← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 66

Sashe 61

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

***** ******* *****
Ranar Asabar d'in week d'in Abulkhairi yashiga layin yara masu zana jarabawar fita daga primary, shima zai wuce secondary insha ALLAH A wannan year d'in, yaron yagirma, kamanninsa da Uncle suna kuma fitowa sosai, hakama Sahib shima yaron yayi girma, dan dakad'anma Abulkhairi zai fishi tsawo, yamafi Abulkhairi wayo.
A ranar Monday d'in kuwa Amatallah ta zabgama Uncle wayo dankar suje asibiti, dan itafa tsoro takeji taje ace akwai matsala.
Dukda yaganota haka ya k'yaleta, dama shimad'in bayason aje asibitin.
Agurguje please
Rayuwar tacigaba da tafiya ahaka, yau fari gobe tsumma, yau dad'i gobe hak'uri, ansha sunan yaron Nazeefa, (Sulaiman). su Amatullah kam anata karatu, dukda tanada damuwa azuciyarta bata bar hakan yazama silar raunanar karatunta ba, kullum Fa'iza da Aysha cikin kwantar mata da hankali suke da nuna mata muhimmancin hak'uri da yarda da k'addara.
Hakama 6angaren danginta su kawu hafizu, koda yaushe sukayi waya yakan k'ara kwantar mata da hankali.
Shikansa Uncle d'in duk abinda zai kwantar da hankalinta da kauda mata damuwar rashin haihuwar yanayi. ganin yanda duk suka damu sai itakuma tafara rage nuna tata damuwar, tama d'auke tunaninta daga wajen gaba d'aya, ta duk'ufa gayama ALLAH kukanta dayawan azumi, sadaka dadai sauransu.
To Ama..... ALLAH dai yasa mudace
****** ****** ******
"Wai lafiyarki kuwa Ama......?"
"K'alau Fa'iza, mikika ganine?".
" kawai tun jiya nifa wani sukuku nake ganinki, tamkar wata mara lafiya".
Kanta ta kwantar jikin kafad'ar Aysha tana jan k'aramin tsaki, "kibari kawai, nifa jikin nawane ma duk babu wani dad'i, kuma babu inda yakemin ciwo wlhy".
Da sauri Fa'iza tace, " tin yaushe kika faraji?".
"Yanaga kin wani tsorata? bafa wani abu bane".
Cikin dariya Aysha tace, " aimu fatanmu yazama wani abun, nifa wani k'yauma naga kinayi kwanan nan hajiyata, miye sirrin?".
Duka Ama... takai mata, Aysha ta goce da sauri tana dariya.
"To miye na dukanta? ba gaskiya tafad'aba? baby ALLAH yasa abinda muke fatane dai, amma koni wlhy naga kin k'ara k'yau, maganace dai kawai banyiba".
" uhm kuma daina wahal da kanku, ni banida komai, kawai inaga malaria keson kamani dai".
Dariya suka mata, akadai bar maganar ahaka, kowa kuma ak'asan ransa yana addu'ar ALLAH yasa abinda suke fatane
Kwana biyu dayin wannan maganar Ama.... ta tashi da zazza6i mai zafi, gashi ranarma Uncle ba d'akinta yakeba, yana wajen Aneesa.
Har zasu fara break fast babu Ama...., dayake weekend ne.
Uncle ya kallesu yana fad'in wai Khadija fa?".
Aneesa tace, "Wlhy nibanga tafitoba tun d'azun, Siddiqa ma tashiga tafito tace barci takeyi, tona d'auka ko gajiyace tahanata tashi da wuri".
Fateema ma tace, " ni wlhy kwana biyunnan ma sainaga kamar Auntyn yara batajin dad'i sosai".
"Nima nad'an zargi hakan, harma Na tambayeta amma tacemin babu abinda ke damunta, bara dai Na dubata kawai".
Sukace to.............
Manage please
One luv
[1/25, 12:25 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{
home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_*
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
____________________
*_Number 39/40_*
____________________
Tundaga falo jikinsa yafara sanyi, dan babu alamar tayi gyara, da sallama yashiga bedroom d'in, babu amsa, ya kalli gadonta, tana k'udundune a bargo tarufe har kanta, da sauri ya k'arasa ya yaye bargon.
"Khadija lafiya kuwa? da uban zafinnan kika lullu6........"
Maganarsa ta tsaya a mak'oshi saboda yanayin daya ganta, ga jikinta zafi zauu, har wani huci ke fitowa.
"Ya salam my best!" yafad'a yana zama gefen gadon, hannu yakuma kaiwa a wuyanta ya ta6a, tarik'e hannun da sauri tana rawar sanyi, "Uncle please bar ta6ani, hannunka sanyi".
"dama bakida lafiya amma baki fad'aba Khadija? kuma har tadaki nazo nayi da asuba".
" Uncle sannan zazz6in ya saukane, banyi zaton zai dawoba da safe".
"Dashi kika kwanama kenan?".
Kanta tad'aga masa tana wani lumshe idanu dakuma dunk'ulewa waje d'aya saboda bargon daya cire mata.
Tashi yay yashiga bayinta, yahad'a ruwa maid'an zafi sannan yadawo, ya taimaka mata tasakko tanata rawar sanyi da fad'in "Uncle please kabarni Na kwanta, ina ganin jirine".
" Sorry my best! Bara namiki wanka kiji d'an k'arfi saimuje Asibiti".
Tirjewa tayi tana tura baki gaba, "nidai Uncle basai munje asibitiba, danasha parasitemol zan warke".
" to naji shagwa6a66iya, muje dai ayi wankan first ".
Da kansa yamata wankan, ya taimaka mata suka fito, a bakin gado ta zauna, ya d'akko Vaseline ya shafa mata, tanata langa6e masa itafa jiri take gani, hakadai ya lalla6ata yasaka mata doguwar riga bak'a.
Fita yayi itakuma takoma ta kwanta harda jan bargo takuma lullu6a, taji dad'in wankan, dan ciwon jikin saitaji yaragu harma da zafin.
Yana fitowa suka hau tambayar miya faru da Ama.... d'in?.
"Batada lafiya Ashe, zazzabi takeyi, Aneesa had'a mata break fast d'inta".
Sun nuna jimamainsu akai, Aneesa ta had'a break fast d'in ta d'auka da kanta domin kai mata, Fateema da Uncle sukabi bayanta.
Da k'yar tatashi tasha kunun bayan su Fateema sunmata yaya jiki, ta amsa dak'yar tana tambayar ya yara suka kwana.
Uncle yayi yayi tatashi suje koda camix ne tunda yau babu aiki amma tak'i, itadai yabata perasetimol tasha kawai.
" nifa bazan baki maganiba kai tsaye, nasani ko ALLAH ya share kukanmu ne, kokuwa salon nama kaina ganganci".
Baki ta turo masa tana matso hawaye, "amma Uncle kofa masu tsohon ciki sunasha, kuma babu abinda yake musu, tunda a asibiti muna badawa aii".
Shiru kawai yayi yana kallonta, yama rasa mizai cemata, daga k'arshe dai saishi ya hak'uran, yabata tasha takoma ta kwanta.
Chapter 61 · 0% Book details