Sashe 5
Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Sallar da baban Ama... Bai fitaba kenan, sai a gida yaja iyalansa jam'i.
__________________________
*KANO STATE*
Kallo d'aya zaka masa ka tabbatar a gajiye yake Driven d'in, a hankali ya furta "ya sallam". saboda go slow d'in daya hango agabansa, ya sauke ajiyar zuciya, tareda yamutse fuskarsa mai cikeda kwarjini, a gogonsa ya kalla dake d'aure a tsintsiyar hannunsa Na haggu, ya dafe goshinsa dan ganin yanda lokacin sallar magriba ya gabato sosai.
Gaba d'aya ransa a 6ace yake, dayasan zai gamu da go slow d'inan daya hak'ura yayi salla kafin ya taho.....
Tunanin sane yakatse saboda Ringing da wayarsa tafara. batareda ya d'aukaba ya kai dubansa kan screen d'in wayar.
My wife tee..
Yagani 6aro-6aro yana yawo a fuskar wayar, ya d'an furzo iska kad'an daga bakinsa. d'aukar wayar yayi yana k'ok'arin kiranta sai kuma takuma kira.
Koda ya d'aga saiya saka Hans free, muryarsa mai matuk'ar sanyi da nutsuwa yace, " Assalamu allaiki Ummu Abul-khair".
"Wa'alaikassalam Nurrina, lafiya kuwa har yanzu baka shigoba? ko ka manta kana azumi ne?".
Murmushin sa ya saki mai k'ayatarwa, ya kai hannu yana shafa gemunsa daya k'awatu da bak'in gashi dakuma fari d'ai-d'ai (furfura). "Ban manta ba My tee.., wlhy go slow ne ya rik'eni, gashi har an shiga sallah".
Ya karashe maganar cikin 6acin rai.
A san yaye tace, " sorry Nurri, ALLAH ya kawoka lafiya to".
"Amin nagode, su Abul-khair fa? Kundai turasu masallaci ko?".
" eh sun tafi shida Sahib".
"Saifuddin fa?".
" bayajin dad'i,
koma islamiyya bai jeba".
"Amma shine bata fad'a min ba?".
Har zata bashi amsa saiya katseta, " kinga ina zuwa, naga motocin sun ragu". 'Bai jira cewartaba ya yanke wayar'. Motar yay ma key yay gaba, saboda hanya data bud'e, dama dai wani abunne ya haddasa go slow d'in.
Cikin mintunan dabasufi 30 ba ya k'araso gida, a k'ofar gida yay parking, yafito yay alwala a nan massalacin k'ofar gidansa, hankalinsa duk yana kan sallar magriba data wucesa, a gaggauce ya gaisa da mutanene dake k'ofar massalacin zaune suna jiran kiran sallar isha'i, ya shige yay sallar magriba, ya idar babu dad'ewa akayi isha'i.
Bayan an idar ya tsaya gaisuwa da jama'a makwafta sannan yakoma mota, horn yayi sau biyu.
Kusan mintuna 5, aka bud'e gate d'in. bayan ya shige ta maida gate d'in ta rufe. Sannan ta k'araso wajen motar tasa.
Yana zaune har yanzu a ciki, wayoyinsa yake k'ok'arin sakawa a aljihu, ta bud'e motar tana fad'in ''sannu da zuwa".
"Yauwa Uwargida na, ya gidan?".
"Lafiya lau yake". K'o k'arin fitowar dayake yasata matsawa baya, ya fito idonsa akanta, kwalliyar tata tamasa k'yau, haka kullum matan nasa suke cikin kwalliya, kowa burinta tazama gwana awajensa.
Murmushi yamata yana kashe ido d'aya, cikin sassanyar muryarsa yace, " kinyi k'yau my tee...".
Itama murmushin tamasa, kafin tace, "thanks you Nurrina".
Kansa ya jinjina mata, "da akwai kaya a backseat ki d'ebo su".
"Okey".
Yara ukune suka fito da gudunsu suna fad'in "oyoyo abbunmu!!".
Murmushi yasaki, har fararen hakwaransa Na bayyana, idonsa akan yaran nasa, ya bud'e masu hannayen sa, hakanne yabama babbar rigarsa ta blue black d'in shadda bud'ewa. gaba d'ayansu suka shige ciki, ya had'asu ya rungume shima yana fad'in " oyoyo my children's, I Miss you all".
Matarsa data gama kwaso ledojin dake kujerar baya tatsaya tana kallonsu fuskarta d'auke da murmushi.
Tace, "oya to a sakeshi ko yagaji, kumuje ciki".
Sakinsa sukayi su duka, yakama hannun Sahib da Ummita, Abul-khair mai d'an wayon ya kar6i wasu daga cikin ledojin hannun mamansa, suka nufi hanyar k'ofar babban falon gidan.
Sahib da Ummita kam sai zabga masa labarin school sukeyi, murmushi kawai yakeyi.
Da sallama suka shigo falon, nanma wata matar nagani tsaye a falon, hannunta rik'eda yarinya dake kunshe cikin kayan sanyi.
Wannan ya tabbatar min cewa matansa biyu
Fuskarta d'auke da murmushi ta k'araso inda suke tana masa sannu da zuwa.
Amsawa yayi shima yana murmushin da k'arema amaryar tasa kallo cikin jin dad'i, dan itama cikin kwalliyar take mai d'aukar hankali. (A raina nace, ''wannan ai sai a gaza gane mai girki
Hannu ya mik'a mata alamun tabasa babyn hannunta.
Ta saka masa babyn dabazata wuce 3month ba a hannun nasa.
"O, my Siddiqa barci kikeyi?". Yay maganar a hankali yana sumbatar goshin yarinyar. Sannan ya mik'a mata ita, " bara naje Na d'an watsa ruwa Neesa!".
Cikin salon kissa tace, "okey Dear".
Harya fara tafiya saiya tsaya, ya juyo yana kallonta, " Saifudden fa?".
"Jimm tayi alamar tsoro, ta kauda idonta daga kansa tace, " yana barci".
"Barci? A wannan time d'in? Halan lafiya?".
Yanzunma a cikin jimamin tace, " bashida lafiya".
"Shine kika kasa kirana ki sanar min?". bai jira amsarta ba yafara hawa matattakalar benen dake tsakkiyar falon, dama tuni yaran mamansu tajasu sunyi 6angaren ta.
Kamar zata fasa kuka tabishi da kallo, tasan haushi yaji, Dan mijin nasu bai had'a matsalar 'ya'yansa data kowaba, yanason yaransa sosai, kodan yadad'e bai samu haihuwarba ne? Oho.
Jiki a sanyaye tashige nata 6angaren itama.
Tun daga falon k'amshi mai dad'i yabugi hancinsa, ya shak'a ya lumshe idanunsa, babbar rigarsa yafara k'ok'arin cirewa, ta k'araso da sauri ta taimaka masa suka cire tare.
Cikin kashe murya tace, " da kanka Nurrina? ".
Murmushi kawai yay yana shigewa bedroom d'insa. da sauri ta d'auki babbar rigar tabi bayansa domin taimaka masa yayi wanka...............