Sashe 21
Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
**********
Uncle M.A kam dasu Nazeefa sai suka shiga kewarta, dan d'an zaman datayi yakawo sabo da shak'uwa mai k'arfi tashiga tsakaninsu.
Su Aneesa kam da Fateema dad'i sukaji, dan koba komai yanzu yarage zarya gidansu, sai dai yana zuwa kamar yanda yakeyi da, da safe kafin yatafi kasuwa ko aiki, kokuma idan ya taso.
A kuma wannan tsakaninne tafiya wani Cause a Dubai na tsawon watanni tara ya sameshi. kuma cikin gaggawa.
A daddafe yaje sukai sallama da Amatallah, yakuma sanar mata data shirya Jabeer zaizo akan makarantarta idan result ya fito, amma sai dai tayi hak'uri, k'ilan zata koma Kano da zama fa.
Kanta ta jinjina masa tana k'ok'arin maida hawayenta.
Shiru yayi yana kallonta, murya a sanyaye yace, "bak'yason Kano ko my best?".
Da sauri tace, " a'a Uncle, inaso wlhy".
Guntun murmushi yayi kawai, yace, "OK shikenan to, ammafa ba wajen Innani ba wannan karon".
Kallonsa tayi, murya na rawa tace, "Uncle ina to?".
Shima saiya kalleta da d'an murmushi yace, " gidana, kobak'ya son zama?".
Hawayen datake mak'alewane suka zubo, amma batace komaiba.
Hannunsa kawai taji akan kumatunta yana goge mata hawayen, muryarsa can k'asan mak'oshi yafara lallashinta.
"Kiyi hak'uri Khadija, mu kar6i jarabawar mu da hannu biyu, ni kaina ina cikin rud'ani wlhy, bansan yanda zuciyata zata d'aukeki a matsayin matata ba, bayan kuma matsayin d'iya mafi soyuwa kike dashi agareni, banida wata mafitane akan hakan, saboda alk'awarin rik'eki naima Brother yayinda Numfashinsa yarage k'iris ya k'are daga gangar jikinsa."
"Kullum cikin tunanin mafita nake, amma nakasa samowa, ni kaina inajin tamkar mun cutar dake, gashi kuma bakin alk'alami yarigada ya bushe, dan banida damar ruguje alk'awarin danaima brother bayan k'asa ta rufe idonsa. kiyi hak'uri, insha ALLAH komai zai zama labari, lokaci na zuwa dazamu fara kallon kammu ni da ke amatsayin miji da mata kinji".
Kai kawai ta iya d'aga masa.
Waya mai k'yau ya bata a kwalinta, " ga wannan ki rik'e, nasaka miki Number ta, duk abinda kike buk'ata kobai mikiba ki kirani ki sanar mini, da nayi tunanin kicigaba da zama wajen Innani harna dawo. to sai kuma baba yace hakan bai daceba, gara kawai a kaiki gidan, k'ila kafin na dawo kin saki jikinki, ga
d'ina nan duk sanda kike buk'atar kud'i saikiyi amfani dashi, Nazeefa zata dawo gidan itama harna dawo, karki yarda wani Abu ya had'aki da Aunty's naki kinji, (duk da ma dai bayan tafiyata d'aya a cikinsu zata Bini) kibasu girmansu kamar yanda na sanki, kuma kicigaba da hak'uri akan duk abinda za'a miki bai mikiba, (duk da dama nasan ked'in mai hak'urice), duk Wanda yamiki wani Abu a cikinsu ki kirani ki sanarmin kinji."
Nanma kanta kawai ta jinjina masa.
"Yawwa my best D.. , ALLAH yay miki albarka, d'inkunanki nacan Nazeefa takai da duk abinda kike buk'ata, banda wasa da karatu, banda tarkacen k'awaye, ki maida hankali sosai, kuma dan ALLAH kirage yawan damuwarnan kinji ko".
Yanzuma kanta ta jinjina.
Yace, " kimin magana please naji mana".
Yanda yay maganarne yasakata murmushi, ta share ragowar guntun hawayenta, "ngd sosai Uncle, ALLAH ya biyaka da mafificin alkairi, Yakuma Baka nasara akan abinda zaka nema".
" amin my best D..., ngd da addu'arki, yanzu miza'a bani dazan ringa tunawa".
"Uncle mikake so?".
" komai nasamu inaso my best D.."
Shiru tayi alamar tunani, zuwa can ta kalleshi, "Uncle kafad'a, ni narasa mizan Baka ai".
Murmushi yayi yana kamo hannun damarta.
Kallo tabishi dashi dantaga mizaiyi da hannun.
Bud'e yatsunta yayi sosai sannan yakai bakinsa tsakkiyar tafin hannunta ya sumbata.
Wani yarrr taji ajikinta, harda 'yar girgiza da runtse ido.
Ya d'ago yana kallon fuskarta da murmushi.
Saurin kama k'ofar motar tayi zata gudu. Yay saurin rik'o hannunta yana fad'in " yazaki gudu baki baniba?".
Wata matsananciyar kunya da mamakin sane ya cika Amatallah, a zuciyarta tace dama haka Uncle yake? naga ta kaina.
Ba yanda baiyiba amma tak'i juyowa ta kalleshi, ganin bazata juyo d'inba saiya zame gyalen kanta tareda d'an kwalin.
Idanu Amatallah ta zaro waje dan mamaki wannan aiki na Uncle.....
Kafin takai k'arshen mamakinta taji ya zare pink d'in Ribbon d'in data d'aure tsaka tsakin gashinta daba wani tsawone dashiba.
Yana zarewa tasamu ta fice, da gudu tashige gidan kakanninta da yayan Ammi da k'aninsa ke ciki yanzu.
tabar Uncle da dariya.
Ribbon d'in ya saka a hannunsa sannan ya d'auki d'ankwalin atanfarta data bari ya d'ora a cinyarsa, ya tada motar kawai yatafi, yanamai jin wani nishad'i dashi kansa baisan ma'anarsaba...........
*_ALLAH ka gafartama Mahaifanmu
[1/16, 1:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_*
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
____________________
*_Number 13_*
____________________
Da sallama ya shiga d'akin.
Amatallah dake zaune a bakin katifar Nazeefa tana canja rigar filo da sauri ta juyo tana amsa sallamar cikin rawar murya. jikinta har rawa yakeyi.
Shiru yay yana kallonta. Sai yaji babu dad'i ganin yanda yanzu kamar tsoronsa takeji, saima yazo gidan sau uku bata bari sun had'uba, yau ma yasan k'ila batasan yazo ba.
Murmushi gefen baki yayi, ya d'an kauda kwayar idonsa daga kanta saboda zanine kawai da vest a jikinta.
''My best D......", sai kuma yakasa k'arasawa, yace, " kintashi lafiya?".
Da sauri tace, "Uncle sorry ina kwana".
Yanzun ma murmushin gefen baki yayi, kafin ya amsa, ya kuma kallonta kad'an, "bak'ya jin sanyine? Kika zauna haka?".
Gaban tane yafad'i, tama manta da kayan dake jikinta, hijjab tajawo da sauri ta saka, wata matsanan ciyar kunya takuma lullu6eta, saita koma ta zauna bakin katifar ta kifa kanta a cinya.
Zama yayi bisa wani stool dake d'akin, cikin sanyin muryarsa yace, " yanzu yaya kikejin jikinki?".
Bata d'agoba, ta amsa da "naji sauk'i, sai dai yawan ciwon kai".
" tunanifa kenan my best?".
Kanta ta d'ago, idanunta cikeda kwallah ta girgiza masa kai batareda tayi maganaba.
Shima kan ya girgiza mata alamar kartayi kuka.
Ta saka hannu ta share hawayen dasuka fara bin kumatunta.
Mik'ewa yayi tsaye dan bayaso ta karya masa zuciya, yace, ''inaga zuwa Monday zan nema miki school d'in dazaki koma, anfara Reghestiretion d'in SSCE, koba k'yason ki zana a wanan year d'in sai next year?".
Share hawayenta ta shigayi tana murmushi, "a'a Uncle inaso zanyi".
Murmushi yayi saboda ganin tana kuka tana dariya, ya matso kusada ita Yakuma k'asa da muryarsa kamar mai tsoron kar a jisu, yace, "kimin alk'awari to".
Yanda yay maganar sai bugun zuciyar Amatallah ya k'aru, ta d'ago manyan idanunta dasuka yi d'an ja ta kalleshi.
Ya jinjina kai alamar ta amince.
" uncle alk'awari kuma?".
"Yes my best".
" uhm Uncle nami to?".
Komawa yayi inda yatashi zaune yasake zama kan stool d'in, "my best inason kimin alk'awari zaki rage yawan damuwa, rashin kwanciyar hankalinki nawane, kukanki yana ta6amin zuciya ainun Khadija, ki daure wajen kar6ar wannan jarabawar tamu, duk sanda kikaji zuciyarki cikin k'unci ki d'auki alkur'ani ki karanta, su brother addu'armu suke buk'ata kawai a yanzu kinji".
Kanta ta d'aga masa tana share hawaye, " uncle insha ALLAHU duk zanyi".
''Yauwa my dear, ALLAH yay miki albarka". 'Yay maganar yana mik'ewa'.
Amatallah tace, "amin".
Agogon hannunsa ya kalla yana fad'in " bara naje to, idan na dawo saimuyi magana ki za6i school d'in da kikeso ko?".
"To Uncle, amma ko wacce kaza6amin tamayi".
"Shikenan, amma baradai Na dawo d'in".
Kanta ta jinjina masa, sannan tamasa addu'ar dawowa lafiya.
Yana murmushi ya amsa sannan ya fice.
A tsakar gida yatarar da Nazeefa.
"Lah Yaya dama kana gidannan?".
Murmushi yayi yana kallonta gaidashi tayi, ya amsa yana tambayarta babu dai wata Matsala akan Amatallah ko?.
" eh wlhy Yaya tarege yawan kukan bakamar da ba, kuma danaga zata fara tunani sainayita janta da hira danta saki jikinta, amma nakula kamar bata isashen barci".
"Nima nalura da haka kam Nazeefa, Dan tama min complain akan kanta yana ciwo".
" rashin barcine da tunani Yaya".
"Babu damuwa, insha ALLAH zan d'auki mataki, kedai kicigaba da k'ok'ari wajen rage mata yawan tunani da damuwar, a satin nan zan nema mata school dazata zana SSCE d'inta, maybe hakan yad'an d'auke hankalinta".
" yawwa yaya, hakan ma yayi sosai".
"Yawwa bara na wuce time Na tafiya, yau bazakije school bane?".
" eh Yaya. Yau bamuda exam......