ketashi mai dad'i (so a 6angaren abinci babu sakarai a matan Uncle, kowacce gwanace
"My best! wannan abincin yayi yawa ai, kozaki cine?".
Da sauri ta kad'a kanta alamar a'a.
Yad'an murmusa kad'an " wai an d'inke bakinne?".
A sanyaye tace, "a'a Uncle".
" Okay duk jan ajine irinna Amare?".
Ba shiri tasa hannu tarufe fuskarta tana fad'in "kai Uncle".
" ALLAH kuwa my best!, najiki tsit ne, amma ina ruwan wanke hannu".
"Bara Na d'akko na mantane".
Baice komaiba, sai dai harta fita yana binta da kallo, a fili yace " ALLAH kenan mai tsara al'amura, shi koda a mafarki yama ta6a tunanin Amatallah a jerin matansa, koda matan NASA keyin kishi da ita abaya wlhy shi bayajin komai a ransa game da ita, kallon d'iya yake mata tamkar su Sahib, amma Ubangiji gagara misali saigashi ya canja al'amura tamkar wani labarin tatsuniyoyi ko finafinai......
Sallamarta ta katse tunaninsa, ta ajiye k'aramar roba data zubo ruwan wanke hannun, zama takumayi tamkar d'azun.
"Yauwa babyna sannunku". yafad'a yana saka hannunsa a ruwan.
Itadai Amatallah mamaki komansa ke bata, tana mamakin yanda ko kad'an bayajin kunyar kiranta da kowanne irin suna yanzun, jibifa abinda yamata d'azun tamkar ba uncle d'intaba.....
Jin hannunta cikin ruwan ta sauke ajiyar zuciya da kallonsa. ido d'aya ya kashe mata, kafin yace, " nasan kema yunwar kikeji ai...
"ALLAH uncle a'a, naci abinci d'azun".
"Saiki k'ara yanzu ai ko".
Babu yanda zatayi dole tasaka hannu kamar yanda yamata umarni sukaci a tare, sai dai a kunyace Amatallah keci, ko kad'an takasa sakin jiki taci Na kirki, sunci kusan fin rabin data zuba taga ya tsame hannunsa yana fad'in "Alhamdllh".
Itama saita tsame nata hannun, dama tuni ta k'oshi, tsoron karyay mata fad'ane yahanata cire hannu.
Kallonta yayi " badai kin k'oshiba?".
Ta langa6e kanta gefe tamkar zata FASA masa kuka tace, "ALLAH uncle nak'oshi, kar cikina yafashe fa".
A mamakinta saitaga ya d'ora hannunsa saman cikinta wai zai duba yaga iyakar Girman cikin.
Da sauri tad'an matsa baya, shikuma yasaki k'asaitaccen murmushi yana shafa gemunsa, Wanda takula hakan yazame masa al'ada, inhar Abu zai faranta ransa koya 6ata ransa sai ya kai hannu yashafi gemun nan da itama kanta shaidace tasan ya k'ara masa k'yau da kwarjini.
" Uncle tunda kaci abincin bara naje Na kwanta, lectures d'in safe gareni gobe".
Wani kallo mai cikeda ma'anoni yamata kafin ya kauda Kansa yana murmushi, yakula dama tuni a d'arare take dashi, yabasar da maganar batareda ya bata izinin tafiyarba.
"Uncle Na tafi?".
Maganarta tasakashi juyowa ya kalleta, Kansa kawai ya kad'a alamar tatafi batareda yayi maganaba.
Ai ko cikin hanzari ta had'a kwanukan ta d'auka ta fice. binta kawai yayi da kallo harta kullema ganinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya.
Chapter 37 · 0% Book details