← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 66

Sashe 48

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

(Hoooo Uncle d'inmu, kana aljannah muna binka da addu'ar fatan alkairi
Aneesa kam saida tayi hawaye a kitchen (duk dama batasan koya angwance d'in da gaskeba) tana son Muhammad harma batasan iyakaba, shiyyasa take kishinsa, itafa ko'a makaranta kishin kar afita yasata kasancewa mai k'ok'arin tsiya, bare kuma Muhammad d'inta, duniyarta, farin cikinta, tanamasa so irin Wanda batama San adadinsaba, ta wanke fuskarta sannan tafito.
(Neesa sai dai hak'uri, duk sonsa dakike k'addararki kenan zama da kishiyoyi
. Sai hak'uri dai. Nina Inason my Abdull d'ina, kuma k'ila saiyamin kishiya
Ya tarar Amatallah na shirin fitowa, taja baya yashigo, kanta a k'asa ta rissina ta gaidashi.
Murmushi yayi kafin ya amsa yana fad'in " ya gajiyarki babyna?".
Bata iya amsashiba, saima k'asa data kumayi da kanta. Bai damuba danshi kunyarta kuma tsundumashi a kogin k'aunarta yakeyi.
Yakama hannunta suka koma ciki yana tambayar INA zataje?.
A marairaice tamkar zatayi kuka tace, "Uncle please kabarni Na sauka, kaga akwai ayyuka da za'ayi, ga breakfast ga......."
Baima bari Takai k'arsheba yajawota saman gadon sosai "yo karsuci breakfast d'in Indai saikin sauka kinyi musu, ai idan wani ya ganki a k'asa saidai nanda 12 Na rana", ya rungumeta a jikinsa " kinga muyi barcinmu ma".
"Uncle!" tafad'a tamkar zatayi kuka.
Hannu yasaka kan la66anta yay mata Alamar zip
Shiru kuwa tayi Dan dolenta, wani salo yafara mata, ahankali tafara lumshe idanu Dan sak'on Na shigarta, jin yana neman canja hanya sai hankalinta yatashi (karfa Uncle yace zai k'arayine nashiga uku ni Khadija), shiru tayi tahau barcin k'arya, dukda zuciyarta Na bugawa da sauri-sauri saboda tsoro, a sannu dai har barcin gaskiya ya kwasheta, dama barcin takeji dauriyace kawai yasata son saukar dakuma kunyar aganta da safe tafito daga 6angarensa.
Jin shiru da saukar numfashinta ahankali bisa k'irjinsa yasashi lek'a face d'inta, goshinta ya sumbata Yakuma rungumeta da k'yau yana murmushi da jero mata wasu addu'oin fatan alkairi zuciyarsa, shima babu jimawa barcin yay gaba dashi.
Babu wanda ya nemeta acikinsu Anty maijidda, saima hidimar d'aura breakfast dasukeyi abinsu.
Garama Aneesa tasoyin magana saikuma tayi shiru.
Dasuka kammala breakfast d'inma Anty maijidda tace Nazeefa ta d'auka takai sama.
Har Nazeefa tashiga ta ajiye bataji koda motsinsuba, hasalima k'ofar bedroom d'in arufe take. 'Yar dariyar mugunta tayi kafin tafara gyaran falon nashi, a zuciyarta kuma tana addu'ar ALLAH yasa an gamune, sai zabga murmushi takeyi harta kammala, ta saka turaren wuta sannan taja musu k'ofar tafice abinta.
A k'asama ta iske su Anty maijidda sunata gyaran gidan, an kora yaran duka waje, 6angaren Amatallah tashiga, tayi mamakin yanda taga mirror d'in a hargitse, batace dai komai tagyara mata ko'ina, ta saka turaren wuta sannan tarufo tafito.
Bayan sunyi breakfast kuma suka shiga kujiba-kujibar d'aura girkin suna da duk abinda za'a buk'ata, zuwa lokacin kuma su Anty Mariya yayyen maijego sun dawo, Dan da daddarennan duk suka tafi gida, yanzn kuma suka dawo Dan kama girki.
*****
Koda Amatallah da Uncle basukai 12 ba kamar yanda Uncle yay fata sun kai dai 10 suna barci abinsu, Amatallah ce tafara farkawa,bayan tayi addu'ar tashi barci ta kalli yanda ta kanannad'e jikin Uncle, kai kace zata komane jikin nashi, ta tsurama fuskarsa ido tana kallo, Uncle yanada k'yau dai-dai misali, kuma yanada haske babu laifi, amma bak'ine, gemumsa da zagayayyen gashin bakinsa sune suka k'ara masa kwarjini da cikar haiba, hannu takai a hankali ta shafa gemunda tadad'e tana kwad'ayin ta6ashi saboda burgeta dayakeyi, masha ALLAH tafad'a a zuciyarta, saboda wani laushi da santsi ga k'amshi da gemun keyi, (ba dole yayi laushiba, kud'in da gemunnan ke lashewa aiba Na wasa bane).
Tunda tafara ta6a gemunsa ya farka, kokad'an bashida nauyin barci, amma bai nuna mata yatashiba, danya kula tanajin dad'in shafa gemun nasa.
Ringing d'in wayarsa yasaka ta janye hannunta da sauri, tayi k'ok'arin janye jikinta amma yak'i bata damar hakan, kallonta takai ga agogon d'akin kafin tadawo da kallonta kansa tana zare idon tsorata da mamakin yanda lokaci yatafi, amma takasa magana bare ta tadashi.
Aka kuma kiran wayar, batareda ya bud'e idoba, baikuma saketaba yamik'a hannunsa d'aya ya d'auka, kad'an ya kalli screen d'in wayar kafin yad'aga yasa a kunne yana fad'in "Assalamu alaika".
Daga can Alhaji Sabi'u yace, " Alahji Muhammad lafiya naji muryarka haka?".
Murmushi Uncle yayi sannan yace, "a barci ka tadani".
" barcifa kace? wasa ko gaske?".
"Da gaske" yay maganar yana kuma k'ank'ame Amatallah kamar za'a kwaceta
"Lallaikam, kaiko wane aiki ya hanaka barcin dare? Saikace dakai ake abincin sunan".
'Yar dariya Uncle yayi, kafin yace, " mutumina bazaka ganeba ne kawai, yanzudai miya faru?".
"Uhhm nakirake dama naji kokana kasuwa, amma badamuwa, idan kafito kakirani inason mu had'une".
"OK, saina fitod'in".
"An rad'a suna ko? Gashi ko 'Yar walima bamu had'aba".
"hhh Alhajina kainane yad'au zafi, shiyyasama ko maganar walimar banyiba, mata kawai suyi nasu, mu munyi namu da asuba ai, baby taci sunan Aminatu".
" Masha ALLAH, ALLAH ya raya manasu akan sunna, ya albarkaci rayuwarsu, yasa masu mana addu'ane bayan k'asa ta rufe idonmu".
"Amin ya rabbi. Insha ALLAH zuwa 12 zan sameka a office kawai".
"okay babu damuwa saina ganka".
Kallonta yayi bayan ya kashe wayar, ta lumshe idanunta dan bataso su had'a ido.
Murmushi yayi yashiga zagaya yatsansa kan la66anta, murya k'asa-k'asa yace " 'yammatana da guduwa zakiyi ki barni kenan?".
Wayyo ALLAH, tafad'a a zuciyarta.
Jin bata amsa mishiba ya yunk'ura yatashi da ita a jikinsa, "shikenan tunda bazakiyi maganaba, tashi muje namiki wanka kar 'yan suna sufara jajenki".
Babu shiri ta ware manyan idanunta kansa.
Ido d'aya ya kashe mata
, tai azamar janyewa.
Sauka yayi itama yakamo hannunta zai saukar da ita ta tirje tana langa6e kai, " please Uncle zanyi da kaina Dan ALLAH".
"ban yardabafa my best, dolene nakuma gasaki karkije kina tafiya agane yau......"
Hannu tasa ta rufe masa baki tana cewa "kai Uncle".
Hannun ya janye yana dariya, " to naji bazan fad'aba, muje Na had'a miki ruwan kawai".
Batak'iba wannan tabishi, yahad'a mata dad'an zafi yace "ki daure karki cuci kanki, kisan yau taron jama'ane agidan kinji".
Ta d'aga masa kai idonta a k'asa.
Kumatunta ya sumbata yafice.
Bakuwa ta cuci kan nataba tagasa ko ina yanda yakamata, dan bawani zafi sosai takejiba dai mai cutarwa, tundama Uncle yamata gashi Na musamman da daddaren, amma tanajin jikinta ko'ina yana ciwo, gakuma wani canji Na musamman dukdai ba yanda tasaba jiba.
Tadad'e tsaye tana kunyar fitowa da guntun towel d'insa dake bathroom d'in, amma babu yanda zatayi ganin time nakuma tafiya a banza tafito a takure.
Babu kowama a d'akin, hakanne yasata sakin ajiyar zuciya, kayanta tagani a saman gado, tayi mamaki sosai, amma haka ta d'auka a gaggauce ta shafa mai da body spry, sannan tashirya tsaf, sosai kayan suka mata d'as ajiki.
Bawata kwalliya tatsaya yiba, tana cikin shafa fauda yashigo da sallama, da alama shima wankan yayo a d'ayan d'akin dake 6angarensa inda Nazeefa ta zauna sanda yana Dubai.
" hummm my Heartbeat Ashe nasan kala nima, kinyi k'yau kamar Na zauna naita kallonki abuna".
Murmushi tayi tace "ngd Uncle".
Shima murmushin yayi yahau shirinsa, ko sau d'aya Amatallah bata kalli inda yakeba.
" my best zoki za6amin kaya ko".
Tad'an kallesa kafin tace "Uncle nikuma?".
Gira ya d'aga mata kawai.
Mik'ewa tayi tanufeshi, danta tuna (maganar Anty furera). Yana tsaye gaban Waldrop d'in, hakanne yasa yad'an matsa tashigo gaba, kallon kayan ta tsayayi, tsarin komai ya birgeta.
Jitai ya sak'alo hannunsa kan cikinta ya rungumeta tareda d'ora kansa akan kafad'arta, itako yazatayi da wannan lamari Na Uncle....
Maganarsa ta katse mata zancen zucin datakeyi.
" kifa za6amin kalar naki ehe".
Murmushi tayi ta jawo wata sky blue d'in shadda d'anya, tad'an juyo ta kalleshi da nuna masa kayan. Wuyanta ya sumbata yana fad'in ke tadabance my best! kamar yanda komanki yake nadaban".
Taji fad'in kalaminsa sosai, Dan haka ta danne kunya ta taimaka masa ya shirya, cikin janfa da wando Na kayan, rigar tawuce gwiwarsa da kad'an, amma sunmasa k'yau ainun, saikace wani d'an 30+ (
...lol).
Tana saka masa ma6allin gaban rigar suna murmushi, tagama tafesa masa turarensa.
Yace "saura hula my best".
Murmushi tayi ta za6o masa derk blue acikin hulinan data gani birjit. A mamakinsa saiyaga tana karin hular..... (Abinda nakasa iyawa
Ama... Zanzo ki koyamin narigama boss d'ina nima
) tsayawa yayi kallonta cikeda birgewa. Bayan tagama tamatso kusadashi, yafita tsawo, danhaka yad'an duk'o ta saka masa, tareda dai-daitata da k'yau.
Kallon kansa yayi a madubi yana murmushi, " my best ina kika iya Karin hula haka?".
"Uncle wajen baba mana, tun ina masa yanacewa baiyiba harna dage Na iya kala-kala".
"Masha ALLAH my best!" Yafad'a yana kuma kallonsu a madubin, tabbas yasha ganin karin hularnan akan brother d'insa, ringumeta yayi yashiga bata masu zafi....(
kundai gane).
Saida tasha dad'ad'an kalamai sannan suka fito falo, dakansa yabata brekfast d'in dasuka gani a falon.
Bayan sun kammala kuwa babu yanda baiyiba su fita tare tak'i, yamata kisses yafice tana masa addu'a.
Chapter 48 · 0% Book details