Sashe 39
Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nima natafi wajen nawa Uncle d'in ___________________________ *Washe gari* Kusan 3:39am ya farka kamar yanda ya saba a kowacce ranar lahadi daren litinin, dakuma laraba daren Alhamis, sauran ranakun kuma yakan tashi tun around 2 randa kuma nauyin jiki da gajiya suka hanashi shikenan, yanda Amatallah ta katantanesa saiyayi murmushi, hannu yasa k'ark'ashin filo ya d'akko k'aramar wayarsa ya kunna fitila ya haska ta, ba k'aramin shigewa jikinsa tayiba, gashi da alama andad'e da d'auke wuta ma, sanyin asuba daya fara busowa yad'an sassauta zafin garin, cikin dabara ya janyeta a jikinsa tareda gyara mata kwanciya yamaye gurbinsa da filo, gani yay tad'an gyara sosai tareda kuma k'ank'ame filon tacigaba da barcinta. Murmushi yakumayi kafin ya fice, shaf ya manta baisa ta ajiye masa kayan tea ba, ALLAH ma yasoshi kowacce tanadashi a kitchen d'in 6angarenta, kitchen d'in falonta yashiga, wanda kowacce tanadashi, saikuma na gaba d'aya Wanda yake a babban falonsu, inda ananne kowacce keyin girki ranar duty d'inta,, haskawa yayi yana son ganin plas d'in tea d'inta da addu'ar ALLAH yasa tana ajiye Hort water kamar sauran, can ya hangoshi a kusurwa, yamatsa yana d'agawa da tunani, ''Alhmdllah" yafad'a yayinda yaji nauyi, nan dai yahad'a shayi mai sauk'in kauri, ya bud'e fright d'inta kota ajiye bread tunda ana ajiyema kowa, kusan uku yagani alamun bata cima ita kenan, saikuma k'ananun cake Wanda da alama ita tasiya kayanta ta ajiye, cake d'in dake nannad'e a ledoji gudun karya bushe ya d'auka guda 2 da ruwa yafito, bedroom d'in ya koma, ya ajiye kayan hannunsa saman k'aramin table d'in fake gaban sofa yawuce bathroom yayo brosh, yana shan tea da cake idonsa akan Amatallah, shikad'ai yasan miyake kissimama zuciyarsa, hardai yagama tsaf yakoma bayi yay alwala, abin salla ya shinfid'a sannan yasaka jallabiyarsa ya kabbara salla. Har aka kira sallar farko yana nafilfilinsa, a lokacin yamik'e yay rakata'ainul fijir sannan yatada Amatallah da k'yar saboda tanada nauyin barci. Ganinsa a d'akin yatuna mata tarefa suka kwana, kanta a k'asa tashige toilet, shikuma yafita yana murmushi. Kamar yanda ya saba d'akin kow accensu yashiga yatadasu, ya taimakama Fateema tayi alwala saboda nauyin datayi, sannan yatada yara suma da taimakonsa sukayi alwalar, d'akin Aneesa yakoma shima Saifudden ya tadadashi, dukda Aneesa tatashi bata tadashiba saboda tasan shike tashinsu kullum. Dukda k'ank'antar yaransa hakan bai hanashi horonsu da zuwa sallar asubahiba komin sanyi ko ruwa, saidai in bakada lafiya kokuma shima bazaijeba akan wani dalili mai k'arfi, saisuyi agida gaba d'aya, amma dai tilasne saika tashi kayi sallar.............. _jiyakam kunjini shiru, dama nasanar daku inada wasu uzurirrika, wlhy da k'yarma nake cire time d'in muku typing, shiyyasa zakuga ko comments d'inku ban tankaba kwana biyu, saima yau nasami damar dubawa, ngd sosai, kuna sakani nishad'i, ina alfahari daku dajin dad'in yanda kukema mahaifina addu'a, ALLAH yabar k'auna, kuma kunan araina daram, shiyyasa nake daurewa nayi typing danna sakaku farin ciki wlhy One luv my sweet Fan's *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_* [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing *_HASKE WRITER'S ASSO..._* _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce ______________________ *_Number 24 and 25_* ______________________ Ta6a k'ofar yay yajita arufe dan haka ya kwankwasa, da k'wankwasa k'ofar da bugawar zuyar Amatallah lokaci d'aya suka kasance, dan tabbas tasan shine, tunda tajiyo hayaniyar yaransa suna ihun murnar dawowarsa. K'ara bugawarsace tasakata mik'ewa dole tanufi k'ofar tana k'ara gyara zaman siririn gyalenta da k'yau. ta bud'e k'ofar cikeda fargabar k'arfa fama kanta gwiwa, sai dai me suna had'a ido da boss jarumtar ta tafara k'ok'arin su6uce mata, matsawa tayi yashigo yana sa6a babbar rigarsa a kafad'a idonsa a kanta yana binta da kallon k'urulla, gani yayi kayan sun kuma k'ank'antar da ita, amma tayi k'yau sosai. Zama yayi a kujerar kusa dashi, wadda ta kasance 2seaters, Amatallah kam tuni ta zube a k'asa tana gaisheshi cikin d'an rawar murya, dan dukkan ALWASHIN ta (Ummu Aysha) dataci bayan barowarta makaranta zuwa yanzu saitaji kwarjininsa ya fatattakeshi. Bai amsa gaisuwarba sai kiran sunanta dayayi cikin sassanyar muryarsa. Ta d'ago manyan idanunta tad'an kalleshi, saikuma ta maidasu k'asa tana cigaba dayin wasa da yatsun hannunta. Yatsun hannun yabi da kallo, wad'anda haryau rad'am suke da zanen jan llalli da 6ak'i, yasaki guntun murmushi mai sauti Wanda har Amatallah d'inma saida tajishi. "My best zonan". ya fad'a yana mik'a mata hannu kamar wata tata Batayi musuba tamik'e kanta a k'asa taje inda yake, tana k'ok'arin zama a k'asa yaruk'o hannunta tareda jawota ta fad'o saman cinyarsa. A fili tace, "ya sallam!!, Uncle Sorry". tayi yunk'urin mik'ewa, a zatonta ko asfa kuskure tafad'a kansa. illahirin jikinta duk rawa yakeyi, dan tunda uwarda ta haifeta duniya hakan baita6a faruwa da itaba ko'a mafarki, dukda cud'anya cikin k'abilu daban-daban da Amatallah tayi hakan baisa koda kuskure wani namiji yata6a rik'e hannuntaba bayan mahaifinta da Uncle M.A, shima kuma saida igiyar aure ta tabbata kansu sannan yafara mata hakan, sai dai kuma idan ta mantane......... Kuma mannata dayay da jikinsa yana sauke sassanyar ajiyar zuciyane ya maido Amatallah daga tunaninta, " Uncle please ". tafad'a tana kuma yunk'urin kwace jikinta. A cikin kunnenta yace, " aji tausayin bawan ALLAH mana my heartbeat". Tsigar jikin Amatallah Ce tatashi yarrr tareda yamutsawar 'yan hanjin cikinta Na tsoro. tafara tuno maganar Fa'iza, ta girgiza kai a zuciyarta tana fad'in bazan iyaba Fa'iza, kimar Uncle tawuce zaton kowa a garen.......... Batakai k'arsheba taji wani bak'on al'amarin dayafi Na zama cinyarsa girgizata, rufe idonta datayi yabama Uncle damar k'arema fuskarta kallo har zuwa la66anta da sukasha lipstick sunata k'yalli, kasa hak'uri yayi kamar yanda yaso, sai kawai ya manna bakinsa akai. Saida ya tabbatar yashanye lipstick d'inan tas sannan ya janye bakinsa. Ai da gudu Amatallah ta sauka daga jikinsa tashige bedroom d'inta, bataja birki a ko inaba sai toilet d'inta. jingina tayi da k'ofar tana hakkin gudun datayi da sauke numfashi, ga hawaye sha6e-sha6e a face d'inta. Shikam tana barin jikinsa yabita da kallo, harta shige sannan yay wani k'asaitaccen murmushi maihad'eda guntuwar dariya, shikansa yana mamakin kansa akan zurfafa cik'in k'auna da begen d'iyar cikinsa, abinda ko'a mafarki bai ta6a wanan tunaninba, hargashi yau takaishi ga rashin hak'uri ya aikata abinda shi Kansas kunyar Kansa yakeji, ya lumshe idanunsa yana furzo iskar bakinsa dawani murmushin dayake k'ara fidda ainahin k'yawunsa da kwarjinin kamala da ALLAH ya azurtashi dashi. ganin bazata fitoba kusan mintuna uku yatashi ya fice. A falo Yakuma iske yara suna kallon Cartoon Na larabci, sun maida hankalinsu sosai akan TV, dan haka baiyi maganaba yashiga 6angaren Aneesa. Zaune ya taddata a fallo, sai dai kallo d'aya yamata yagane tasha kuka, zama yay kujerar dake kallonta, cikin tsare gida yace, "lafiya dai ko?". Maganarsa takuma tunzuro Aneesa, tawani turo baki gaba tana kuma d'aure fuska itama, a tsiwace tace, " wai minamaka kake wulak'antani irin haka? miye laifina danna soka? kokuwa wannan shine salon sakayyar dazakamin bayan karaboni da k'asata da iyayena......." Wani banzan kallo yamata, Wanda yasata 6ame bakinta babu shiri, tasan halinsa sarai yatsani raini da rashin tausasa harshe, amma itama rantane yagama 6aci akan abinda yamata da safe bai isheshiba yak'ara mata wani yanzun. Maimakon yabata amsoshin maganganunta se cewa yayai "miya had'aki da Amatallah da safe?". Ranta Yakuma 6aci, shaid'an Na angiza zuciyarta tace, "Woow! dama munafuncina akayi a wajenka shiyyasa kake wulak'antani? itakuma da salon data shigo gidan kenan? kaima miji munafuncin kishiyoyi...." ''Aneesa!! Karfa kibari fushina yakai k'arshe a kanki, ki sanarmin abinda Na tambayeki". a fad'ace yayi maganar, amma hakan bai hana muryarsa fita cikin sanyiba da nutsuwa. Dukda Aneesa takai k'arshe a 6acin ranta hakan bai hanata tsorata da Shiba, tasan halinsa sarai, Duk abinda kaga ya tanka a Kansa, to lallai ya d'aukeshi da girma, amma komi matarsa zata masa Na 6acin rai bata Isa ya mata ihu ba, saidai yayi abinda kema zai bak'anta ranki cikin ruwan sanyi, rabonta dataga irin wannan Fushun a taredashi tun fad'an k'arshe dasukayi da Fateema lokacin daya had'esu gida d'aya, dan lokacinma dukansu gida yace su tafi saiyazo, saida babansa ya hana sannan ya hak'ura saboda gaya masa da sukaje sukayi......... Tunaninta ya katse lokacin dataga yamik'e yafice bai sake cemata komaiba, binsa tayi da kallo ranta Na suya da mamakin Amatallah, lallai zata gyarama yarinyarnan zama a gidannan, wato ita kuma NATA salon had'a fad'a da miji ko, idonta harya kai tsaurin haka, ai ko tayi Na farko tayi Na k'arshe, zata shayar da ita mamaki. Nace ''hummm". Yanzunma yaran basu luraba harya haye samansa, ransa gaba d'aya a 6ace yake da Aneesa, dan harga ALLAH bazai d'auki k'untatama marainiyar ALLAH ba, mahaifinta yabashi itane dan ganin zai iya rik'e masa ita, bakuma zai yuwu wani ya k'untata ta yabariba koda wanene wlhy. kayansa ya cire yashiga wanka, koda yafito k'ananun kaya yasaka bak'in dogon wando da farar t-shirt mai gajeren hannu, yad'an fesa turare yadawo falonsa, saida yabud'e freight ya d'akko ruwa ya d'auki kofi da aka jere a wata 'yar glass drawer sannan ya zauna saman kujera, koda yasha ruwan saiya zame ya kwanta tareda lumshe idanunsa, ba barci yakeba tunanin tattaunawarsu da Alahaji sabi'u yakeyi, dakuma yanda suka tsara abubuwa, ahaka har tunaninsa yakoma kan rayuwar data shud'e, kewar Brother d'insa tadawo masa sabuwa a zuciya, ayanzu abubuwa dayawa suna damun zuciyarsa amma babu Wanda zai sanarmawa, yashare 'yan kwallan dasuka taru masa a gefen ido kafin yakai dubansa ga agogo, 9:34pm, wayarsa ya jawo da zummar kiran Fateema saikuma ga kiranta ya shigo, guntun murmushi yayi sannan ya d'aga, saida tamasa sallama ya amsa sannan tace, ''najika shirune Nurrina, koka fasa ne?". d'an huci ya furzar, kafin yace ''a'a my tee...., yara fa?". "Gasunan harsun gaji da jiranka sun kwanta saboda school". " oh sumin afuwa, tunda sun kwanta kuzo kawai". "Okey". kawai tafad'a ta yanke wayar. Amatallah ya kira, tana ganin kiransa gabanta yafad'i, a tsorace ta d'aga wayar, muryarta har zuga take, kansa kawai yad'an girgiza, yace, " khadeeja kin kwantane?". Sunan daya kirata dashine yasata d'anjin sassauci a zuciyarta, danta kula sai akan muhimmin Abu yake kiran ainahin sunan nata. a sanyaye tace, "a'a karatu nakeyi". Murmushi yayi mai sauti yace, " okay, tom kizo samana yanzunnan". bai jira amsartaba ya kashe kiran. Hannu tasa aka tana fad'in "nashi 100 ni Khadija, mikuma zanma Uncle a