← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 66

Sashe 13

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahaka suka kammala karatunsu Na secondary, sun rabu cikin damuwa sosai alokacin, Dan kokad'an basuyi murna da graduate d'in nasuba.
Kwanaki bakwai kacal dayin candy d'insu Muhammad yakasa hak'uri yashirya sai jos, sosai Isma'il yay farin cikin ganinsa, hakama kawu.
Har zuwa yanzu huzayya tananan da makircinta, amma zuwa yanzu Isma'il baya d'aukar raininta.
Haka suka maida Kansu kulum cikin yawo daga Kano zuwa jos, har results d'insu ya fito, suduka sunsami abinda suke buk'ata, wannane yasakasu farinciki.
Babu 6ata lokaci kuma aka shiga nema musu makaranta, cikin amincin ALLAH kawu mahaifin Isma'il yay nasarar sama musu a University ta jos.
Wannan ne dalilin dawowar Muhammad jos da zama, sai lokaci-lokaci yakanje Kano.
Sun fara University babu dad'ewa ALLAH yayma Amina yayar Isma'il rasuwa, sosai rasuwar ta girgiza Isma'il da kawu, hakama Muhammad danya santa sosai.
Rayuwar samartakar Isma'il da Muhammad abin sha'awace, dan zaratan samarine masu kulada addini da kare Kansu wajen rud'in zamani da samarinmu ke jefa Kansu. Sun maida hankali sosai akan karatunsu, kuma suna samun nasara sosai.
Suna a level two ALLAH yahad'asu da Khadija, yarinya nutsatstsiya itama, tunda Isma'il yaga Khadija yafara k'aunarta, sai dai ya 6oye abin a zuciyarsa da burin saisun kammala karatunsu ya furta mata.
Sai dai kash Ashe shima Muhammad ya kamu batareda sanin Isma'il ba, shikam yakasa rik'e hakan a ransa ya furtama amininsa Isma'il.
Hankalin Isma'il yatashi sosai, saboda k'aunar Khadija yakeyi sosai, amma haka yayta jarumtar dannewa, yabama brother d'insa kwarin gwiwwa da goyon baya 100%, shinema da kansa ya sanarma Khadija soyayyar da brother d'insa kemata. batawani basu wahalaba ta amince, dandanan soyayya mai k'arfi tashiga tsakanin Muhammad da Khadija. Isma'il kuma yanata yak'in cireta a ransa, dan har k'asan zuciyarsa yagama aminta yabarma d'an uwansa Muhammad ita.
Kullum Muhammad kan takura Isma'il akan yakamata shima yayi budurwa, yanda dasun kammala karatu sai ayi bikinsu tare.
Dariya kawai Isma'il keyi yace katayani nema brother, nifa har yanzu ban k'yalloba.

Suna gab da kammala karatunsu saiga Saliha shima ALLAH yabashi.
Muhammad yayi murna sosai, yakuma k'arfafa d'an uwansa.
Alk'awalin ALLAH ya cika, su Muhammad sun kammala karatunsu, nanma ansha tata 6urza akan komawar Muhammad kano.
Koda Muhammad yakoma gida sai mahaifinsa yajawosa suka cigaba da zuwa kasuwa, ahankali Muhammad ya dilmiya a harkar, ya kware sosai tareda kawo canje-canje masu yawan gaske a kasuwancin mahaifin nasa, kasancewar shi d'an zamanine kuma mai ilimi.
Shikam Isma'il yana jos babu abinda yakeyi, lokaci-lokaci dai yakanzo kano, yayi kwanaki ya koma abinsa.
A wannan tsakanin auren Isma'il yatashi, ALLAH bai cika musu burinsu nayin aure rana d'ayaba, dan Isma'il ne yafara angwancewa. batun yanda shagali ya kasance 6ata lokacine ma aii.
Bayan auren Isma'il Muhammad yakawo musu shawarar sukoma suyi masters nasu, (degree na biyu), 100% Isma'il ya aminta da batun. dan haka suka fara nema a University of Lagos (Lagoon), nanma sunyi nasarar samu kuwa, dan haka suka fara karatunsu cikin nasara. A lokacin Saliha matar Isma'il nada ciki.
Rashin auren Muhammad yafara damun Isma'il, dan haka yafara takura masa akan maganar Khadija.
Amsar daya saba bashice yakuma maimaita masa, akan yana jiran Khadija ne kamar yanda iyayenta sukace saita kammala karatu ta.
"Haba brother, kaikuma saika zauna saita kammala d'in?".
Dariya Muhammad yayi, yadafa kafad'ar Isma'il yana fad'in " cool dawn mana my brother, duka kwana nawane yarage? Insha ALLAH baifi watanni 7 bafa kaima kasani".
"Haka kullum kake fad'a, amma har yau ni banga wata bakwai d'in zata k'areba, kuma mizai hana kaima baba magana a tsaida rana tun yanzu, bayan ta kammala sai musha biki kawai".
Shiru Muhammad yayi yana nazarin maganarsa, zuwa can kuma yace, " gaskiyarka fa brother, kaima kazo da shawara".
Babu 6ata lokaci sukayi amfani da shawarar Isma'il aka kai kud'i aka tsaida rana, sai ta kammala karatunta.
Watanni bakwai na cika kuwa akasha biki, lokacin Saliha ta haihu d'an baizo da raiba.
Wattani shida tsakani saliha yakuma samun wani cikin, amma Khadija dai babu labari.
Watanni tara cif Saliha ta haifi d'iyarta mace k'yak'yk'yawa.
Muhammad yayi matuk'ar farin ciki, tamkar shi aka haifamawa, komai kuwa Na hidimar sunan baby Muhammad ne yayishi, hatta da suna ma shine yarad'a mata Khadija, sunan mahaifiyar Isma'il, kuma matarsa.
Tun daga wannan lokacin Muhammad yad'auki son duniya ya azama Khadija dasuke kirada (Amatallah), komai yagani Na yara saiya siya matashi, kullun firarsa akan best daughter d'in sace.
A haka suka kammala degree d'insu Na biyu daga lagos suka dawo gida, Isma'il jos, Muhammad kano.
Muhammad yacigaba da kulada kasuwancin baba, kuma har zuwa lokacin ko 6atan wata Khadija batayiba, duk k'arshen wata Isma'il kan d'akko iyalansa suzo kano, kokuma shi Muhammad yaje danasa iyalan.................
Kubini bashi a page 11 please
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_*
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
*_Ku gargad'i mai gina ramin mugunta!!
Wannan gaskiyane
*Doctor Alhaji mamman (shata)*
ALLAH ya gafarta maka

____________________
*_Number 9_*
____________________
A k'ofar gida yay parking motar sa, sannan ya kama k'ofar zai bud'e, a rufe take.
Shiru yayi yana kallon k'ofar, yasan tunda baya nan bazasu ringa barin k'ofar a bud'eba. Mota ya koma ya d'akko wayarsa. Aneesa yakira.
A yangance tamasa sallama.
Shikuma ya amsa murya na rawa.
Gabantane yafad'i, tacire wayar daga kunnenta ta kuma kallon screen d'in domin tabbatarwar shine kokuwa?. ganin shid'inne yasata maidawa a kunnen.
"My dear! Lafiya kuwa?".
Ajiyar zuciya ya sauke, a raunane yace, " kizo ina k'ofar gida......
Bata jira yakai k'arsheba tafito da sauri. K'aramar k'ofar gate d'in ta bud'e ta lek'a.
A tsaye ta gansa ya jingina da jikin gate, gabanta yakuma fad'uwa, hakan ya kuma tabbatar mata babu lafiya.
Takowa yayi ahankali yashiga gidan, ta kalleshi tana fad'in "dear motarfa".
Kansa ya girgiza mata yace, " fita zan kumayi". yana maganar yana tafiya.
Wannan yasata binsa da sauri itama. babu kowa a falon k'asa, dan haka ya haye samansa, Aneesa na binsa abaya.
A kan gadonsa ya zube yana sauke numfashi, Aneesa ta zauna kusadashi tana tambayarsa miyafaru cikin damuwa.
Bai bata amsaba, sai dai cewa yayi ''had'amin ruwan wanka".
Jiki a sanyaye tamik'e zuwa bathroom d'insa, ruwa mai d'an zafi ta had'a masa, tana niyyar fitowa shikuma yashigo, matsawa tayi yashiga sannan ta fita.
Yana wanka yana hawaye, lallai duniya abar tsoroce, jiya iyanzu yana tareda amininsa, amma yanzu gashi awani hali mai rikitarwa, ALLAH sarki Saliha, ALLAH ya gafarta miki
Aneesa kam da sauri ta sauka k'asa zuwa 6angaren uwargidanta.
A falo ta iskesu itada yara suna homeworks d'in makaranta.
Yanda tashigo a rikice yasaka Umman abulkhair saurin kallonta, "lafiya kuwa momyn yara?".
" inafa lafiya ummansu.........nanda ta sanar mata abinda ta Sani gameda canjawar mai gidan nasu, da dawowar babu zato babu tsammani da yay musu, alhalin gobene yakamata yadawo.
Atare suka fito zuwa d'akinsa.
Bai fitoba, dan haka suka zauna zaman jiransa. Babu dad'ewa yafito, sannu da zuwa Fateema tamasa.
Batareda ya kallesuba ya amsa yana k'ok'arin shinfid'a abin sallah. Sallar magriba ya gabatar, sannan yay isha'i, duk suna zaune suna kallonsa.
Yay addu'a yana share kwallar dake bin kumatunsa.
Sosai jikin matan nasa yakuma yin sanyi k'alau, sun k'agara ya idar suji mike damunsa.
Ganin yanda suka damu matuk'a yaga baidace yabarsu a duhuba, cikin dauriyar danne hawayensa yaymusu bayani.
Daga Aneesa har Fateema kuka suke sosai.
Mukullin mota da wayarsa kawai ya d'auka yafita zuwa asibitin, yabarsu Aneesa nacigaba da kukansu.
A motama yana driven yana hawaya, yakasa jarumtar danna kukansa, tausayin Amatallah da abokinsa kawai ke nuk'urk'usar ruhinsa. a haka ya Isa asibitin.
Jabeer da kawunsu Malam Yakubu ya tarar suna jiran isowarsa.
Gaida kawu Yakubu yayi, ya amsa tareda masa ta'aziyya sannan suka k'arasa ciki.
Inda aka kwantar da baba sukaje, suduka kallo d'aya suka masa suka fara hawaye. Ba k'aramar k'una baba yasamuba gaskiya, abin ko dad'in kallo babu. barci yakeyi saboda sunmasa allurar barci kozai samu sauk'in rad'ad'in dayakeji.
Jiki a sanyaye sukabar d'akin, inda Amatallah take sukaje, tana kwance kamar yanda ya barta. matuk'ar tausayinta ya mamaye zukatansu, Uncle M.A ya kauda kansa daga kallonta saboda hawayen dasuka cika idonsa, d'an yatsa d'aya yasa ya goge sannan yanemi gefe ya zauna.
______________________________
Uncle M.A da Jabeer a asibitin suka kwana.
Wajen k'arfe 7:am suna shirin tafiya da gawar Ammi gida dan amata sutura Amatallah ta farfad'o.
Da sunan iyayenta ta farka a baki, tana kuka tana kiran Ammi da baba ta. da sauri wata Nurse taje ta sanarma doctor shu'aibu Amatallah ta farka.
Dagashi har Uncle M.A a hanzarce suka k'araso.
Tana ganin Uncle M.A tamik'e da sauri tana fad'in Uncle ina Ammina da babana!, suna ina dan ALLAH Uncle? ".
Rasa mizai fad'a mata yayi, yay tsaye kawai yana kallonta, idonsa taf da hawaye. Doctor shu'aibu ne kawai ke lallashinta. da k'yar yasamu ta tsagaita da kukan.
Doctor yamatso kusada Uncle M.A, ahankali yace, " Alhaji Muhammad yakamata mubarta taga gawar mahaifiyarta........
Bai k'arasaba Jabeer yashigo yana hakki, ''yaya! Yaya! Kuzo yaya Isma'il ne, gashi can.......
Suduka basuji k'arshen maganarba suka fice da gudu, harda Amatallah dake binsu cikin layin rashin k'arfin jiki.
'Dakin da Baban Ama ke kwance suka shiga.

Hannunsa dabai k'oneba sosai yake mik'oma Uncle M.A, yana kiran brother a ahankali. ga numfashin sa Na fita da k'yar.
Uncle M.A ya k'arasa da hanzari gareshi, shima hannun ya mik'a masa yana hawaye da fad'in sannu brother.......
Dai-dai nan Amatallah tashigo tana tangad'i, kawu yakubu da wasu mutane hud'u suma suka shigo d'akin.
K'ara Amatallah ta kwala tazube awajen saboda tozali datayi da babanta.
Dukansu kanta sukayi har Uncle M.A daya zare hannunsa daga na babanta.
Baisan ya cacumotaba yana kiran Khadija! Ke Khadija!! Please karkimin haka kema dan ALLAH Khadija. Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, ya ALLAH gareka nake, a gareka kuma nake neman taimako......yak'arashe maganar yana fashewa da matsanancin kuka.
Shima Jabeer kukan yafara ganin yanda yayansa ke kuka sai kace ba babban mutum ba.
Baban Ama ma hawaye yake yana murmushi da kallon abokinsa da d'iyarsa.
Da k'yar doctor shu'aibu yasamu ya janye Amatallah daga jikin Uncle M.A.
Chapter 13 · 0% Book details