← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 66

Sashe 7

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

da sauri nabi bayansu Dan ganema idona ina zasuje kuma
______________________________
Zaune take akan abin salla, tunda ta idar da sallar isha'i bata tashiba, Ammi Na zaune akan d'aya daga kujerun plastic namasu jiyyasa. tunkan su shigo k'amshin turarensa yayo gaba.
K'irjintane yafara bugawa da sauri-sauri kamar yanda yakeyi koyaushe, hannu tasa ta dafe tana mamakin wannan lamari, aranta tace, miye ma'anar hakan ni Khadija?.....
Sassanyar muryarsace ta tadaki kunnenta. Ammi ta amsa sallamarsa tana mik'ewa, tareda musu sannu da zuwa.
Shikad'ai ya amsa, Dan Baban Ama waya yakeyi.
Ta gefen ido Amatallah ta ke satar kallonsa, ya canja kaya zuwa fara tas d'in jallabiya mai dogon hannu, sai bak'in wando daya lek'o kad'an da silifas d'in babanta a k'afarsa.
Kujerar da Ammi ta tashi ta tura masa, ya ajiye ledojin hannunsa kafin ya zauna yana fad'in "sorry madam mun barku Ku kad'ai ko?".
" lah babu komai wlhy, kaida kasha hanya ma, kamata yay kayi kwanciyarka ka huta basai kadawoba".
Kafin yabata amsa Baban Ama yagama wayar. matsowa yayi inda suke yana dariya, kibari kawai, babu yanda banyi dashiba ya zauna yak'i, wai saiyaga mamana". Yay maganar yana kallon direction d'in da Amatallah ke zaune.
duk tana jinsu, saita k'irk'iri addu'ar k'arya, bayan kuma tadad'e da idar da salla. shafawa tayi sannan tataso, kanta a k'asa ta rissina tana gaishesu.
Atare suka amsa da tambayarta ya k'arfin jiki?.
tace, "Alhmdllh".
Uncle M.A yace, ''My best daughter kinci abinci kuwa?".
Da sauri ta d'aga masa kai alamar eh taci.
Hararta Ammi tayi, " k'arya dai babu k'yau Amatallah, yaushe kikaci abincin?".
Kanta tad'ago ta kalli Ammi, idonta taf da kwalla tace, "kai Ammi".
" kai Ammin uwar mi?, tashimin anan kafin na bigeki ak'ara miki kwanaki a asibitinnan".
Da sauri Amatallah ta haye gadon datake jiyya.
Uncle M.A yace, "madam inafa jin kunyarki, naga kin tasomin d'iya a gaba".
" haka kullum takeyi wlhy brother, nafad'a mata rashin cin abinci halittane, harma ina mata misali dakai, amma bata d'agama mamana k'afa ko kad'an.
Uncle M.A ya kalli Ammi yana murmushi, sorry madam, rashin cin abinci halittace, haka kusan koda yaushe innani kemin, sai dai in baba Na kusa ya kareni ko Maijidda, yanzu haka matsalar kenan nidasu Fateema, kowacce da irin tunaninta, nifa har asibiti innani takaini ina yaro ban mantawa wlhy, wai likita ya dubani banacin abinci, kowani ciwone dani?.
Dariya sukayi gaba d'aya, harda Amatallah datayi murmushi tana satar kallon uncle M.A d'in.
sun d'an ta6a hira, harya kira Fateema da Aneesa suka gaisa da Amatallah da Amminta, amma kowacce badan ranta yasoba, musamman Aneesa dakejin zafin Amatallah sosai, (koda yake halintane, tanada zafin kishi, akan Alhaji Muhammad d'in
, saboda auren soyayya sukayi).
Sai wajen tara suka tafi da k'yar, akabar Ammi da Amatallah.
dukda baba Ama Na fargabar barinsu su kad'ai, saboda halin da Amatallah ke kwana aciki, gefe kuma yanajin kunyar barin abokinsa ya kwana shika d'ai, haka dai suka tafi yana addu'ar ALLAH yasa su kwana lfy..........
*_masoya, INA alfahari daku over wlhy_*
One Luv my fan's
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_(home of expert and perfect writer's)_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_*
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
____________________
*_Number 4_*
____________________
........"Haba dan yanzu Ku kun k'yauta kenan? har a kama su zike kusan 2days amma babu Wanda ya sanarmin acikinku?".
"To yanzu da ace shi gagis ya mutu fa? Kenan bazaku sanarminba? Kunsanfa yarannan sunada maruk'ar amfani a garemu yanzu, dolene komai k'ank'antar Abu mu tsaya musu....".
" sorry sir!, muma bamuji zancenba sai d'azun wani acikinsu Daba'a kamaba yazo yafad'a mana".
"Yaza'ayi ku sani kuwa? tunda bakwa maida hankali wajen kula da aikinku. yanzu ina gagis yake?".
" sir! Yana asibiti kwance, sukuma su zike suna police station."
"Mtsoww!!, aikin banza kawai, yanzu saiku shirya muje mu kar6o su zike, dan sunada matuk'ar amfani a tafiyarmu. Shikuma gagis zuwa gobe sai wasu acikinku suje su dubashi a asibiti".
" okey sir!.
_(Nace, "hummm, hattara matasa, kun gadai halin 'yan siyasar k'asar tamu, wannan d'an takarar bata gagis dake kwance a gadon asibiti yakeba, a'a, tasu zike yakeyi, dansu sunada lafiyar dazaiyi amfani dasu, shiyyasa zaije da kansa ya kar6osu a hannun police, amma gagis, zai tura wasune daga mutanensa su duboshi, tunda shi bashida amfani agareshi a halin yanzu. to wlhy haka kuke a wajensu, sai zaku musu amfanine suke kulaku, idan kuma rashin lafiya ko wani tsautsayi ya sameku basuda matsala daku
, bare kuma idan sun d'ane kujerar
dasuke nema
_____________________________
"Dear amma dakayi hak'uri da tafiyar nan sai da safe idan ALLAH ya kaimu mana".
d'ago idanunsa yayi yana kallonta da murmushi, saboda yanda tayi maganar.
cikin tsokana yace " my Neesa kodai bakison kwananki ya gudune?".
Hannu tasa ta rufe fuskarta tana 'Yar dariya, "kai my dear! Nidai ALLAH bance haka ba, ai nasan maganin baba zaka amsone".
"Tom shikenan my Sweet Neesa, amma ba maganin babane kawai yasani tafiyar yammarba gaskiya, dan Alhmdllh jikin baba da sauk'i, bakamar wata d'aya daya shige ba. Amatallah ce batada lafiya, suna asibiti ma an kwantar dasu".
Tuni fara'ar fuskarta ta ragu, babu yabo babu fallasa tace, " ALLAH yabata lafiya".
Daganan tamik'e ta hau had'a masa kayansa.
Binta yayi da kallo kawai, yad'an girgiza kansa yana murmushi, baisan miyasa dukkan matan nasa suke nuna kishi akan Amatallah ba?, bayan sunsan jinjinar alak'ar dake tsakaninsa da mahaifin yarinyar, sun kuma san babu yanda za'ayi ya iya auren Amatallah, danshi matsayin d'iyarsa yake kallonta, bai ta6a banbanta matsayin Amatallah dasu Abul-khair ba. Sai dai kuma matansa sun gaza gane hakan, ayanzu haka suduka insunga Amatallah d'in bazasu iya ganetaba, saboda tadad'e batazo kano ba.
A baya basu nuna kishin Amatallah d'in, amma tun zuwan dayayi jos sati 4 daya wuce kar6o maganin baba, saiya d'auki pictures d'in Amatallah a wayar babanta (abokinsa), shikam harga ALLAH bada wata manufa yayi hakanba, shiyyasa daya dawo yanuna musu hoton dansuga yanda tak'ara girma, shima kusan 3years bai gantaba, suna ganin hotunan suka canja fuska. tundaga lokacin ko maganarta yayi saisun nuna jin haushinsu, yarasa miyasa suke hakan shikam?.......
Ta6asa datayine yasashi dawowa hayyacinsa, har yanzu bata saki fuskaba tace, ''gasu Na had'a".
Mik'ewa yayi yana fad'in ''to sannu da k'ok'ari, ya d'auki sauran abin dazai buk'ata da tsarabar daya yoma Amatallah yasaka a madaidaiciyar bag d'in data had'a masa kayan.
Jakar ya d'auka, yad'ago yana kallonta, tsaye take jikin mirror, tayi kicin-kicin da face, ahankali yatako gabanta, yad'an murmusa kafin ya rungumeta a jikinsa, acikin kunne yaymata rad'a, sannan ya sumbaci la66anta da goshinta yana fad'in "saina dawo".
Duk da maganarsa tasaka zuciyarta yin sanyi, amma saita gimtse, batace komaiba tabiyo bayansa, jakar takar6a suka sakko k'asa tare.
Babu kowa a falon, yara duk suntafi school.
Kallonta yayi yace, ''bara nayi sallama da Fateema".
Kauda kanta tayi daga kallonsa, batace komaiba.
Gaba yay abinsa, zuciyarsa Na mamakin kishi irin na mata. komin k'ank'antar Abu sai sun nuna kishi akansa, musamman Aneesa tafi fatima kishi.
A Falo ya tadda Uwargidan tashi zaune tana kallo, tamasa sannu da zuwa.
Amsawa yayi yana zama kusada ita, idonsa akan TV yana kallon film d'in datake kallon. sai kuma ya maida kallonsa kanta.
" Fateema zanje Jos ne".
"Jos kuma Nurri? Da ranarnan? Ko jikin babane ya motsa?".
" a'a, ba jikin baba bane, zan dai kuma amso masa maganin nan ne, daganan naduba jikin Amatallah batada lafiya, sunama Asibiti an kwantar da ita".
Dukda maganarsa ta soki zuciyarta amma saita danne, tace, "ayya ALLAH yabata lafiya? Mike damunta haka?".
" Uhm to, bandai saniba, d'azu nake waya da Brother shine yake sanarmin."
Azuciyarta tace shine kake sauri katafi tunda ga 'Yar Goal. afili kuma tace, "ALLAH yabata lafiya to, a gaida mana dasu".
"okey zasuji".
Harya mik'e yakoma ya zauna, yakula da yanda itama yanayinta ya canja, amma dayake tafi Aneesa hankali tayi k'ok'arin danne kishinta, yay murmushi yana fad'in "koma abinda zan tuna baza'a baniba?".
Kamar zatace bagashi zakaje inda za'a makaba. saikuma ta danne tace, ''to mikake so?".
Girarsa d'aya yad'age yace, " komima?".
Kumatunsa ta sumbata.
Shima haka ya sumbaci nata, sannan suka fito.
Aneesa Na falo tsaye, tagama cika fam da haushi, koda suka fito bata kallesuba tayi gaba abinta, binta kawai yayi da kallo, itakam Fateema saita ta6e baki tana Harar bayan Aneesa.
Har jikin motarsa suka rakashi, Aneesa tasaka masa bag d'in a gefensa, bayan yatada motar yamik'o musu hannunsa Na dama, d'aya bayan d'aya sukayi musabaha
, sannan yace, "abama yara hak'uri nayi tafiya basu saniba, sannan dan ALLAH karna dawo naji abinda zai 6ata raina, Ku kama kanku, insha ALLAH 2days kawai zanyi nadawo".
Atare sukace insha ALLAH bazakaji komaiba, ALLAH ya tsare.
Yace, " amin to my Sweet wife's". dan son tsokanar su yace, " Amma bakuce na gaida Amaryaba".
Kowacce kauda kanta tayi gefe basuce komaiba, dan bak'aramin dukan zukatansu maganar tayiba, ashedai hasashensu gaskiyane?.
Da sauri Aneesa tashige ciki tana hawaye.
Chapter 7 · 0% Book details