← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 66

Sashe 44

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

A falo ta iskesu shida yaransa, duk suna a jikinsa kowa nabada labarin abinda aka koya musu, sallamarta tasakashi d'ago idanunsa ya kalleta. Koda suka had'a ido saita sakar masa murmushi, hakanne ya sanyaya zuciyarsa daga haushinsu dayakeji.
"Sannu da zuwa Uncle". tafad'a murya k'asa-k'asa.
Dukda surutun yaran hankalinsa Na kanta, kuma yaji mita fad'a. ya d'auke idonsa akanta yamaida kan Abulkhairi, "Abulkhairi kuje maza a canja Uniform ayi alwala nima ganinan sakkowa mutafi masallaci kunji".
Atare suka mik'e suna fad'in to Abbbunmu.
Daga shi har Amatallah da kallo suka raka yaran, kowa Na murmushi.
Ya maido kallonsa kanta, " my best kinyi k'yau da goyon kuwa".
Murmushi tayi kanta a k'asa tace, "ngd Uncle, kadawo lafiya".
Still murmushi shima yayi, ya kwantar da kansa jikin kujerar yana kallonta, " ba godiya zakiminba tunda ba k'yautar Siddiqar nabakiba, kawai kema kidage ki haifomin naki".
taji kunyar maganarsa, Dan haka ta kauda kanta gefe tana murmushi.
Yasa hannu yakamo nata, cikin zolaya yace, ''kokuwa yau zamu samune ma kawai nayi shiri?".
Batasan sanda ta dubeshiba tana zaro ido waje, shima yayi yanda tayi, sai suka tuntsure da dariya kuma.
Tace, "kai Uncle".
Yace, "ALLAH my heartbeat ".
Murmushi kawai tayi, shikuma yashafi kumatunta, "Matsoraciya wasa nakeyi, sorry nataho Na barki a school ban nemekiba, 6atamin rai akayine".
'Dan kallonsa tayi da mamaki, har zatayi magana saikuma tayi shiru, gwarama kawai tabarsa a yarigata tahowar.
"Fad'i mana".
Yayi maganar idonsa akanta.
" a Uncle babu komai, gashi can ana kiran salla".
"Alhmdllh" yafad'a tareda mik'ewa yashiga bedroom d'insa, babu dad'ewa yafito, da alama alwala yayo da brosh. Zama yayi inda ya tashi, yaci dabino uku yasha ruwa kafin yamik'e yana shafar gefen kumatun Amatallah, "bara naje masallaci babyna".
"Adawo lafiya" Amatallah tafad'a a kunyace".
Itama sakkowa tayi danyin sallar, ta sauke Siddiqa agadonta tashiga bayi.
Su Uncle basu dawoba saida akayi isha'i, zuwa sannan tad'an gyara fuskarta da hoda da kwalli da d'an janbaki kamar yanda Anty maijidda da Nazeefa suka gargad'eta akan bakoda yaushe ake zuwa wajen miji fuska a kod'eba.
Ranar dai Uncle yaci girkin Amatallah yana mata Santi, itako sai dad'i takeji tana dariya, daga Fateema har Aneesa babu Wanda ya tanka, yara kuwa suna taya Abbunsune.
Yauma a d'akinta ya kwana, tasha kunya kamar jiya, koma nace fiye da jiya, Dan yaukam Uncle kasa barinta yayi harda 'yan wasanni, Wanda ganin ta tsorata yak'yaleta daga baya sukasha barcinsu, dukda yarigata barci ita tsorone ya yanata saida taji yayi.
*_5days ogo_*.
Kwanakin Amatallah 6 kenan da kar6ar miji, a kwana shidannan ba'a maganar shak'uwarsu, dan koyaya dai tasaki jiki dashi, dama kuma hakan shine fatan Uncle d'in. gashi kuma gobe Fateema uwargida zata kar6eshi ko Aneesa, duk kuma sai Amatallah taji babu dad'i, koba komai tasaba da kwanciyar dasukeyi tare a gado d'aya.
Da daddare suna kwance, barci sukeyi hankali kwance, Amatallah Na jikin Uncle ta dabaibayeshi kamar zata shige jikinsa. bugun k'ofane ya farkar da Uncle, ga Amatallah kam hakan bamai sauk'i baneba, saboda shegen nauyin barcinta.
Da k'yar yazame Amatallah a jikinsa yatashi gabansa na fad'uwa, tabbas yasan babu lafiya, yakumafi kawo hakan ga Fateema.
Ilai kuwa yana bud'ewa yaci karo da Aneesa wadda take a rikice, sai yarfa hannaye take tana safa da marwa.
Yana bud'e k'ofar tayo kansa, " dear Umman yarace babu lafiya, ina k'yautata zaton ko nak'uda wlhy......"
Abinda yafaru shine tun farkon dare bayan Uncle yashiga sunyi sallama takejin babu dad'i dajin alamomin ciwo, amma harya fita bata iya fad'a masaba dankarya tashi hankalinta, saima ALLAH yakawo barci ya figeta da wuri, acikin barci ta farka da matsanancin ciwo, cikin azaba ta d'akko wayarta da nufin kiransa, saidai takira har sau biyu bai d'aukaba, hakanne yasata maida akalar kiran ga Aneesa. Arikice Aneesa tashigo wajenta, ganin nak'udace ta d'auke yaran d'ai-d'ai tamaida 6angarenta, shine taje ta tado Uncle bayan itama takirasa bai d'agaba. Shikuma ya danne wayarne da filo harta shiga silent bai saniba, wannan ne yasa bai d'aga kiransuba.
Har rige-rigen shiga 6angaren Fateema sukeyi itadashi, zuwa sannan kuma Fateema nak'uda gadan-gadan.
Aneesa tace dear mutafi asibiti mana".
"Neesa kalli agogofa, 2:41am akwai had'ari gaskiya, mudai bata taimako muga ko ALLAH zaisa mudace ta haihu lafiya".
Aneesa tayi na'am da hakan, addu'a Uncle yafara tofama Fateema a ruwa, hannunsa rik'eda d'ankwalinta yana share mata gumi. Aneesa kuma Na taimaka mata dawasu dabarun...
A wannan time d'inne kuma Amatallah tafarka arikice saboda mafarkin Anty Fateema datayi tana kuka, ta laluba babu Uncle, ai babu shiri ta wantsalo daga gadon, hijjabi kawai ta d'ora a saman kayan barci ta tafito, tundaga falo tafara jiyo nishin Fatima da maganar Aneesa tana fad'in daure Umman yara, insha ALLAH kin kusa.
Wani nishi da Fateeman tasaki yasaka Amatallah fashewa da kuka saboda tausayi, saikuma tad'an tsagaita taji kukan jariri ko murnarsu Uncle d'in da haihuwar amma saitaji tsitt, saima gauron numfashi da Uncle yasaki tareda fad'in "Fateema!!"...............
mun shiga d'ari, kardai Uwargida.....
ba ruwana
One luv my Sweet fana
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
Chapter 44 · 0% Book details