Sashe 50
Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Da taimakon su Nazeefa suka had'a abinci da abinsha masu k'ayatarwa, harda suyar kaji, abinka da hannu dayawa dandanan asuka kammala, aka had'a komai a falon bak'i dakecan waje, komai yayi babu yanda za'ayi suji kunya kuma, harda alalan dasukayi Na jama'arsu duk suka d'iba suka ajiye, zuwa sannan gidan kam ya d'inke da jama'a.
Su Amatallah duk aka canja kaya, komai tanayinshine kawai, amma jikinta duk babu dad'i, saidai Alhmdllh tana k'ok'arin daidaita tafiyarta, kasancewar dama ita mutumce mai sanyi, komai NATA a nutsuwa takeyinsa, su Anty Sadiya suna 6angaren Aneesa takasa ta tsare. Sai 6angaren Amatallah yazama Na yaran mata, su Nazeefa da k'annen Fateema, dadai yara-yaran matan danginsu, suna falon Ama sunata shan shargallensu ana barkwanci da tsokanar juna.
Saigasu Fa'iza Goodness Rita dawasu k'awayensu Na makaranta da'ake gaisawa.
Nanfa fili yakuma kacamewa da hira, kokad'an babu Wanda yanuna k'yama gasu goodness kasancewarsu ba addininsu d'ayaba, suma tun suna d'ari-d'ari har suka saki jiki anata hira da dariya.
"Amatallah ta kalli Fa'iza cikin tsokana tace, " sannu uwar uku, ALLAH nazatafa bazaki iya zuwaba?".
Hararta Fa'iza tayi cikin wasa tace, "a'a uwar 12 ba ukuba, kenifa garau nakejina ko reren gudu saimuyi ehe".
" tab dawa zakiyi reren? Aiko zan barki a taku biyu harnaje Na dawo baki motsaba".
"Hawaba yarinya, badan karnama Uncle d'inmu asarar sabon babyba danace muyi".
" sabon baby a ina?".
"A cikinki". cewar Safina wata cousin d'in su Uncle.
Aiko nan tsokana tadawo kan Amatallah, ta dage tana kare kanta, nandai Ramla da Bilkisu suka shiga kare mata suma.
Sun kacame da surutu wayar Amatallah nata ringing bata saniba.
Anty maijidda tashigo tana magana da k'arfi yanda zasuji.
" oh ni Hauwa'u, anya kuwa wani najin maganar wani a cikinku? Kunjikuwa yanda kuka cika mana kunnuwa? Amatallah mijinki nata kiranki a wayama baki saniba kenan?".
Da sauri Amatallah ta kalli wayar, gata a gefenta amma batajiba, dayake wayar a silent take, kuma ta kifeta, mik'ewa tayi tana fad'in "ALLAH banjiba Anty".
" yazakiji kuna wannan zuba tamkar rediyoyi, kizo to".
Tsallakowa tayi tafito, Fa'iza da goodness da Rita suka kalli juna suna murmushin jin dad'i, dansunga sauyi ga aminiyar tasu, atunaninsu bazata mik'eba kai tsaye hakaba saita nuna jin kunya, (amma sai sukaga babu kowani alamar hakan tare da ita) basusan dauriya Amatallah tayiba kar ai mata dariya
, (Dan tak'aru da hirar yaran matan da tund'azun akan gidan aure dama aketa surutun).
A waje ta iskeshi shida Aneesa tsaye suna magana, kishi da haushi suka kamata, (ya ita da miji wata dafara zuwa wajensa
) (Ama... An fara kishi kenan....lol
Danne zuciyarta tayi ta k'arasa, sannu dazuwa tamasa, ya amsa idonsa akan kwalliyarta data tafi dashi, maganar dasukeyi da Aneesa ya maimaita mata.
"Abokainane gasunan kusan su goma, kokad'an banyi zaton zuwan nasuba, saida nafitane Alhaji Sabi'u ke sanarmin sunce zasuzo ganin baby, naji dad'in k'ok'arinku, ALLAH yaymuku albarka kunji my wife's".
Atare sukace Ameen, kowa kishi nacinta a zuciyarta, amma a fuska bazaka ganeba, (Aneesa ma anfara k'ok'arin dannewa
" yauwa to yanzu saikuma Fateema magana, idan mun kammala cin abincin saikuzo Ku gaisa kenan, akawo Aminatun. Sai daifa bahaka zakuzoba k'attin banza su ganeminku, asawo hijjabai".
Daga Aneesa har Amatallah dariya sukai masa.
"To ai gaskiyane, danma karsuce, ALLAH da har nik'af zance kusa, kunsan inada kishi, khadeeja Ce kawai bata gama saninaba, amma ahankali zaki fahimci hakan kema"., yay maganar da kanne mata ido d'aya.
Murmushi tayi ta kauda idonta akansa.
Sarai Aneesa ta gansu, kuma taji zafi sosai, harma saida fuskarta tad'an nuna, amma tayi k'ok'arin waskewa dafad'in ''ALLAH nagaji over".
" sorry my neesa". Uncle yafad'a cikin tausayawa, ya kalli Amatallah ma yace sorry my best, nabaku wahala ko?".
"Lah babufa komai Uncle, ai alsunan babynmuce, damunyi barci gajiyar zata ware ko Anty?".
Murmushin yake Aneesa tayi, ta kad'an kanta kawai, amma mamakin Amatallah takeyi, dama tana magana haka? Dan tuni ta lura Amatallah miskilace.
Ciki suka koma, uncle kuma yakoma wajen bak'insa.
Kamar bayan 1hour yakirasu duk awaya akan suzo sun gama, kowacce cikin hijjabi tafito, Amatallah ta kar6i jaririyar daga hannun Fateema suka jera abin sha'awa suka nufi falon.
Sallama sukayi ak'ofa, saida aka amsa musu sannan suka shiga.
A mutunce suka gaisa, Uncle ya amshi Ameenatu a hannun Amatallah yabasu, fita sukayi suka bar musu ita tunda barcima takeyi.
Duk saida suka gama ganinta suka saka mata albarka da addu'oi sannan aka maidota da alkairi mai yawa daga garesu.