← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 66

Sashe 62

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zazza6i dai yak'i sauka, saidai jikin ya huce yakuma dawo, ba Uncle ba hatta su Aneesa duksun damu, dan tasaba ranar weekend sunta shagalinsu da yaran agida kafin su tafi islamiyya, su Kansu yaran duk sunyi sukuki.
Da daddare dai abinda batason dole akayi, Uncle yakira doctor Shu'aibu yadubata, gudun karya bata Magani suyi 6arna yace tayi gwajin tsinke.
gwajin farko ya nuna mumsami baby
Murna wajen Uncle ba'a magana, babu kunya ya rungumeta a gaban Doctor Shu:aibu, Ama..... kam hawaye kawai takeyi, dukda tad'an dad'e tana zargin cikine dama, soboda aikintane, (dan kunsan doctor Ce fannin mata insha ALLAH anan gaba kad'an zata zama kwararriya
Su Fateema Kansu dai murna sukeyi, kodan k'aunarda Ama....kema 'ya'yansu dolene su tayata farincikin samun NATA itama, kuma ko kad'an basuji kishin farin cikin da mijinsu ke nunawa akan cikinba.
Doctor Shu'aibu yace, "dama nasan itama tasan tanada, kawai dai ta 6oye mukune".
" Uncle ya kalli Ama..... yace, "wai haka my best!?".
Kanta ta 6oye cikin bargo tana murmushi.
Duk sai sukayi dariya, Uncle yaraka Doctor sannan yadawo suka cigaba da farimcikinsu.
Ranar dai dole Aneesa tayi sadaukarwa na kwananta ga Ama....., Uncle yakwana a wajenta saboda jikinta. (Anee kin biyamu kwannamu
Hummm kafin kacemi maganar cikin Ama....Yazagaye dangi makusantansu, har 'yan jos an gwargwad'a musu, murna dai ba'a magana, 'yan dubiya su Anty maijidda dasu Asiya su Nazeefa mai jego, ita Ama... Kunyarsuma takeji, duk kuma d'okin son samun cikin saiya 6uya yanzu da'aka samu d'in.
Babama yayi murna, hakama innani, dukda bata fito ta nuna a filiba, amma takanas shehu yakawota tazo ta duba Ama.....
Amatullah nashan wahalar cikinnan, dan laulayi takeyi sosai, dolene kaganta Tabaka tausayi, dukta rame sai uban haske data k'ara, dukda kasancewarta bak'a.
Girki dai su Fateema sun sauke mata, saidai ta kwana da miji, wataranma idan abin yay tsanani hakura suke da kwanan Nasu ya kwana a d'akinta, tanashan k'arin ruwa kam tamkar wata gallon
, kullun cikin zirara mata akeyi.
To Ama...ALLAH yaraba lafiya.
***********
Kwanci tashi babu wahala wajen Ubangiji, ga Ama.... cikinta yashiga wata na 7, yafito d'as kuma yamata k'yau, tanata karatunta hankali kwance, dan Alhmdllh tunda cikin yashiga wata na 5 tasamu sauk'in laulayin, saidai abinda ba'a rasaba, harma taje jos tayo sati biyu acikin d'an hutun dasuka samu, tazaga dangi sosai dukda ba wannane zuwanta Na farkoba, har anguwarsu taje ta gaida makwafta dasuke mutunci dasu kafin rasuwar su baba, dukda ma wasunsu sun rasa rayukansu a lokacin wancan rikicin, wasu kuma sunbar garin gaba d'aya, har kuka tayi dataga kufan gidansu, Dan tuni Uncle yanemi shawarrata akan ayi masallaci ko islamiyya awajen, domin ladan yadinga kaiwa ga iyayenta, takuwa amince, yasa akayima wajen gyara bayan an rushe, masallaci akayi k'arami da islamiyya mai aji hud'u k'anane amam, sai Bohol da akayi mutanen anguwar NATA d'ibar ruwa, dama basudashi. Wani son Uncle Yakuma ratsa ruhinta saboda wannan hidima dayay ga mahaifanta, (kowa yasan anason sadaka mai gudana ga mamaci). a zuwanne takejin labarin d'aure Ramzaki da akayi, saboda kashe wani da Mr Pam yasa sukayi, kuma aka kamasu, koda sukace shine yasakasu aka kirashi saiyace shibaima ta6a ganinsuba ballantana ya sansu, k'arya suke masa, hakanne yasa aka kaisu Court, hukuncin shekaru 25 aka yanke musu a prison. Amatullah dai jitayima INA itace alk'alin , da ratayesu zata sakama ayi take anna, amma hakanma tayi farinciki koba komai zai d'and'ani azabobi kafin yaje waken ALLAH kuma. Satinta biyu tadawo Kano ta koma school aka cigaba da bugawa.
Rayuwar gidansu nanan yanda take, saidai 'yan canje-canje daba'a rasaba, amma sunan akan tattalin mijinsu da kishinsa, kuma hakan bai hanasu k'yautatama junaba.
Haka shima mijinsu mai gajiya da basu soyayya mai tsaftaba, kowacce gwargwadon iko yana nuna mata tattali da soyayya, yana k'ok'arin adalci a tsakaninsu, wadda yafi so kuma yabarma zuciyarsa.
Maganar K'UNGIYARSU kam saimuce Alhmdllh, yanzu haka suna k'ok'arin had'a wani gagarumin taro na k'asa, domin wayarma matasa dakai a kan za6en dake tunkaro k'asar, Wanda bai wuce saura kwanaki k'alilanba a gudanar dashi.
Sai dai kuma a wannan tsakaninne wani Abu Mara dad'i yafaru
, shine Rasuwar baba, adaren juma'a ranar alhamis kenan jikinsa yay tsanani, hankali tashe Innani takira Uncle kusan 1pm, harma ya kwanta, dan ranar a d'akin Amatallah yake, suna tsaka da barci tana kwance a jikinsa, yayinda hannunsa ke rungume da cikinta, da k'yar ya iya lalubar wayar a k'ark'ashin filo, batareda yaga mai kiranba yad'aga dafad'in "please wanene?".
Muryar data daki kunnensa tasashi wartsakewa babu shiri, innani yajiyo tana fad'in " maza kazo gida Muhammadu jikin babanku ya rikice".
A firgice ya wuntsilo daga gadon, haryana bigema Ama.... cikinta, Wanda zafinne yasata farkawar dole tana fad'in "wayyo ALLAHNA".
ina Uncle bai sauraretaba, sorry kawai yace mata yafice da sauri.
Dukda azabar da Ama... keji haka ta tashi zaune da k'yar, mamaki yacikata, tabbas babu lafiya, dan ko juyi zatayi cikin barci saiya farka, kuma zai taimaka mata ta juya cikin lalla6awa, amma yanzu ji yanda ya maujeta bai kulaba, sakkowa tayi tafito tana d'an cije baki, dan har yanzu inda ya bigeta bai daina zafiba, yaran cikinta sai motsawa yakeyi alamar shima yaji zafin maybe (
lol).
Tana fitowa falon yana fita shikuma a rikice, ya canja kayan barcinsa zuwa farar jallabiya, hakan yakuma rud'ar da Ama... ta tada su Fateema duk ta sanar musu.
Jigum-jigum sukayi, kowa yana sak'e-sak'e da tunanin mike faruwa? dukda wani 6angaren tunaninsu yana kan babane k'ila, saboda jiya jikin nasa yad'an motsa har sukaje suma suka gaidashi.
Kasancewar titi babu motoci sai tsilli-tsilli yabama Uncle damar zabga gudu, lokacin dayaje gidan lamari ya 6aci kam, danba baba ba hattada Innani tafita hayyacinta, Aysha sai kuka takeyi, hakama gwaggo Rakiya.
Dole adaren suka tafi asibiti, sai daifa babu tsumi babu dabara, kafin asubahi rai yayi halinsa
, ALLAH ya d'auke kayansa.
Mutuwar data zamema Uncle ta uku dabazai ta6a mantawa da itaba, duk yanda yaso ya daure ya rarrashi su Innani yakasa, shima kansa yakifa akan gawar yafashe da kuka

hakanne nima yasani kukan, danna tuna da rasuwar nawa mahaifin
, ALLAH ka gafarta musu, ka yafe musu, muda suka bari ALLAH ka d'auki ranmu muna a masu imani da tsonka ya rabbi, ya ALLAH ka k'ara mana soyayyar manzon ka tsaftatacciya a rihinmu
Marayu ALLAH yabamu hak'uri kunji, inayinku a duk inda kuke.
To anyita ta k'are, baba yatafi ya barsu Uncle, yanzu shine babban wa, shine kuma Uba.
Washe gari misalin 10am akayi jana'izarsa wadda ta tara d'unbin Al'umma, kodan d'ansa yatara, dan matasa dama dattijan sunta tururuwar halattar wannan jana'iza domin nuna hallaci ga Alhaji Muhammad Ahmad Labbo.
A kwana Ukun data gabata ba'a cewa komai, dolene kaga Uncle dasu Ya Jabeer subaka tausayi, barema su Nazeefa da Shehu da Anty maijidda, hakama su Amatullah duksun jigatu, amma Yaya za'ayi da ikon rabbi, saidai hak'uri.
ALLAH sarki Innani, mace mai hak'uri da k'ok'ari, tasha jiyya harta tsawon shekaru kusan 7, ALLAH yabata ladan jiyyar datayi ta adalin mijinta dattijon kirki mai yakana da dattako.
******* ******* *******
Tun bayan rasuwar baba abubuwa sukaima Uncle cak, Yakoma sai a hankali, kasuwama yadaina waiwayarta, wajen aiki kam danya zame masa tilasne, sauk'in sama ba kullum baneba, K'UNGIYA kanta tasan jagoranta yazama abin tausayi, dole sai Alhaji Sabi'u ne yacigaba da tafiyarda shugabancin kafin komai ya daidaita.
Su Kansu matsansa saidai Addu'a suke binsa dashi, amma komai nasa yayi sanyi.
Ahaka dai yauda gobe har zuciya tafara sanyi da hak'un dangana, yafara komawa kan harkokinsa dakuma jan 'yan k'annensa a jiki, yakuma ninka kulawarsa ga mahaifiyarsu Innani, wadda ayanzu itace Uwa Uba kuma, itama kanta dukta fita hayyacinta, ga girma na tsufa.
Chapter 62 · 0% Book details