← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 66

Sashe 54

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

salonki khadeeja, ked'in tadabance...... Fitowar yaran yasashi maida hankali garesu, harsunyi wanka anmusu shirin masallaci, duk suka gaidashi ya amsa cikeda so da k'aunarsu. ''Yauwa my sweet children's ku zauna kar Wanda ya6ata jikinsa naje nima nayi wanka karmu makara salla, ina Ummah?". Sahib yace, ''Abbu tana wanka". "OK, to nima bara naje nayi ko". A tare sukace to " Abbu ". Tunda yashigo falon mayataccen k'amshin turaren da Amatallah ke saka masa yabugi hancinsa, shak'a yayi ya lumshe idanu kafin yak'arasa bedroom d'in. A toilet yajiyo motsinta, dan haka yafara cire babbar rigarsa. Yana ajiyewa tafito itama, k'arasowa tayi inda yake, kowanne idonsa akan d'an uwansa, yana k'aunar yarinyarnan harma baisan iyakaba, sometimes idan tana Abu saita ringa d'ebe masa kewar Brother d'insa... K'ok'arin cire masa bottles d'in rigarsa datakeyine yasashi dawowa hankalinsa, tamkar wani yaro haka ya koma mata, itace tamasa komai hatta da wankan da shirin masallacin cikin milk color d'in shadda, ta fesheshi da turare, shidai kallonta kawai yakeyi, 'Yar k'arama da ita sai wayon tsiya, abaya yana ganin kamar Amatallah zatana cutuwa agidan saboda k'ank'artatrta da k'arancin wayo, amma a yanzu yakula koda za'a cuceta saidai tawani fannin amma bawajen kulawa da mijiba, ta kowanne fage tagama kwarewa, har yana mamakin tamkar wadda ake koyamawa, dukda har yanzu salonta Na nuna kunyarsa tana nan tanayin kayanta, (wadda kunyar tata nakuma sakashi a shauk'in k'aunarta) dan idan 'yan kunyar nakanta takan masa Abu tamkar ranar suka fara had'uwa amatsayin miji da mata, shikansa saiyanjin kamar ranar aka kawo masa ita........ Yanata zancen zuci har tagama kimtsashi tsaf. "Kayi k'yau my Uncle". tafad'a tana shafa fuskarsa. Hannun yarik'e ya sumbata, kafin yajawota jikinsa ya rungume tana shak'ar dadd'an k'amshinsa. Cikin sassanyar muryarsa yace, " ALLAH yamiki albarka khadeeja, yajik'ansu brother kinji". Tana murmushi ta jinjina masa kanta, kafin tad'ago tana kallon fuskarsa, "my lollipop bara nabaka ko fura kad'ansha mana? banason kafita da yunwa". Yanda ta narke masa haka shima ya narke mata, " no my heartbeat karmu makara fa, idan nadawo naci abinci kawai....." Bata bari ya k'arasaba ta tashi daga jikinsa tana tura baki gaba. Saurin rik'o hannunta yayi ya maidota baya yana fad'in sorry my beat karki fushi, haba Amintacciya 'ya daga ALLAH, banito nasha ko kad'anne". Tad'an kalleshi tana turo baki gaba, a shagwa6e tace, "really?". Gira ya d'aga mata kawai danya kasa magana. hannunsa takamo suka fito galo, ta zaunar dashi a kujera sannan tad'iba furar a frighte d'insa tasaka suga kad'an ta motsa, kusadashi tadawo, (hummm) mai makon ta zauna gefensa saita zauna a cinyarsa tana kashe masa ido d'aya. Wani lalataccen murmushi ya sakar mata, ya sak'alo hannunsa a k'ugunta, " my beat karfa kimin Squeezing da kaya nida zanje masallaci". Kofin furar tasaka masa abaki tana 'Yar dariya. amma batace komaiba. Haka taita basa furar saida ya shanye bai saniba, ta ajiye kofin a Center table tana fad'in Uncle kafa shanye tas". Bakinta ya sumbata, "yazanyi tunda 'Yar shagwa6a ta turkeni". " wato Uncle turkekama nayi ko? Shikenan munyima fad'a karka kumamin magana harka dawo masallaci ehe. Da sauri yakamota yana dariya, ya manne bakinsa kan nata. (Hummm dagananfa.....babu ruwana Da k'yar tasamu ya saketa yafice yana kashe mata ido d'aya da d'aga mata yatsun hannunsa biyu alamar bye bye. Gira ta d'aga masa itama tamasa alamar I love you da hannunta. Tsayawa yay cak yana kallonta, harya d'an juyo zai dawo takoma bedroom d'insa da gudu tarufo k'ofar, tasan inhar ya kamata bakinta saiyaci k'aniyarsa, gashi time d'in masallaci nakuma k'urewa. Sauka yay yana murmushi, dakumajin k'aunar Amatallah dake Shiga jininsa da 6argo. har yanzu yaran Na falo inda yabarsu, Shiga yay 6angaren Fateema suka gaisa, sannan yashiga wajen Aneesa itama, dukda tanata shamasa k'amshi bai damuba danyasan laifinsa.
Chapter 54 · 0% Book details