← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 66

Sashe 31

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ma ta lura, ta juya fuska tana dariya. Duk da abinda yamata ya 6ata mata rai, amma saita danne, ta k'araso daf dashi tana masa sannu da zuwa, cikeda fara'a ya amsa mata da kanne mata ido d'aya. ta sakar masa da wani sihirtaccen murmushi kuwa da d'age masa gira. Kallo d'aya tama Fateema tace sannunki. Ran Fateema ya 6aci da rainin wagon Aneesar, ya gida kawai tace itama tayi gaba abinta. Har suka k'arasa ciki yana baza idon son ganin Amatallah amma babu ko k'urarta. Anty Maijidda Na lura dashi, sai kawai tayi murmushi, a zuciyarta tace ya Muhammad Amatallah tawuce arhar ka ganta kai tsaye, saika bita har d'akinta. Dukda daular abincin da Aneesa ta had'a musu bata d'auke hankalin Uncle ba, gaba d'aya hankalinsa nakan son ganin Amatallah, soyake kawai yaga halin datake ciki. Suna cikin cin abinci Fateema ta kalli Nazeefa tana fad'in "Nazeefa wai Amatallah fa?". Da hannu Nazeefa ta nuna 6angaren Amatallah d'in. Uncle datun da suka fara maganar ya d'ago ido yana kallonsu yace, " lafiya dai ko bata fitoba?". Nazeefa tace, "Yaya ban saniba nima, tundai d'azun tana ciki".. Ajiye spoon d'in hannunsa yayi ya mik'e yana fad'in "bara Na dubata to". duk binsa da kallo sukayi, wani haushi yakama Aneesa. Fateema kuma tayi murmushin mugunta, dama danta rama abinda Aneesa tamata ta tambayi Amatallah d'in, Dan tasan dole mijinsu yayi wani Abu akai. Anty Maijidda kam da Nazeefa sai dariya sukeyi a zukatansu. Amatallah da har suka shigo cikin falon tana jiyosu, tana kwance a doguwar kujerar falonta tana game a waya, dukda zuciyarta sai harbawa take da fargaba. game d'in kawai takeyi, amma bawai yana mata dad'i baneba, Rabin hankalinta nakan su Uncle d'in. A hankali yaturo k'ofar falon ya shigo. Ko kad'an Amatallah bataji shigowar saba, sai k'amshin turarensa saboda ta juyama k'ofa baya, kuma a la66ansa yayi sallama yanda bazai yuwu tajiba. Shiru tayi tana hasashe, a zatonta ko tun daga waje k'amshin ke shigo mata. Uncle kam al'ajabine ya kamashi, shiyyasa yakasa motsawa, tunda yake bai ta6a ganin Amatallah da kwalliyaba sai yau. Jin kamar mutum tsaye akanta yasata juyowa cikeda fargaba. da Sauri ta mik'e tana fad'in "Uncle sannu da zuwa, ALLAH banasan ka shi..go..ba ne". Murmushi yayi, ganin yanda jikinta har rawa yake, kai kace taga wani ojuju ne, takawa yayi a hankali har inda take batareda yace komaiba, daga zaune Amatallah tad'an matsa baya kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta, a kujerar ya zauna shima kusada ita, ai saitaji kamar tatashi ta tsilla a guje. Hannunsa ya d'ora kan yatsun hannunta datake wasa dasu, yanda Jan lallen yay rad'am ne ya burgesa, murza yatsun yayi, hakanne yasaka Amatallah d'agowa tad'an kallesa. Komi ya tuna kuma saiya saki hannun, cikin sassanyar muryarsa yace, " haba my best! Babu fad'a miya kawo gabane? Laifin mi mukayi aka k'i fitowa tarbarmune, ko ba'a murna da dawowarmu mu koma Inda muka fito?". Hannu tasa ta rufe fuskarta dantaji kunya sosai tace, "Sorry Uncle, ALLAH ba haka bane fa, kawai dai". Murmushi yayi mai k'ayatarwa, yasa yatsun hannunsa biyu ya d'ago ha6arta tareda saka d'ayan hannun ya janye hannayenta data rufe fuska, saita rumtse idanunta. "bud'e idon to, kifad'amin kawai dai me? kokuma nayi wani Abu". Tace, "ALLAH uncle inajin kunya". " my best! to miye najin kunyar?, nifa Uncle d'inkine, ko yanzun an daina Uncle d'in dani sai mij......" Bai kai k'arsheba ta waro manyan idanunta a kansa. Shima saiya waro nasa kamar yanda tayi yana murmushi har hakwaransa Na bayyana a fili. Yunk'urawa tayi zata tashi danta gudu ya rik'e hannunta yana fad'in kinga wasa nakeyi, muje kici abinci, kowa ya hallara babu ke, har Fateema Na tambayarki taga bakizo mata sannu da zuwaba". "Uncle azumi nakeyi ai". " azumin me my best? Yaufa Saturday?". Rasa mizata cemasa tayi, dankuwa k'arya ta mullik'a babu wani azumi, tana dai jin kunyar fitane saboda kwalliyarta. Hakanne yasa yagane k'arya take. Mik'ewa yayi itama ya mik'ar da ita tsaye. Ta marairaice masa fuska kamar zatayi kuka, "wayyo Uncle da gaskefa nakeyi". Baima San tanayiba, dan kallonta yake daga sama har k'asa, bak'aramin zama kayan sukayi a jikintaba..... Ganin hankalinsa bama kanta yakeba ta girgiza hannunsa dake rik'eda nasa. Kallonta yayi da sauri, yace, " mikikace my best!?". A shagwa6e tace, "kai Uncle kana nufin baka jiniba ma?". Kasa amsata yayi, yaja hannunta dan yakula inhar suka kai wani lokacin a falonnan zai iya kauce hanya ya aikata abin kunya.... ''Uncle please zanje da kaina, ALLAH zanma ci abinci". Amatallah tayi maganar da sauri dan ganin da gaske soyake ya kaita har falon yana rik'eda hannunta. Baice mata komaiba ya saki hannunta, fitowa sukayi yana gaba tana bayansa, dan haka ta 6oye sosai a bayansa. Fitowarsa yasaka Fateema da Aneesa d'agowa suna kallonsa, kowa da dalilinta na kallonsa da son suga Amatallah d'in. Anty Maijidda tace, " a'a Yaya lafiya dai ko? ina Amatallah d'in to?". Juyawa yay a zatonsa bata biyoshiba, sai ya ganta a bayansa, tana famar 6uya, matsawa yayi gefe yanda zasu ganta yana fad'in ''k'alau take, kunyarku takeji saboda tayi.....". Sai kuma yay shiru ya k'are maganar da 'Yar dariya yana zama a kujerar daya tashi wadda Aneesa da Fateema suka sakashi tsakkiya. Amatallah jitai tamkar ta nurse k'asa dan kunya, Fateema da Aneesa duk sukad'an waro idanu kanta cikin mamaki da ganin k'yan datayi. Aneesa Na mamakin yaushe Amatallah ta koma haka?, Fateema kuma Na mamakin canjawar Amatallah d'in a watanni hud'u. Nazeefa kam cikin nuna kamar batasan da kwalliyar Amatallah d'in ba tace Woow!! Amatallah, wannan wanka yayi, kinfito a amaryarki". Jabeer da Shehu da Anty Maijidda da Uncle duk dariya sukayi, yayinda wani kishi ya tokare mak'oshin Aneesa da Fateema. Amatallah komawa tayi baya da sauri tashige bangarenta. Nanfa duk aka saka mata dariya, harda yaran. Nazeefa tashiga kwala mata kira, amma sai Uncle yace "barta Nazeefa, haka Khadija take da kunyar tsiya". " Yaya ai bataci abincin bafa". " 'Diba ki kai mata kawai, kowama yakamata yay saurin kammalawa yanzu zakuji magrib". Duk da to suka amsa. Nazeefa ta d'iba komai dai-dai misali Dan tasan Amatallah batada cin abinci sosai ta kaimata. Har Nazeefa tashiga ta fito Amatallah bata yarda sun had'a idoba, dariya Nazeefa tayi kawai tafito abinta.
Chapter 31 · 0% Book details