Sashe 17
Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da doctor shu'aibu, sai Su jabeer kuma. Kowa dai ya hallara. Aneesa da Fateema sai mamakin wanna taro sukeyi, su duk zatonsu akan ruk'on Amatallah ne, anason aza6i wadda za'a bamawa acikinsu, tunda sunsan dolene mijinsu zai cigaba da rik'onta. Fargaba dukta cika Uncle, damuwarsa d'aya akan yanda Amatallah zata kar6i zancen auren ne. Bayan addu'oi da aka gabatar kawu yakubu yamik'e a nutse yafara jawabi tundaga farko har k'arshen abinda ya wakana aranar da Baban Ama zai rasu. Tun jikin Amatallah Na rawa a 6oye harya fito fili, tafara karkarwar rawar sanyi sosai, kuka kam tama nemesa tarasa gaba d'aya. Anty maijiddah dake kusada itace tajawota jikinta tana lallashinta. Idon uncle k'yam akanta, ko k'yaftawa bayayi balle yatuna akwai wasu halittu su Aneesa awajen. Daga Aneesa har Fateema kam mutuwar zaune sukayi, kowacce takasa motsin kirki, har kawu yakubu yagama jawabi yakoma nasiha agaresu. Tashin hankali kenan, Wanda ba'a samasa rana. Wannanfa shine ana wata gawata tazo. Dad'i sosai yakama Nazeefa, Dan aganinta babu Wanda Amatallah tadace dashi kamar yayansu Muhammad, lallai wannan shinefa ake kirada *HA'DIN ALLAH*. har taro yatashi mutum uku basu iya koda tariba, Aneesa, Fateema, garama Amatallah tanata hawaye da rawar sanyi. Ranar kam haka ta kwana rijif da zazza6i mai zafi ajikinta, sai sambatu takeyi dakiran sunan Amminta da baba. Da k'yar innani tasamu tayi barci, dama ita ba had'in auren ba, halinda yarinyar zata tsinci kanta, dakuma yanda zata kalli al'amarinne damuwar. ___________________________ Alhmdllh k'ura ta kwanta, zuwa yanzu jos da Kaduna abubuwa sunfara dai'daita, sai dai bak'aramar asarar rayuka dana dukiyoyi akayiba, lamarin ko k'yan gani babu, abin tashin hankalin abin yafi shafar matasanmu, kusan duk sune aka kashe da raunika kuma ga wad'anda suka rayu. A kudancin k'asarma Alhmdllh komai ya lafa, sai kuma yad'a 6arnar da akayi a kafafen yad'a labarai Na waje dana gida, hanyar samun kud'i kuma ta bud'ema 'yan jaridu. Jami'an tsaroma sai fankama suke, hakama 'yan siyasa abin kamfen dayima jam'iyya mai mulki gugar zana tasamu, muma kammu talakawan ba'a barmu abayaba, sai zabga kalaman ALLAH wadai muke ga gwamnati batareda dubi da mune muka haddasama kanmuba. K'asar duk tabi ta rud'e da surutai marasa kan gado, kowa k'abilarsa da addininsane mai gaskiya, babu mai yarda a jingina masa koda laifi d'ayane, masu tsoro kuwa harsun tattara inasu-inasu sunma k'auyikansu da yankinsu saukar angulu, Na kudanci sunkoma yankinsu hakama arewaci, kowa 'yancin fad'ar albarkacin baki dayake ik'irari dashi tasashi kasa yima k'asar k'yak'yk'yawan fata, saima k'ara Neman hanyar kare kai Dan aganin wasunmu bata mutuba rufa tayi, akwai sauran yak'i agaba, kowa yakoma gidane yasawo sulken yak'i. A 6angaren manyan k'asar kam d'if kakejinsu, kaikace babu sarakunan gargajiya ak'asar, malaman k'asar da pastors sunyi gum da bakunansu basa cewa komai sai sunsami ke6ancewa da mabiyansu a k'uryar lunguna, wasunsu suzama masu tunzura matasan da nuna musu sune masu gaskiya, k'alilan dasuke Na kirki sune masu tsawatarwa da nuna kuskure da illar abinda yafaru. Kowa yazama d'an jari hujja, mutuncinsa kawai yake k'ok'arin karewa da yankinsu, zancen nuna gaskiyar muzama k'asa d'aya al'umma d'aya son zuciya yasa mungina rami duk mun binne furucin bakunanmu, mai k'ok'arin so a gyara saikaji jama'ar yankinsa sun rad'a masa suna *MARA KISHIN KAI*. humm kai da shi mai tada husuma komai yanka albashin had'a rikice-rikice wanene mara kishin kai aciki?. Wlhy idan bamu gyaraba wankin wula tana dab dashirin kaimu tsakiyyar dare mai duhuwar dazamu kasa koda ganin tafikan hannunmu. Da ni da kai duk 'yan k'asane, munada zarrar kawo canji koda ta hanyar tsarkake zukatanmu ne da gyara halayyarmu. Ba gwamnati da shuwagabanni ne kad'ai ke buk'atar gyaraba, hatta damu talakawan masu ik'irarin Neman gyara da hura haccin sai an gyara d'in muna buk'atar gyara kanmu. Taya kakeson k'asarka tazama mai tsafta ta hanyar jagorancin shuwagabanni amma kai talakan k'asar kullum kana tebirin 6arna. Bakasan darajar zuminciba, bakasan muhimmancin addininka da koyi da k'yawawan aiyyukan daya kawo makaba, bakasan wace k'yautatawa yakamata iyalanka su samu daga garekaba, balle ajega zancen makwafta da abokan zamanka Wanda addini ya banbantaku, baka Neman abincinka ta hanyar hallal balle kaciyar da iyalanka suzama nagartattu masu tsafata, kullum harshenka yana kan aibanta 'ya'yan jama'a da zund'en matan mutane, sai hassada da ganin k'yashin cigaban d'an uwanka fal ruhinka. Kina mace kinkasa son abokiyar zamanki balle 'ya'yanta, kullum zuciyarki cik'in k'yashi da bak'inciki take idan mijinki ya k'yautatama iyayensa da 'yan uwansa, kinkasa nutsuwa wajen bautama ubangijinki amma kece sahun gaba agidan uwar gulma ko gidajen Malam tsubbu da bokaye anufin Neman taimako, burinki kullum ace kece sama dakowacce mace a6angaren k'yale-k'yale da kayan k'awa Na duniya, buri dason burga yahanki fad'ama mijinki gaskiya yayinda kikaganshi bisa karkatacciyar hanyar dazata iya kaiku wuta ke da shi da 'ya'yan dakuka haifa, Kana matashi amma kullun burinka akan kayi kud'i kake, ka auri mace ajin farko a k'yawawa kasaka acikin gidanka Na k'awa danta zame maka fure, babu ruwanka da tarbiyyarta ko addininta balle nasabar data fito, jin kanka kake on top kai yanzu kafara zamaninka mutuwa da sauran tak'i a tsakaninku da ita, baka ganin kowa da gashin arzik'i saboda kai ka iya kuma karanka yakai tsaiko, kasani sai dai ka sanar babu mai sanar da kai saboda kasha boko ka k'oshi, da ance kayya kaine sahun farko a masu d'akko makami afara y'ar rere tsakaninka da jama'ar gari, aganinka kai dai-daine bakada matsala da duniya, koyanzu kabarta hankalinka a kwance tunda baka haihuba. Wlhy muji tsoron ALLAH, mufara tuna komu su waye kafin gangar shaid'an tamana tasiri a zukata mu kwashi filin rawa muna tangad'in maye dajin kanmu can k'ololuwar sararin samaniya muna yawo cikin giza-gizai. Kowa yaje inda zashi yadawo akwai rana d'aya tak da za'a baka littafin ayyukanka a hannun haggunka ko damarka, wannan za6in yarage naka. Duk nau'in shed'ancin dakakeji ka gawurta tarihi ya nuna anyi wani kafinka, kuma anshafeshi yazama labari tamkarma bai zoba. To kaikuma asuwa da naka tak'adarancin bazai zama labariba harma ayo Wanda yafika k'warewa. Abin mamaki dukfa da wannan halayen namu amma mukeson samun shugabanni nagari, bayan ALLAH yafad'a mana, dai-dai sugabanninmu dai halayenmu kuma. Tab d'i, ashe kam da sauran kallo Kayi nazari, kiyi nazari, nayi nazari, muyi nazari domin gano illolin takubban shed'anarmu komunada rabon gyarawa kafin randa mala'ikan mutuwa da rundunarsa zasu zagaye sashinmu Dan k'udundunar ruhinmu zuwaga Wanda yayka yayni dama duniyar da abinda ke cikinta. ALLAH ka ganar damu gaskiya koda bazata mana dad'iba, ka tasirantar da ita agaremu, mu kar6eta mukumayi aiki da ita danmu samu komawa ga ALLAH cikin salama _____________________________ "Wai kana nufin bazakayi break fast ba agida dear?". Gyara zaman hular kansa yayi, sannan ya d'auki turare ya fesa, kafin ya juyo sosai yana fuskantarta, cikin sassanyar muryarsa yace, ''sorry my neesa, wlhy ina saurine, dan inada meeting a da lectures k'arfe 12, gashi inason shiga naga jikin baba, nakumaje kasuwa, yau kayanmu zasu iso. Please kimin afuwa mana my sweet". Ya k'are maganar da matsawa kusada ita ya rungumeta a jikinsa. Bakinta ta d'an turo kad'an, cikin d'aurewar fuska tace, " kai dai kanason ganin Amatallah kawai, babu wani duba baba". Lumshe idanunsa yayi yana guntun murmushi, ya d'agota daga jikinsa yana mai zuba idanunsa kan k'yak'yk'yawar fuskarta datasha kwalliya. "My neesa! kina ganin nayi laifi kenan koda ganin Khadija zanje? a tunanina koda babu aurena a kanta ta cancanci irin wanman kulawar daga gareni, karfa ki manta jinin brother d'inace ita. a zatona kodan halin da yarinyar ta tsinci kanta ta cancanci kubar mata ni gaba d'ayama ai". Sosai Aneesa ta zaro idanu waje, " mubar matafa kace?". "Eh mana". 'Yay maganar cikin d'age gira'. Bakinta ta ta6e, cikin matuk'ar hasala tace, " ai wlhy ba haifi d'iyar dazan banmata kaiba, raba dai-dan kama danekiyi tsoron azabar ALLAH ne kawai yasani hak'uri, nifa wlhy harma mamaki nakeyi yanda kayarda da auren d'iyar cikinka, shin baka tunanin kamata tsufane?". Wani abune ya soke zuciyar Uncle M.A, ya kafe Aneesa da idanu ko k'yaftawa bayayi. tabbas maganarta ta mugun shigarsa. bai ce mata komaiba ya d'auki wayarsa da key yafice. Bayansa Aneesa ta raka da harara, yau ko shiga su gaisa da Fateema bai yiba. Sai tashin motarsa kawai taji. Da kansa yabud'e gate ya fice, sannan yafito daga motar ya yarufe, tafiya yake amma maganar Aneesa nakuma tasiri a zuciyarsa, shikansa tunda aka d'aura aurenan abinda ke damunsa kenan, sai yaga kamar an cutar da Amatallah, duk da shikam garas yake jin kansa da lafiya, bai San miyasa maganar Aneesa tamasa zafiba da yawa, bayan shima yasan gaskiya tafad'a. Hannunsa yakai yashafo ma dai-daicin gemunsa, kafin ya furzar da iskar bakinsa yana kuma dafe sitiyari. Ya d'anja lokaci a hanya kafin ya isa gidansu, saboda 'yan makaranta. Babu kowa a tsakar gidan, sai dai yaji kamar alamar mutum a Ketchin. Yasan maybe Nazeefa ce, Dan haka saiya wuce d'akin baba. Sai da yayi sallama, aka bashi izinin Shiga sannan ya shiga. Innani ya tadda gefen baba tana gyara masa rawani bisa kansa data yafa masa, da alama wanka tamasa, kullum da sassafe take masa wanka ta shiryasa, shiyyasa saika taddashi tsaf. Tunda yashigo baba da innani suke binsa da kallo, Dan tabbas sun gano alamun damuwa a fuskarsa, duk da sunsan damuwar rashin isma'il har yanzu bata barshiba, hakan bai hana baba fad'in "Muhammadu lafiya kuwa?." Duk girman d'a agaban iyayensa yarone Dan haka sai Uncle M.A yakuma jin zuciyarsa tayi rauni, zama yayi ya gaida iyayen nasa, da tambayar ya jikin baba?. Tambayar baba yasake mai maita masa. Innani dai batace komaiba, tama kauda kanta daga garesu, tanata ninke kayan baba daya cire, sai dai dukkan hankalinta Na kansu. Yay k'asa da kansa, cikin sanyin muryarsa yace, "baba akan maganar auren nanne, sai nake ganin kamar an cutar da yarinyarnan, musamman idan akayi dubi da shekarunta da nawa". Murmushi baba yayi tareda gyara rawanimsa dayake rufe masa fuska, yace, " miyasa kake wannan tunanin Muhammadu?, ai ba haramun baneba idan mai shekarunka ya auri kamar Khadija, sai dai malamai sukance yin zai iya zama cutarwa ga ita yarinyar zuwa gaba, Dan sanda zaka kai wasu shekarun tsufa ita kuma sannan take tashen k'uruciyarta, kaga zata iya cutuwa saboda kai k'arfinka ya ragu, amma zakaga wani kuma idan ALLAH yabashi lafiya babu abinda bazai iyaba alokacin, (anta6a ma