← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 66

Sashe 16

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shekaru uku dasuka wuce ciyo yasamu baba, kad'an-kad'an abin ya fara masa, tun suna magani a tsaitsaye harya kwanta rijuf, sosai Alhaji Muhammad ke tsaye akan ciwon baba, sunje asibitoci da dama Nigeria amma lamarin sai dai addu'a kawai, ciwon koya tafi saiya dawo, saboda yahad'a da girma, ciwon baba dakuma harkar kasuwancinsa daya bunk'asa, ga aiki yahanashi ziyarar jos, sai dai koyaushe Baban Ama Na hanyar duba jikin baba, wani lokacin suzo da Ammi wani lokacin shi kad'ai, Amatallah kam bata biyosu, tun wani zuwa datayi ita kad'ai Hutu su Aneesa sukayi fad'a a kanta itada Fateema tace bata sake zuwa. Koyaya su Ammi sukayi da ita saitak'i biyosu, in zasuzo saitayi tafiyarta gidan ka kanninta iyayen Ammi, Dan zuwa lokacin tafara zama budurwa, tana secondary kusan js 2, duk da yakamata acema taje SS, amma yawan rikin da jihar jos ke fuskanta yasaka karatun yana samun koma baya a jihar sosai. Kullum zancen Uncle M.A ina best daughter d'insa? yakamata tazo masa Hutu. Amma k'iri-k'iri Amatallah tak'i. Hak'ura yayi yabarta saboda shima ciwon Baban da dawowar nauyin gidansu gana iyali ya gama d'auke hankalinsa, ga kuma aiki dayakeyi duk da ba kullum yake a office ba dai. Kwatsam sai Baban Ama yasamu wani mai Maganin gargajiya, ya d'aukeshi sukaje har Kano domin duba baba, Alhmdllh kuma aka dace, Dan baba nasamun sauk'i sosai da wannan Magani, bayan yak'arene Uncle M.A yazo jos kuma kar6awa baba wannan Magani. Anan yaga yanda Amatallah ta girma, duk saiya rikice da mamaki da al'ajabi, Dan yanzu tana shekara 19, SS 3 kuma a Secondary, sune zasu zana SSCE a wannan shekarar. ya d'aukko hotunanta dan nunama matansa suga yanda ta koma, amma sai kishi ya rufe musu ido, suka fara tunanin ko sonta yakeyi, saboda motsi kad'an yace, "my best daughter". Shikuma kawai mamakin yanda tayi girmane ya tsaya masa a zuciya bawani abuba. amma matansa sun hau sun zauna sonta yakeyi. To kuma ga yanda al'amarin ubangiji ya kasance, Ashe ALLAH ya k'addarata acikin matansa Na aure Wannan shine asalin labarin wad'annan brothers guda biyu. Hummmm koya zata kaya kuma idan matan Uncle M.A sukaji a gaske Amatallah tazama matar mijinsu, kishiyarsu, tabbas a kwai cakwakiya. Ku dai Ku kasance dani bilynku kawai. *_WASA FARIN GIRKI!! My fans_* Mukoma labari _____________________________ Hankalin Uncle M.A yatashi, yanda yaga rikicin ya fad'ad'a har zuwa wasu jihohin, bak'amin ta6a zuciyarsa lamarin yay ba, musamman daya tuna babu brother d'insa yanzu a doron k'asa, dama a wajensane yasamu kwarin gwiwwar kafa k'ungiyar dazata farkar da matasan, a yanzun kam baisan ta Yaya zai tunkari lamarinba, sai dai insha ALLAH zaiyi k'ok'ari wajen hana kansa rashin k'warin gwiwwar aikin alkairin daya kulla niyya, shawarar da amininsa brother d'insa yabashi itace zata zam jagora wajen k'aiminsa da wanzuwar himmarsa........ Ringing d'in wayarsane yasashi sakin ajiyar zuciya, hannunsa yasa yafara lalubenta a gefensa, Dan kwance yake a kan gado, tunda yadawo sallar asubahi yakuma d'an kwanciya, saboda tunani baya barinsa samun isashen barci, tunanin jikin baba da rashin d'an uwansa, ga kuma Amatallah da aurenta, Dan har zuwa yanzu bata farfad'oba, iyalansa kuma basusan da aurenba. Ganin sunan doctor Shu'aibu yasashi d'aga wayar da hanzari, ko gaisawa basuyiba doctor Shu'aibu ya shaida masa Amatallah ta farfad'o, kuma Alhamdllh cikin hayyacinta, sai dai tanata kuka da kiran iyayenta. Da hanzari ya diro daga kan gadon, jallabiyarsa daya dawo masallaci ya d'auka ya Sanya, ya d'au key d'in mota yafita da sauri. A falon k'asa yaci karo da Fateema dake k'ok'arin had'a break fast saboda yara zasuje makaranta. "A'a lafiya kuwa Nurri? Saurin mikakeyi haka?". Bai ko juyo ya kalletaba yace, " zanje asibiti ne, Amatallah ta farfad'o". Duk da tana matuk'ar tausayin yarinyar, amma sai da zuciyarta ta sosu, taraka bayansa da kallo harya fice daga falon, wani takaici yadaki zuciyarta akan mazarin da mijin nasu keyi. (Wata zuciyarta tace, aiko baikamata kiji haushinsaba, Dan babu Wanda ya cancanci damuwa da lamarin yarinyarnan sama dashi, kiduba halin data shiga mana). A sanyaye Fateema tace, "hakane kuma, ALLAH kabani hak'urin jure duk abinda zan gani". Nace, " to amin uwargida". ******** Uncle M.A a rikice ya isa asibitin, tun a k'ofar d'aki yay karo da gwaggo Rakiya tana kuka, bai ce komai ba yashiga d'akin da Amatallah take. Doctor Shu'aibu Na tsaye kanta, sai Nazeefa dake zaune gefen gadon rungume da ita, kuka takeyi rurus da fad'in a kaita taga babanta da Amminta. A hankali Uncle M.A ya sauke ajiyar zuciya, ya k'araso gaban gadon idonsa akan Amatallah. d'ayan gefen gadon yaje ya tsaya, ya kalli doctor Shu'aibu a raunane. Jin jina masa kai doctor Shu'aibu yayi, tareda masa nuni ya lallasheta da idanu. Uncle M.A ya jinjina kansa, sannan yay k'ok'arin maida kwallar idonsa yana cije le6ensa Na k'asa. Alama yayma Nazeefa ta barta ta fita itama, saboda doctor Shu'aibu shima yafitan. Nazeefa ta zare jikinta daga Na Amatallah, ta sakko daga gadon. Hakanne yasaka Amatallah d'ago jajayen idanunta, tana ganin Uncle M.A tak'ara k'arfin kukanta tana fad'in "Uncle ka kaini naga babana da Ammina Dan ALLAH". Bai ce komai ba har Nazeefa tafita. Sannan ya zauna a bakin gadon kusada ita, hannu yasa ya jawota kusadashi ya rungumeta kawai, tuni idonsa suncika da kwallah, harsun fara taruwa a gefen idonsa. Rud'anin da Amatallah take cikine yahanata mamakin rungumar da uncle yaymata, Dan tunda tafara girma da wayo ya daina rik'e koda hannuntama. jinta a jikinsa yasakata kuma fashewa dawani kukan mai tsuma rai. d'an yatsa d'aya Uncle yasaka ya d'auke hawayen dasuka taru masa a gefen ido, ya k'ara rungume Amatallah sosai ajikinsa, cikin daidaita muryarsa yace, " Khadija! ". Yanda yakira sunantane yasakata tsaigaitawa da kukan, amma bata amsaba. Ya kuma fad'in " Khadija! Kina jina?". Cikin da shashshiyar muryarta ta amsa da "Na'am uncle".............. Inaga maybe gobe idan ALLAH ya kaimu bazaku ganniba gaskiya Idan kuma naga comments yanzu idan nadawo anguwa nayi muku One Luv my fans *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [1/16, 1:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing *_HASKE WRITER'S ASSO..._* _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce ____________________ *_Number 12_* ____________________ Shiru yad'anyi Na wani lokaci, kafin yagyara mata kwanciya a jikinsa, murmushi yayi mai ciwo sannan yace, "Khadija duk duniya wayafi kowa a halittun ALLAH?". 'Dan d'agowa tayi ta kalleshi kad'an, sai kuma ta maida kanta a gefen hannunsa, muryarta a dusashe tace, " MAZON ALLAH (S.A.W) Uncle ". Lumshe idanunsa yayi yana fad'in " masha ALLAH Khadija, yanzu yana ina?". Yanzun kam tashi tayi sosai tabar jikinsa, jingina tayi dagadon idonsa Na kanta. "Uncle ya koma ga Ubangijin sammai da k'assai". ''Alhmdllh Khadija, yakikeji darashin kasancewarsa a duniya". Mamakin tambayoyin Uncle suka fara bata, amma saita dake tace, " inajin babu dad'i, amma nayi hak'uri tunda ubangijine ya tsara hakan, ina dai Addu'ar ALLAH ya sadamu dashi a ranar ceto". Kansa yakad'a mata, muryarsa takuma sanyi fiyeda sanyin datake dashi, yakamo hannayenta biyu yarik'e a nasa, "Khadija ke musulma ce kuma mumina, kinsan k'addara da jarabawa, duk wani mumini akwai irin jarabtar da ALLAH kanyima rayuwarsa, wani yabashi dukiya mai tarin yawa, amma bashida lafiya, wani talauci amma yanada lafiya da 'ya'ya, wani ilimi amma sai ya jarabceshi da hatsabibiyar mace ko shi d'in ya kasance hatsabibin, ko cikin 'ya'yansa, wani haihuwace ALLAH bai bashiba, wani ya haihu 'ya'yan sun zame masa fitina, wata macen gidan mijine jarabtarta, wata rashin aure, wata rashin lafiya, wasu kuma saikiga ALLAH ya had'a musu komai Na rayuwa, sai dai kinsan wani Abu?". Amatallah ta girgiza masa kanta. Yacigaba da fad'in kowanne irin matsayi ka taka a rayuwarka inhar bakajin tsoron ALLAH ba to kaifa ba komai baneba, duk k'ask'ancin waninka inya kasance mai tsoron ALLAH toya fika agareshi, ubangiji shika d'ai yasan iya adadin halittun daya halitta masu numfashi a duniya, kuma shine ya tabbatar mana duk sai ya d'and'ana mana mutuwa, wad'anda suka rigamu tafiya ba sauri sukayiba, muda muka rage bamuyi jinkiriba. A wannan ga6ar ina mai baki hak'uri, da rok'onki akan kizama cikin bayi masu ambaton Alhamdullahi ala kulli halin aduk yanayin dasuka tsinci Kansu a rayuwa, ki kar6i jabawarki da hannu biyu dankizama cikin salihan bayi muminai..........." Hawayene masu zafi suka fara zarya a kumatun Amatallah, tabbas bayanan uncle namata nuni akan babu babanta a duniya, ahankali tace, "uncle babana yarasu ko? Karka 6oyemin, kafad'amin, insha ALLAH zuciyata zata iya d'auka, domin ubangiji baya jarabtar bawa da a binda bazai iyaba. namaka alk'awarin kasancewa cikin bayin ALLAH masu hak'uri da kar6ar jarabawa ko wacce iri". Da k'yar ya iya had'iye wani kulutu daya tokare masa k'irji, sannan ya d'aga mata kai a hankali shima hawaye nabin nasa kumatun. Jikinsa kawai tafad'a tasaki kuka mai tsuma rai, hannu biyu ya kar6eta ya rungume, suka cigaba da rairawa a tare, abin gwanin ban tausayi. Sun d'auki tsawon lokaci ahaka kafin Amatallah cikin kuka tace, " uncle Ammina fa?". "Sai hak'uri Khadija, Saliha tama rigayi brother ra..s....u...wa...". yak'arashe maganar da k'yar, saboda wani d'aci dayakeji a zuciyarsa. Sunyi kuka mai isarsu shida ita, kafin doctor Shu'aibu yazo yana lallashinsu, dole akama Amatallah allurar barci danta samu nutsuwa. *_One week later_* Alhamdllh a sati d'ayannan daya gabata abubuwa masu yawa sun faru, ciki harda rud'ani mai rikitarwa da Amatallah ta shiga, dole aka d'akkota daga asibiti aka maidota gida wajen innani. Basu 6ata lokaciba aka dage mata da addu'oin dangana da hak'uri, Alhmdllhi ansamu nasarori kam, Dan addu'a takobin mumini Ce. Nutsuwa tazo mata sosai, sai dai yawan kuka datakeyi, sannan maganama yanzu kam saita wunima batayiba. Kullum uncle Na hanyar gidansu innani. Nazeefa da Innani suna matuk'ar k'ok'ari wajen rage mata kewa da yawan damuwa, hakama jabeer, Shehu kam sai a hankali, danshi dama bayajin magana, zaman gidamma bayi yakeyiba, danma yana masifar tsoron uncle Muhammad d'inne yake rage wani abun. Har zuwa yanzun daga Amatallah har matansa babu Wanda yasan da zancen aurensu, innani da babane kurum sai jabeer da maijiddah suka Sani, ko Nazeefa batasan komaiba. Bayan sati uku da rasuwarsu Ammi cif baba yace yakamata asanarma Amatallah zancen auren, karya zam saita saki jiki kuma akuma maidata ruwa, gamma taji komai yanzun tahak'ura baki d'aya, hakama matan uncle yakamata Susan halin da'ake ciki. Innani tayi na'am da wannan batu, Dan haka aka kira kawu yakubu
Chapter 16 · 0% Book details