← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 66

Sashe 65

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alhmdllh wannan lamari yakuma k'ara fiddo kimar Uncle a idanun duniya, nanfa wasu manyan k'ungiyoyin duniya na matasa suka fara gayyatarsa domin zama Na musamman, harma dawasu shuwagabannin k'asashe.
Uncle yazama babban gwaska, tauraro abin alfarin MATASANMU da k'asarmu, kowa burinsa yayi mu'amulla dashi, dolensa ya ajiye aikin dayakeyi a bayaro, dan nauyi yamasa yawa sosai, ga iyali ga aikin al'umma.
Dukda wad'annan nauye-nauyen hakan bai hanashi cigaba da tattalin iyalansaba, saima abinda yay gaba, suma kuma suna tattalinsa dabashi kulawa, kowacce tana kishinsa da k'ok'arin kafa babbar fada a zuciyarsa.
Duk d'insu yana yabama k'ok'arinsu da jinjinama halin dattakonsu, dan kishinsu shine yakamata asamu akowanne gidan aure, saidai yasan wani zafin kishin yakan had'a da zalincin wasu mazan
ALLAH dai ya shiryesu Uncle.
**************
Ana gab da za6e sukasha binkin Aysha da Dr yazeed, Wanda Uncle ne komai a bikin, duk wata hidima daya kamata iyaye suyi shine yayma Aysha, kuma baigazaba wajen zuwa takanas ya fad'ama danginta komai, harma da rok'onsu wasu sushiga lamarin auren, koba komai dai d'iyarsuce, kimarsa da halin dattako yasakasu nad'o gari zuwa bikin, tabbas jikinsu yayi sanyi daganin Goodness (Aysha) bata rasa komai Na rayuwaba, saima d'aukaka da ALLAH yak'ara mata, ga miji ga karatunta mai yankeba, Wanda fatansu tasha wahala sabida rashin tallafinsu, a haukarsu hakan zaisa tadawo addininsu, shiyyasa suka koreta, to Ashe Na kwarai basa k'arewa, saigashi ALLAH yaymata nasibi da samun wasu dagin masu k'aunarta.
Bata nuna musu komaiba, saima kar6arsu da nuna musu har yanzu sunada muhimmanci a rayuwarta, dan ba'a canjama tuwo suna.
Su Ama.... Sune amarori k'irjin biki.
Ahakadai taro yatashi lafiya, amarya tatare gidan mijinta, Innani harda hawayenta Na rabuwa da Aysha, dan harga ALLAH tana k'aunar yarinyar har cikin ranta.
To shatu ALLAH yabada zaman lafiya da zuria d'ayyiba.
************
Za6e yagudana cikin lumana da kwanciyar hankali kamar yanda su Uncle sukayi fata, Alhmdllh kuma ansamu biyan buk'ata daga matasan wajen za6en shugabanni Na gari masu kishin k'asar dason cigabanta.
Sannan matsan dayawa sunsami wasu fannoni Na madafun ikon k'asar , kamadaga ministers, Commissioners, da wasu fannoni daban-daban Na muk'amai
Saimuce ALLAH yatayaku rik'o
******* ****** *******
Yau takasance Juma'a, tunda Uncle yadawo sallar juma'a shida yara bai sake fitaba, sukayi Lunch gaba d'aya kamar yanda yazama doka yanzu agidan, duk weekend tare sukecin abinci suda yaransu.
Sallar La'asar tasaka taron firar watsewa, Uncle da yara suka tafi masallaci su Aneesa kuma kowa tashige d'akinta.

Da sauri Amatullah tak'arasa gaban gadon ganin Raihana dake barci Na neman sakkowa, tatashi tuni, kasancewar yarinyar tanada matuk'ar hak'uri ko kuka batayiba, tagaji da wasa agadon shine tafara k'ok'arin sakkowa, ALLAH ma yakawo Ama... d'in datasha k'asa.
Dungure mata kai Ama... tayi tana fad'in "mamana dakin fad'o Aida kinjamin masifa wajen Uncle nasan bawai zai ragamin baneba".
Kamar Raihana taji mi Ama... ke fad'a saita ta6e Baki tana niyyar yin kuka, rawa Ama... tafara mata tana rera mata wak'a kamar yanda take musu itada Rayyan idan suna rigima.
Tuni Raihana tayi shiru takoma 6alle Baki tana dariya, Ama..... ta sauketa tana dariyar itama, yauwa Ammi Uwa mai dad'i, zauna kiyi wasa nayi salla kafin Rayyan yatashi shima, yau inada Shiga kitchen".

Idar da sallarta babu dad'ewa tajiyo kamar ana magana sama-sama daga babban falo, kuma tamkar muryar Aneesa.
Cire hijjab tayi ta d'auki Raihana dake wasa a k'asa tafita (dan tuni yaran sunama rarrafe).
" momyn yara lafiy......."
Maganar Ama... takatse lokacinda idonta ya sauka akan zee-zee dake zaune itada Rita dawasu 'yammata biyu Wanda duk Amatullah ta sansu amma ta manta sunansu.
Aneesa ta katseta da fad'in "kokin sansune Auntyn yara?".
Sosaima kuwa, aiduk school mate d'inane, ''amma lafiya kuwa Rita?".
Yatsine fuska Rita tayi tana wani
taunar cingom, a yangance ta nuna zee.
Ama.... Ta maida kallonta ga zee d'in, ''Zainab lafiya?".
Saida Zee tamata wani kallon sama da k'asa sannan tace, "maigidan nazo nema".
Fateema dake fitowa tace, " maigidan kuma? shikam Nurri miya had'ashi da wad'annan masu kamada kilakin?".
Daga zee har muk'arabanta babu wacce ta tanka, saima taunar Cingom sukeyi, jikake k'ass! k'ass!! k'ak'as!!!.
Saida suka gama shan k'amshinsu sannan d'aya daga cikin 'yanmatan biyu tace, "Amaryarku ce tazo gaisheku ".
Kallon juna Aneesa da Fateema da Amatullah sukayi, Aneesa sarkin rashin hak'uri tafara lailayo musu zagi.
K'in tankawa sukayi, saima cigaba da iya shegensu sukayi.
Ana haka maigidan yadawo, kallon matan nasa dasuka tsareshi da idanun tun shigowarsa yayi, " lafiya kuma kukam?".
Aneesa Ce ta nuna masa su zee tana k'ara kumbura baki.
Gabansa yafad'i, azuciyarsa yace yarinyarnanfa ta gundureni, yanzu abin yakai harma gidana..........?
Fateema ta k'atse tunaninsa, "Nurri waisu waye sune?".
Kallonta Uncle yayi, sannan ya kalli yaransa dake tsaye cirko-cirko suna kallon iyayensu da wad'annan bak'i dabasu san kosu wayeba.
" Abulkhairi ja k'annenka kuje tsakar gida kuyi wasa, kar Wanda yadawo sai an kirasa".
"To Abbu".
Suna fita Uncle ya kalli su Zee.
" miya kawoku gidana Zainab?".
Kanta ta sunkuyar k'asa tana wani murmushi, "nagane kusan 2weeks baka picking calls d'ina shiyyasa nace bara nazo naga lafiya".
Tsayuwarsa yagyara sosai, hannayensa zube cikin aljihun blue d'in jallabiyarsa, ya fiddo d'aya yashafa gemunsa sannan ya maida, cikin sauke numfashi yace, " k'alau nake, kawai ayyukane sukamin yawa, ngd".
Yana gama fad'a yanufi samansa batareda yakuma kallon kowacce acikinsuba, harsu Amatullah d'inma.
Wani mayataccen kallo zee tabishi dashi, yanda ma yake taka steps d'in benen kawai abin birgewane, harya kai k'arshe kuma bai juyo ya kallesuba.
Su Aneesa suncika sunyi FAM, shin me mijin nasu yake nufine? Budurwar tasace kenan da gaske?.
Ai bak'inciki hana Amatullah maganama yayi, saita juya 6angarenta kawai.
Aneesa ce tafara masifa, "to gayyar tsiya arna a idi sai a tashi abar mana gida ko, tunda bana gado baneba".
Su Rita zasuyi magana Zee ta hanasu, tamik'e tsaye tana fad'in " kutashi muje, karku wani damu kanku, kwana nawane nazama matar gidan nima, kowacce shegiya acikinsu saita bar gidan da k'afafunta, dan nikad'ai nakeson kasancewa da abin sona, duk d'unsu basukai matsayin Na had'a kishi da sub.......
Dukan da Aneesa takaima bakinta yasakata yin shirun dole, tadafe baki "kai kai nikika dakarma baki?"....
" andaki bakin naki, Ku kama gabanku ma kafin mu jigataku a falonnan''. Cewar Fateema.
Kwafa su Zee sukayi suka fice.
Fasifa k'awayen nata suka hau yi bayan sun fita, akan miyasa bata bari sun koyama matannan hankaliba.
Tace, "kubarsu, lokacinsune, daga sanda nashigo gidan babu mai sake yin tari acikinsu, kudai kusaka ido kusha kallo."
Dariya suka shek'e da ita damata jinjina.
Koda su Zee suka fita sai Aneesa da Fateema suka nufi saman Uncle, a zaune suka iskeshi hankali kwance yana searching tasha a TV, sallamarsu kawai ya amsa batareda ya kallesuba, dan yasanma miya kawosu.
Fateema tace "wai yanzu nan Nurri wannan kuma wacece?".
Kallonta kawai yayi ya kauda kansa,
Aneesa takuma maimata masa tambaya, " Dear maganafa mukeyi! Wacece wannan kilakin?".
"To mikukeso Na fad'a muku? Nace ba abinda kuke tunanin bane, kumin kallon mayaudari, kokuwa nace sona take ni bana sonta ku kirani mak'aryaci, inama mai baku shawarar karku tasirantar da abinda bakuda ilimi akansa a zuciyarku.
Babu wacce ta tanka masa acikinsu, sukayima ficewarsu suka barmasa falon.
Kallo kawai yabisu dashi, ya sauke ajiyar zuciya ta 6acin rai, tabbas lokaci yayi dazai takama yarinyarnan Zainab birki akan haukarta, tunda har tsaurin idonta yakai ta kwaso k'awaye tazo masa gida wajen iyalansa, harma tadunga musu furuci mara k'yau, (dan yana jiyo duk abinda yafaru bayan barinsa wajen), iyalinsa sune mutuncinsa, martabarsa da dukkan sirrinsa, bazai lamunci wata ko wani ya raina masa suba ko 6ata rayukansu, yayi kwafa yana jingina kansa jikin kujerar da lumshe idanu.
Yakai tsawon lokaci yana tunani awajen kafin ya sakko k'asa, babu kowa a falon, yarama suna tsakar gida suna wasa, ya kalli 6angaren Aneesa yaga arufe, Fateema ma a rufe, saiya nufi Na Amatullah.
Tunda Ama... tajiyo k'amshin turarensa ta ajiye Rayyan datake bama nono tashige bathroom, tanajin Rayyan d'in ya fashe da kuka amma bata kulaba tarufe bayin.
Da sauri Uncle ya k'araso ya d'aukeshi, jijjigashi yafraayi yana fad'in "oh my brother na, waye yasaka kuka? Ina Antyn tajene?".
Rayyan yayi shiru tareda lafewa jikin babansa, sai ajiyar zuciya, zama yay falon yana jiran fitowarta, amma bulum, mamaki yakamashi, yatashi yalek'a bedroom d'in babu kowa, sai Raihana a kan gado data koma barci, zama yayi abakin gadon yana jiran fitowarta, nanma shiru kakeji.
Ama.... kuwa zamantama tayi a toilet d'in tana charting hankalinta kwance, duk kuma bidirin da Uncle keyi tana jiyoshi. tashiyay yafara knocking d'in k'ofar bathroom d'in, amma shiru kakeji. mamaki yakamashi, kodaima bata d'akinne? wannan tunaninne yasakashi ficewa da Rayyan a hannu, tsakar gida yafita inda yaran ke ball, zama yay yana kallonsu da tunanin lamarin matan nasa fal a kansa, wato dai sun had'e masa kai kenan, yay murmushi da k'arajin k'aunar matan nasa a ransa
Kiran Sallar magriba tasakashi tasa yaran maza gaba suka tafi masallaci kamar yanda yasaba, yabama Ummita Rayyan suka koma falo itada Siddiqa da mah-mah.
Jin sunfita masallaci Ama.... tayi sallah sannan tashiga kitchen nata, tadafa cus-cus. taimaza takai masa nasa ta sakko kafin su dawo.
Chapter 65 · 0% Book details