Sashe 34
Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
d'inan babu Wanda yasan gidan wani, toni rana d'aya aka d'aura aurena da kishiyata, ni da safe ita da rana, kuma yanada wata matar, saidai tana gidansu, sa6anin dasuka samune yayo auren huce haushi damu mu biyu, yanzu kuma shirin dawowa take an sasantasu". Ba k'aramin mamaki da al'ajabi bane yakama Amatallah, a ranta tace halin maza sai abarsu. a fili kuma tace "amma Fa'iza kunsan da haka kuma kuka aureshi?". " to yazamuyi Amatallah, auren zumincine, da mamana da babansa uwa d'aya uba d'aya, waccan kuma budurwarsace dama, saboda itanema suka rabu da matarsa akan yace zai Aurota ta tada hankalin kowa a families d'in, harya kai gamata saki d'aya saboda sakko iyayensa datayi a haukarta, mamansa kuma tanada zuciya, hakan yasa tace bayan auren dayakeson k'arawa yahad'a dani mu zama biyu, saitaga yanda uwargidansa zatayi d'in, shinefa dalilin dayasa aka d'aura aurenmu rana d'aya, ni da safe ita da azhur, kusan shekara biyu kenan, uwargidan bata kuma wani aurenba, bakiga yanzu duk yanda tafita hayyacintaba, kullum cikin bibiyarsa take tana bashi hak'uri da rok'on ya maidata, dan suna matuk'ar son juna, to shine manya dai suka shiga aka sasanta, yanzuma jibi zata dawo". "Tabb, lallai wasu matan basuda hankali, nifa banga mafitaba ga macen da zata rud'ar da kanta wai dan miji zai sake aure, raini yake kawowa wlhy, kowa yanamaka kallon shashasha, kinga yanzu ta jama kanta daga d'aya anmata biyu, kuma mijin bazai kalleta da darajaba kamar da can?". " wlhy kuwa hakane Amatallah, ALLAH dai ya sassauta mana kishinan, wasu Matan sun Gaza gane kishi cikin SIYASA tafi kawo zaman lfy da daraja wajen miji, kamazo kana hauka kan Namiji baisan kanayiba". "Tokin gani, kuma wlhy kishiyarma indai kina nuna mata komai ba komaiba a fiska koda kina kishinta a rankin saikinga tana shakkarki da tsoron takaki, dan baki bata wata k'ofar dazata rainakiba, kuma mijin bazai ta6a aminta ta raina kiba, kinga ai kin nemama kanji daraja har wajen dangin mijin. yanzu wlhy Uwargidanmu inkikaga yanda take kishinta saita burgeki, amma Aneesa ba a magana, harma mamaki take bani". ''Karki damu Amatallah, zan koya miki wasu abubuwan, dukda shi zama da kishiya basai ankoyama mace shiba, wahalama na sakata ta koya, kamardai yanda ni wahalarce tasani koyon". "Kai dan ALLAH?". dariya Fa'iza tayi, " ALLAH kauwa Amata, ke idan INA Baki labarin gidanmu ALLAH saikice k'arya nake, ai garaku na fahimci kishin masu Ilimi akeyi a gidanku, mu Amaryarmu tafi uban kowa zafin kishi, ga uwargidan itama babu sauk'ice". "To ALLAH ya k'yauta". Nandai suka d'an tattauna, Fa'iza ta ankarar da Amatallah abinda Aneesa ke nufi da maganarta. " kinga daga yanzu kema sauk'i shirya aii, amma dan ALLAH inason tambayarki, kumafa ki fad'amin gaskiya inhar kin yarda dani". "Na yarda dake wlhy Fa'iza, shiyyasama nafad'a miki sirrina ai". Murmushi Fa'iza tayi, sanan taja hannunta suka zauna kan wata baranda, dan dama basukai ga fita gate ba. Kafad'arta ta dafa, " Amatallah shin kinason Uncle d'inki kuwa?". Dariya Amatallah tayi, sannan tace, "gaskiya kikace na fad'a miki kuma zan fad'a miki Fa'iza. lokacin da akai aurenmu dai bana masa son aure, dan kallon uba nake masa, lokacin ga rud'anin rashinsu Ammi, amma tunda na fahimci yanason cikar burina akan karatu, da k'aunar dayakema mahaifina sainaji nafara masa SO irinna aure, Ahankali kuma yaytamin abubuwan dasukaja ra'ayina ta waya, da kuma taimakon shawarwari da k'anwarsa Nazeefa taita bani, saina kuma gane babu Wanda yasan muhimmancina da kuma zaiji tausayina kamarsa, nasan kuma wannan babana ya kalla harya k'ulla wanan auren, Wlhy Fa'iza ina son Uncle har cikin raina, saidai ina masifar jin kunyarsa, musamman idan na tuna alak'arsa da mahaifina".