← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 66

Sashe 24

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Rashin comments d'inku kesani wannan laziness d'in, buk'atar typing d'ina kullum yana hannunku
, inkun gyaran nima zakuga sauyi a gareni
*_ALLAH ya jik'an iyayenmu
[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_*
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
____________________
*_Number 16_*
____________________
Da gudu ta wuce Furera matar kawunta yayan Ammi dake tsakar gida tana wanke-wanke.
"Ke Amatallah lafiya kuwa?". Anty Furera tafad'a a tsorace tana zare hannunta daga ruwan wanke-wanken, ganin tawuce d'aki itama tatashi da gudu ta shige inda Amatallah tashiga harda rufe k'ofar.
Ganin haka da Sadiya tayi matar k'anin Ammi itama saita afka d'akinta ta banke k'ofa harda sakata.
Sufa duk zatonsu wasune suka biyo Amatallah d'in, gashi mazan gidan duk basanan sun fita.
Tashi Amatallah tayi daga kwanciyar datayi a gadon Anty Furera danjin tarufe k'ofa.
''Lah Anty Furera lafiya kuwa kika rufe k'ofar?".
" keza'a tambaya Amatallahi, miyafaru kika shigo gida da gudu haka?".
Sai yanzu Amatallah tatuna da yanda tashigo, dariya tashiga tuntsurama Anty Furera, dan ganin jikinta har rawa yake saboda tsoro.
Sai da Anty Furera tamata magana sanan ta tsagaita da dariyar datakeyi, "Anty Furera babu komaifa, wai da kina zaton minene?".
Ajiyar zuciya Anty Furera tasauke, " kai Amatallahi kin d'auki hak'ina wlhy, kinsan garinan ba lafiya yacikaba, har yanzu a d'ar-d'ar kowa yake, waya biyoki haka to?".
Guntuwar Dariya Amatallah tayi, ''kai Anty Furera haka kike da tsoro ashe?, babu komai wlhy, bud'e kiga wayarda Uncle ya siyamin".
Amatallah tayi maganar donson kauda tanbayar da Anty Furera kemata.
Bud'e d'akin tayi, sai lokacin itama Anty Sadiya tabud'e nata.
Fitowa tayi tana tambayarsu ko lafiya taga sun shiga d'aki?".
Labari Anty Furera tabata, A
matallah bata bari zancen yayi tsawoba tabasu kwalin wayar suka shiga kallo da yaba k'yanta.
***********
Uncle M.A kam haka yabar jos cikin farin ciki da kewar brother d'insa, dan baibar garinba sai da yabiya ta gidan su.
Komai ya k'one, da Alama ma ankuma sakama gidan wutane, dan randa abun yafaru gobarar bako ina ta cinye hakaba, amma yanzu harda gidajen makwaftansa, bayan kuma waccan ranar wutar bata ta6a kowanne gidaba, anguwarma gaba d'aya tayi kaca-kaca.
Mota yakoma yatafi kawai, wani 6angare na zuciyarsa na tuno masa abinda yafaru tsakaninsa da Amatallah, sai yakanyi murmushi, lokaci-lokaci kuma yakan kama d'an kwalinta dake kan cinyarsa ya shak'i k'amshin.
Haryaje Kano ribbon d'inta na a tsintsiyar hannunsa. sai da zai shiga gida yacire d'ankwalin yasaka ribbon d'in ciki ya nannad'e ya tura a aljihu.
Yau girkin Fateema ne, dan haka ita tabud'e masa gate. yauma kamar kullum a cikin kwalliya take, hakama yaransa suna gida saboda Alhamis ce babu islamiyya kuma ana hutun boko, itama Aneesa cikin kwalliyar tafito tamasa sannu da zuwa, suduka basusan ma inda yajeba.
Da taimakon Fateema yay wanka, sanan ta shirya masa abinci, bai ciba sai da suka dawo sallar Magrib shida yaransa.
Suna kammala cin abinci suka fita sallar isha'i, daga can gidan su yawuce da yaran gaba d'aya, suka gaida kakanninsu.
Sun dad'e agidan suna hira shida Jabeer da Shehu da Nazeefa, Rabin hirar duk akan tafiyarsace dakuma Amatallah, innani dai bata saka musu Baki sosai, amma tana saurarensu, baba kam tunima yayi barci, dan babu laifi jikinsa da sauk'i.
Basu koma gidaba sai da yaga plashing d'in Fateema, dole yatafi shi kad'ai yabar yaran nan, dan dare yayi, kuma duk sunyi barci, gashi a Napep sukazo ba motaba, shima mashin d'in Jabeer ya kar6a yatafi a kai.
___________________________
Gobene takama tafiyar Uncle, duk abinda yakamata ya kimtsa yayisa, abinda ya danganci gidansa dana mahaifansa duk yamik'ashi hannun Jabeer, hakama lamarin kasuwa, dukda akwai yara masu kulada shagunan, amma dole sai da mai kulawa lokaci-lokaci.
Abu d'ayane ke damunsa arai dabai samu koda kafa harsashin saba, yarasa wazai fara tunkara da batun? Dan bakowa baneba yakeda zuciyar irin wannan jihadin, musamman ma daya kasance abune da sai an ta6a aljihu.
Zuciyarsace tashiga bashi shawarar kiran Sabi'u m Ali. Wayarsa ya d'auka sai dai zuciyarsa na fad'a masa yakira ko karya kira, danya kai tsawon wata 10 rabosa da waya dashi, dama can yafisu k'ok'arin kira a waya dama zumincin dagashi har marigayi.
Shawara ya canja, yafara masa test massage. kusan mintuna 15 saiga kira yashigo. Wayar ya d'auka yana k'aramar dariya, Dan ganin Alhaji Sabi'u ne. Sai da ta tsinke sannan shi ya kira. Alhaji Sabi'u na d'agawa Uncle M.A yafara bashi hak'uri kawai.
Dariya Sabi'u yayi daga can yace, "ya zanyi daku, kai da Isma'il ko kad'an bakwason zuminci dani na lura".
" a'a wlhy, ba haka baneba, amma amana afuwa kanmu bisa wuya".
"Hhh shikenan ya wuce aii, ya gida ya iyali?".
" duk lafiya lau muke".
''To Alhmdllh".
Gyaran murya Uncle M.A yayi, sannan yace, "wlhy maganace a bakina, gashi kuma ban saniba ko kana kano?".
" eh ina Kano, ai munma dawo gaba d'aya, zirga-zirgan ta isheni ne".
"A lallai na yarda munada laifi sosai a wajenka, yanzu nan har kadawo da iyalinka Kano amma babu labari balle a k'ulla zuminci?".
" to nima nayi laifi amin hak'uri, bama su dad'eba, 3month's kenan da dawowar, kaina bisa wuya".
Still dariya Uncle M.A yayi, yace, "shikenan to, indai ban takuraka ba zuwa 4:pm insha ALLAH zan shigo, Dan gobe zan bar k'asar ne".
" mutumina ina kuma zaka fad'a haka? Halan kaida Isma'il ne?".
"A'a, nasan namaka laifi gaskiya, amma Isma'il ALLAH yamasa rasuwa kusan 6month's ago". yak'are maganar hawaye na cika idonsa.
A can kuwa Sabi'u ya masifar rikicewa, sai sallalami yakeyi, dole Uncle M.A ya yanke wayar, dan k'ara karya zuciyarsa yakeyi. kusan mintuna goma sannan Sabi'u yasake kira, yamasa ta'aziyya sosai sannan yace babu damuwa yazo su had'u a gida, zai turo masa address d'in inda suke yanzun.
Uncle M.A yamasa godiya sukayi salama. Jin gina yayi da kujera ya furzar da huci, a hankali ya furta ALLAH yajik'anku brother, I miss you so Much wlhy.
Har Fateema tashigo ta shirya masa abincin Karin kumallo a k'asan carpet bai saniba, ya Lula sosai a duniyar tuna rayuwarsa da Brother d'insa.
Ganin shirun yayi yawa Fateema ta k'arasa kusadashi ta zauna. Sai da ta ta6a kafad'arsar sannan ya juyo yad'an kalleta.
" haba Nurri tunanin mikake hakane?".
"Kansa kawai ya girgiza mata baice komaiba".
Shuru tai tana Kallonsa kawai, amma fuskarta ta nuna alamun shiga damuwa.
Hannunta yakamo yana murzawa a hankali, cikin sassanyar muryarsa yace, " my Tee... ina tuna brother ne".
Tausayi yabata sosai, tasan har Abadan mijinsu bazai ta6a manta Baban Ama ba, Dan ubangijine kad'ai yasan irin k'aunar dasukema junansu. hannu tasa tad'an shafi k'asumbarsa zuwa gemu, sorry Nurrina, kacigaba damasa addu'a, muma duk ita muke jira, ALLAH ya gafarta musu sukuma".
"Amin ya rabbi".
" please abinci to, karya huce".
'Dan murmushi yayi ya sauka yana fad'in "wayo dai za'amin. yara fa?".
" taf ai wad'an nan tuni suka karya tun kana barci".
"Tofa lallai, yau kuma ba'a jira Abbu ba?".
" hhh aiko dai basu jirakaba, harma mai lesson d'insu yazo".
"OK, bara nima kiga na karya, fita zanyi naje nadawo da wuri, sonake yau na yini a gida ina kallonku kawai".
" kai Nurri, saikace wad'anda zasu mutu?".
"Mutuwarma ai bamuda tabbas d'in rashin zuwanta my tee".
"hakane kuma Nurrina".
Bayan ya kammala break fast yay wanka, gayu sosai yaci cikin shadda galila brown color mai duhu, yayi k'yau sosai, ya d'ora hular zanna bukar itama brown. Fateema dake fesa masa turare sai k'od'a k'yan dayayi take.
Murmushi yayi yana kashe mata ido d'aya, " my tee fesamin turarennan sosai, wata k'ilma nasamo ta hud'u".
Daina fosa turaren tayi, ta wani had'e fuska ta juya masa baya.
Dariya sosai yayi, har hakwaransa na bayyana, ya rungumeta ta baya yana mata magana a kunne, "my tee... bakwason ta hud'un ne?".
Juyawa tayi suna kallon juna, ta d'ora d'an yatsanta saitin zuciyarsa, idonta akan face d'insa, shima kallonta yakeyi yana murmushi, " Nurrina indai ina cikin nan
ban damuba, kayi in dai amaryace, ai kowa da halinsa zai zauna."
Rungumeta yayi yana murmushi, "my tee... Karyi kokwanto kinji, kinacan k'asan-k'asan zuciyar Muhammad, babu kuma wata mace dazata iya tureki ko wacece ita kin gane".
Dad'ine sosai yakama Fateema, takuma rungumeshi tsam ajikinta tanaji kamar tashige kawai ciki, a hankali tace, " I love you more my Nurri".
Shima a hankalin kamar mai tsoron ajisu yashiga jero mata kalamai masu kwantar da hankali, kai kace itaka d'aice matarsa babu wasu.
Hakan da Alhaji Muhammad kema matansa yakesa kowacce d'aukar kanta itace mowa, Dan duk matar data kasance tana tare dashi, yakan nuna mata soyayya tamkar ita kad'ai gareshi, shiyyasa suke masifar kishi da juna, kowacce d'auka take anfi sonta da k'aunarta.
Shikam yanayin hakane danya saka kwanciyar hankali da farinciki a tsakaninsu, kuma Alhmdllh yaci nasara da salonsa
Tare suka sakko falon k'asa, ya shiga 6angaren Aneesa.
A falo ya isketa tanama Siddiqa kwalliya, idonta a k'ofa harya shigo dan tunkan ya shigo k'amshinsa yayo gaba, ba k'aramin d'aukar hankalinta kwalliyarsa tayiba.
Ta sakar masa murmushi, shima ya maida mata murtani yana zama kusada ita.
"Dear irin wannan d'aukar wanka haka? ina zuwa?".
" zanje Jos ne wajen amarya".
Baki tad'an ta6e badai tace komaiba.
"Ko bak'yason najene?". 'yay maganar yana d'aukar Siddiqa dake cinyarta'.
"ni a suwa dazan hanaka zuwa wajen matarka?".
Kusada ita yamatsa sosai, yasa hannu d'aya ya sak'alo k'ugunta dashi tareda kuma mannata da jikinsa, "ke a matata wadda nake tsananin so mana my Neesa".
Kallonsa tayi tana wata dariya ban yardaba.
Goshinta da la6annta ya sumbata yana kuma mannata jikinsa da fad'in " kobaki yardaba ne my Neesa?".
"Humm dear kenan, zaka wajen wata kuma kanamin dad'in baki, da dai a baya dai na yarda, amma yanzu kam ganganne".
Siddiqa ya gyarama kwanciya a cinyarsa yana dariya, " My Neesa kice yanzu ni kinbar yarda dani Ashe?".
"Ya zance nabar yarda dakai kuwa, na yarda dakai mana, akan wannan maganar daine kam sai a hankali".
" lallai naga ta kaina, to maida wuk'ar, babu inda Muhammad d'inki zaije my lover, zanje cikin garine wajen wani abokina, insha ALLAH yanzu zanje na dawo, sonake yau na kasance daku Ku kad'ai, fitarma danta zama dolene da banyiba".
Murmushi tamasa, harda masa kiss a kumatu.
"Ya mik'e da Siddiqa a kafad'a, " humm my Neesa kishi".
Itama mik'ewa tayi tana dariyar, "yo kaga laifina ne dear?, Kasan kuwa yanda nake jinka kuwa? ba k'aramin danne zuciyata nakeba idan naga wata mace ta ra6u da kai, amma babu yanda zanyi, haka ALLAH ya k'addaramin raba dai-dai d'inka da wasu mata". ta k'are maganar kamar zatayi kuka.
Tausayi tabashi, dan shi kansa yasan Aneesa na matuk'ar k'aunarsa fiyeda tunanin mai tunani, shiyyasa shima yake mata uzuri akan wasu abubuwan, murya a sanyaye yana kallon kwayar idonta yace, " I love you so much my Neesa".
jikinsa ta fad'a, tahad'ashi shida Siddiqa ta rungume itama tace, "I love you Abadan my Heartbest".
Sosai yakuma mannata da jikinsa, yana sakar mata tagwayen kisses a wuya.
ho Uncle Muhammad kazama na......., uhm babu ruwana dai
Lokacin dasuka fito falo tuni Fateema ta shak'i haushi, amma kokad'an bata nuna a fuskaba, saima wani salon kallo datake masa, hakan kuma saiya hasala zuciyar Aneesa, ta kar6i Siddiqa a hannunsa takoma batareda tamasa rakkiyarba. Fateema kuwa taji dad'in hakan sosai, ita kad'ai tarakashi, saida suka gaisa da mai ma yara lesson sannan yayma yara saiya dawo Fateema tabud'e masa gate yatafi.
Duk yanda Sabi'u yabashi Address d'in haka yabi.
Tarba aka masa ta girma, sai kace Wanda yadad'e da fad'an zaizo.
Iyalansa duk sukazo suka gaisa, shima matansa biyu da yara 7, d'ansa namiji na fari harya zama d'an saurayi.
Sabi'u yakuma yimasa ta'aziyyar Isma'il, da kuma jimamin wannan rasuwa, dan Alhaji Muhammad sai da yasanar masa duk yanda lamarin ya afku. sosai Alhaji Sabi'u yay ALLAH wadai da wanan hali irinnan 'yan siyasar k'asarmu da matasa, yakuma nuna fushinsa akan yanda irin wad'annan rikice-rikicen kan faru musamman lokacin gabatowar za6e, da an kad'a tambarin siyasa shikenan kowa yana cikin d'ar-d'ar na tsoron afkuwar tashe-tashen hankula na rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI* dakan taso a irin lokacin.
Da wanan damar Alhaji Muhammad yay amfani wajen sanar masa manufarsa shida Brother d'insa, sai dai mutuwa tai musu gaggawa.
100% Alhaji Sabi'u yabada goyon baya, da alk'awarin shima zai shiga a dama dashi a tafiyar.
Alhaji Muhammad yaji dad'i da karamcin abokin Nasu, nan dai suka tattauna abubuwa da dama dasuka shafi k'asarnan kuma suke damunmu, musamman ma yankin AREWACIN NIGERIA.
Abubuwan tamkar an shiryasune daga plan A zuwa Z.
Rikicin boko haram kamar bazai k'areba, ALLAH dai yakawo mana iyakarshi, bayan kisan gilla da akaima al'ummar arewacinmu, sannan kuma sune ake kira da 'yan ta'addar, sai dai muna murnar samun sauk'in bomb's sai kuma na satar shanu ya shigo, shima abin mamaki a arewaci kawai yake faruwa kuma jama'ar yankin ke amsa sunan 'yan Ta'addar. Zaune bata k'areba fa bayan dak'ile Satar shanu sai kuma Kidnapper's da ayanzu sune ke addabar yankin na arewacin kasar again.
Shin wannan lamarin bazai Baku mamakiba kuwa? bakwa ganin abubuwan kamar dama angama tsarasune daki-daki, idan wannan bai tasiriba sai a koma wancan?.
Miyasa komai baya faruwa sai'a arewacin k'asar kawai? alhalin bushewar idanun matasanmu batakai ga aikata irin wad'annan manyan ta'addacinba.
Ba wai dan ina 'yar arewa nake maganar nanba wlhy, sai sai kawai lamarin kan bani mamaki, yanda kowanne bala'i sun k'are a Arewacinmu. nasan kuma banima kad'ai ba, duk mai hankali yayi wannan tunanin.
Shin a ina matsalar takene?.
Manyanmu ne?.
Talakawa ne?.
'Yan siyasa ne?.
Matasanmu ne?.
Kokuwa k'ulla mana akeyi dan a ruguzamu
Chapter 24 · 0% Book details