← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 66

Sashe 14

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

kai jama'a, ALLAH ka gafarta mana.
Kusan mintuna 16 aka samu komai ya lafa, amma Amatallah tana a halin doguwar suma.
Uncle M.A ya koma inda Baban Ama yake, saboda kiran sunansa kawai yake.
Yanzuma hannunsa yarik'e, ahankali yake iya magana, amma duk suna jinsa sabida shiru da d'akin yayi.
_"d'an uwana kaga yanda k'addara tayi damu, tsakanin jiya kawai zuwa yau, mungodema ALLAH brother, danshine mafi hikimar masu hikima akan hakan, mutuwa tabbatacen abune akan kowanne bawa, saidai kowa akwai sanadin tafiyarsa brother, wannan mu shine namu sanadin d'an uwana, duk duniya banida kamarka, dukda inada dangi amma kafisu matsayi agareni, sun kashemin Saliha ta hanyar soka mata wuk'a, awannan halin na isketa bayan dawowata sallar magriba, nikuma sun kunnamin wuta, tabbas nasan yaran da Khadija taganine sukai wannan aikin, brother! Na d'auki hakan a matsayin K'ADDARARMU, ga Khadija nan nabaka halak malak, ita kad'aice tarage mini, babu kuma mai iya rik'emin ita tamkar ni sai kai d'an uwana Muhammad, ba ruk'on Amatallah kawai nakeso kayi nawani d'an lokaciba, sonake ta kasance a gareka har k'arshen rayuwarka. brother inaso yanzunan a d'auramaka aure da Khadija..."_
Wata muguwar zabura Uncle M.A yayi, jikinsa da muryarsa na rawa yace, ''brother mikake fad'ane haka?, haba brother khadija fa d'iyatace, inajinta tamkar su Saifudden ne a zuciyata, karkayi haka dan ALLAH brother, gara kace na aurama j........

_Da sauri Baban Ama ya katseshi cikin hawaye, "a'a brother karkace komai dan ALLAH, inhar nid'in d'an uwankane da gaske, bakuma k'yamar had'a zuri'a kakeyi daniba ka amince da auren Khadija tunda ALLAH bai haramta makaba, karkayi dubi da d'iyatace, kasancewarta a wajen kane kawai zaisaka ruhina nutsuwa a cikin kabarina, inada tabbacin har Abadan bazaka ta6a barinta tayi kukan rashina ni da mahaifiyarta ba, duk Wanda zaisan muhimmancin Khadija ko kulawa da ita bayankane, dan ALLAH ka amince, danni lokuta k'alilanne suka rage a cikin dak'ik'un rayuwata, brother nima mutuwa zanyi, insha ALLAHU tare zaku bunne gawata data matata, bazan rayuba brother, Nika d'ai nasan minakeji, please ka amince dan girman ALLAH da k'aunar dake a tsakaninmu._
Kowa a d'akin kuka yakeyi saboda tausayi.
Uncle M.A yana kuka yace, " indai hakan zai sakaka farinciki na AMINCE brother, na amince da auren Khadija dukda ina kallonta a matsayin d'iyata, insha ALLAHU zaka tashi brother, cuta ba mutuwa baceba..........
Kasa k'arasawa yayi saboda kuka daya sark'esa.
Baban Ama ya k'ara k'ank'ame hannun Uncle M.A yana fad'in "ngd da amincewarka brother, kasani farinciki, zanbar duniya cikin shauk'in farincikin ganin auren Khadija da ALLAH yabani ita d'aya tilo a duniya, ALLAH yasaka farinciki da kwanciyar hankali a rayuwarku, ALLAH ya hana duk wani azzalumi tasiri akan wannan aure, ina rok'on alfarmar a d'aura yanzunan brother kafin numfashina ya k'are.
Kai kawai Uncle M.A ke d'aga masa yana zubda kwallah
*****
Kawu yakubu da sauran mutane hud'u, sai doctor shu'aibu da abokan aikinsa doctors kusan 10+, sai Jabeer dawasu mutane k'alilan masu jiyya suka shaida d'aurin auren *_Alhaji Muhammad Ahmad labbo da Khadija Isma'il uba (Amatallah)_* akan sadaki naira dubu 30 da kawu yakubu yabada, bayan Jabeer yayi saurin zuwa ATM ya fidda, kawu yakubu ne wakilin ango, yayinda Baban Ama da kansa yay waliccin auren d'iyarsa tilo Khadija (Amatallah).
Ana gudanar da d'aurin aure cikin dariya da tsantsar farinciki, amma nasu Amatallah acikin kuka da tsantsar k'unar rai aka d'aurashi, babantane kawai keyin kuka da murmushi lokaci d'aya.
Cikin farin ciki ya k'ank'ame hannun Uncle M.A yana masa godiya, tareda k'ara jaddada masa Amanar Amatallah.
Kuka kawai Uncle M.A keyi yana fad'in "brother bazaka mutuba, kabar fad'a domin ALLAH, cuta ba mutuwa baceba brother....
Murmushi mai ciwo Baban Ama yayi, " brother sai dai hak'uri, mutuwa kam tazama tilas, ka tabbatarma Khadija na yafe mata, ALLAH ya albarkaci rayuwarta, yasaka mata hak'uri da juriyar danganar rashinmu, tayi hak'uri da k'addarar data shigowa rayuwarta, watarana sai labari, badan ALLAH baya sonta bane ya d'aukemu, watak'il hakan shine mafi alkairi a rayuwarta, ngdma ubangiji dayabamu damar rayuwa da ita na tsawon shekaru 18, har zuwa yau danaga aurenta, ALLAH yayi mata al ....bar.... ka.......
Baban Ama ya k'arasa maganar a rarrabe, ahankali kuma yafara kalmar shahada.
Lamarin daya rikita Uncle M.A kenan ya rungume Baban Ama yana kuka mai ciwo da k'unar zuciya......
Jin jikin Baban Ama ya saki yasaka Uncle M.A d'agowa yana girgizashi da kiran Isma'il! Isma'il!!!! Please karka tafi kabarni dan ALLAH, brother karka tafi please.........
Yanda Uncle M.A ke kuka da sambatu sai da kowa ya koka awajen, da k'yar aka iya janyeshi akan gawar Baban Ama, aka lullu6eshi da farin bedsheet d'in dake kan gadon.
Chapter 14 · 0% Book details