← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 66

Sashe 42

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kusan 12 Lecturer d'insu na English bai shigoba, dukma sun fidda rai da zuwansa, wasuma suna k'ok'arin barin hall d'in sai suka hango wani malami na tahowa. Gabatowarsa ta saka wani d'alibi fad'in "kuttt wlhy kowa ya nutsu boss ne da kansa zai mana lecture yau......"
Bai gama rufe bakiba Uncle yashigo, mamaki sosai Yakama Amatallah, dama Uncle yanada alak'a da school d'innan har haka? Tasan dai kamar yana aiki anan, amma bata d'auka yana Lectures ba. Mamakinsa yakuma kamata, yayi masifar tsare gida alamun babu wasa kenan, ta tuna Uncle mai yawan fara'a ashe haka yake a waje. Sai dai yanda 'yan class d'in suka nutsu abin yaso bata dariya, musamman idan tayi dubi da yanda aka raina wasu lecturers d'in, bakamar wasu group na samari da 'yammata da ake kira *Gayun zamani* kallonta takai mazauninsu tagansu a nutse kamar basuba.
Kallonta ta maida ga Uncle d'in dake magana cikin nutsuwa dakuma kwararren Turanci. Yana bayanine akan zai d'aukesu lecture d'in saboda lecturer mai d'aukarsu yasamu Accident a daren jiya.
Nan suka shiga mishi addu'a.
Tunda yashigo yaga Amatallah, amma yashare tamkarma baisan da ita a hall d'in ba, saidai tuni Fa'iza dasu Rita suka ga kallon dayake satarta dashi, hakanne yasasu shan jinin jikinsu kodai shine Uncle? dukda Amatallah bata sanar dasu Uncle na aiki ananba.
Harya gama lecture d'in yafita sannan suka samu damar tanbayarta, dariya kawai tayi batace komaiba, yayinda Rabin hankalinta ke kan 'yan class d'in dake gulmar Uncle, wani d'alibi harda mik'ewa yaje inda lecturers kan tsaya idan zasuyi lecture ya kwaikwayi salon Uncle d'in, nanfa aka kwashe da dariya, d'alibin yace, "please guys bai burge kuba?".
Nanma suka amsa da sosaima ana dariya, wata ma a 'yan matan ta mik'e tana fad'in " aini babu abinda yafi d'aukar hankalina gareshi sai salon maganarsa ma
i sanyi da takunsa, kai jama'a malamin nan yayi over, inama zan dace da na tsinci tsuntsu daga sama".
Nanma dariyar aka Sanya da sakin ihu.
Ta kuma kwaikwayon muryarsa yanda yafad'i sunansa, my Name is Muhammad Ahmad labbo, nine zan cigaba da jagirantarku kafin mai d'aukarku yasamu sauk'i.......
Salon nata yasakasu kwashewa da dariyar ihu suna kiran saikinyi zee-zee.
Ta shafi inda ya d'ora hannunsa ta sumbaci hannunta da fad'in "I love you so much Muhammad mai babban suna".
Nanma dai bata sake zaninba ihu sukayi.
Dukda wannan Abu dake faruwa Amatallah tayi kicin-kicin da fuska ko sau d'aya batayi dariyaba tunda budurwarnan tafara kwaikwayon Uncle.......
Maganar zee takuma katse mata tunaninta, " kai my guys, ammafa bawan ALLAH nan akwai tsare gida, ya matarsa keyi?".
Wani yay caraf yace "zee-zee dakin Shiga daga ciki zaki canja manashi".
Dariya ta tuntsure dashi, sannan ta rungume hannunta ak'irji tana lumshe ido, " wayyo! ALLAH Da nikam nasamu duniya, saidai kumin addu'ar samun lahira kuma, wlhy da gaske yasace zuciyata sonsa nak.........
Amatallah bataji k'arshen zancenba tatashi tafice saboda wani masifar tsanar zee daya turnik'eta, harma da sauran 'yan ajin dake tayata da ihu.
Rita dasu Fa'iza suka take mata baya da sauri suna kiran sunanta.
Baki zee ta ta6e tana rakasu da harara, kafin ta kalli 'yan ajin tace "tofa kunga wani Sabon salo, ko wata ke sonsa a cikinsu? Tab wlhy Ashe da anyi yak'i a bayaro".
Sosai yanzu ihunsu yafi na d'azun, wasu dasuma abinda zee take bai birgesuba suka fara ficewa, wasu kam suma abinda kedamun zee shike damunsu wato son Uncle d'in (basusan tsoho bane......lol
Da k'yar su Fa'iza suka lallashi Amatallah dake kuka, goodness tace, "ai hankali aka kiya miki, saiki tashi dan kamo mijinki, wazai kallesa yace matansa Uku bare yayi tunanin yakai shekarun dakika fad'a mana, wlhy sisi kardai kiyi sake.....
Sosai suka mata fad'a, bakamarma Fa'iza dakejin tamkar ta mangareta.
Koda aka tashi lecture d'in k'arshe wajen 2:30 bata nemesaba, dukda kuma yace idan tagama ta kirashi, tafiyarta tayi bayan tasha gargad'i wajen Fa'iza akan kartaje tamasa shirme tunda bashine yace zee tasoshiba, kuma tabata shawara akan abin sharruwa daya kamata ta had'a masa.
Tadai tafi tana zun6ure-zum6ure. (Ama...kishi lol

_________
Uncle kam baisan wainar da'ake toyawabama shi, saidai idan yatuno yanda Amatallah ke satar kallonsa a aji yakanyi murmushi.
Yasamu ganawa da dukkan lecturers d'in, Yakuma kawo musu kudirinsa na kafa k'ungiyar matasa dakuma zawarcin abokan tafiya.
Wasu sun bada had'inkai, wasukam sunata 'yan kame-kame saboda sunji maganar hardata kud'i, duk Uncle ya lura dasu.
Ya tausasa harsher yana fad'in " karfa hakan ya dameku, bawai tilasne saika zuba kud'inkaba, inhar zuciyarka atsarkake take da nufin son a gyara tafiyar matasan zaka iya bada gudun mawarka, Dama munsaka maganar kud'inne saboda tallafama Matasan dabasu sami koda karatun secondary d'inba, sai Mike ganin Sana'a yafi dacewa su a tallafesu da ita, saikuma wad'anda karatun Nasu ya tsaya iya secondary d'in, sunada buk'ar mu taimakesu domin cigaban karatunsu, saboda wasu sun cancanta amma rashin tallafi yasakasu maida takardunsu kasan jakka sukoma maula ko dabar siyasa ko shaye-shaye, akwai kuma Matasan dasun kammala karatun amma babu aikinyi, bazai yuwu kowanne saiyazama ma'aikacin Gwamnati ba, Dan bazata iya d'aukar kowa aikiba, to kunga saimu tallafa musu da sana'oin hannu dazai rik'e rayuwarsu kodan rage musu rad'ad'i wajen tunzuruwarsu ga aikata ta'addanci, mukuma cire musu ak'idar nayi karatu dolene Nina naga kaina a office. Wad'annan hanyoyin zasu rage ma matasanmu yawan Shiga TARKUNAN 'yan siyasarmu masu gur6ata tunaninsu da kud'i harsuna haddasa mana rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI*, kudancinmu sunrigada sunyi nisa a irin wannan taimakon, zakiga mutum d'aya ya d'auki nauyin yara goma karatu, koma fiye dahaka, babu kuma abinda suka had'a, kawai k'auyensu d'ayane. Amma mufa 'yan arewa duk iri-iren wad'annan abubuwan bamayi, kullum burinmu mu Gina k'aton gida, musa tsala-tsalan mata da ma'aikata masu yimusu hidima, saika samu harabar gidan mutum d'aya da mota goma, har yaran gidan k'anana sunada motarsu da ake kaisu yawo, amma gawasu suna cikin wahalar rayuwa bama tausayinsu, idan munga idonsu ko kud'insu sai sun tsaya takarar kansila ko ciyaman ko d'an majalisa ko gwamnan jaha, to sannanne zasuna mana 6arin kud'i kamar basusan ciwonsuba, a wayonsu idan sun hau kujerar mulki sunsan zasu maida fiye da abinda suka watsa mana".
"Mun manta damaganar alk'awuran aiki dasukai masa, wannan tunanin namune ya Karya arewacinmu, akowane lamari mune koma baya, yanzu damuna taimakon matasanmu wasu azzalumai sun isa su sami damar haddasa mana tantin ta'addaci a yankinmu? Bakwajin ciwon yanda ake kashe mana matasa ana kama wasu acikinsu ana jinginasu da ta'addancin? Idan kana ganin babu d'anka aciki ko k'aninka, baka tunanin ta6ar6arewar komai har 'ya'yan naka su taso suma sugaza amfana da komai na k'asarsu? Shin bakwa tunanin ba ayanzun matsalar takeba sai zuwa nangaba mun rasa jagororin tallafin arewacinmu, sufa matasannan damuke zuba ido wajen kallon lalacewarsu koma jagorancin lalacewar tasu watarana sune zasu zamto rik'e da k'asar. Shin mikuke tunani akansu idan k'asar tazama a hannunsu? Kuna ganin 'ya'yanmu k'anana zasu shane? Kokuwa yankinmu damu kanmu zamusha? Kufayi tunani akan wannan lamarin, dan duk d'inmu iyayene, kuma yayyane, musan zafin damukeji yayinda mukaga d'aya acikin zuri'armu kangararre, shin bakwa tunanin ya sauran iyaye sukeji suma?. Akiraka mai kud'ine abin birgewa kokuwa ALLAH ya aminta da k'yawawan aiyukanka? Wannene za6inku?!!!".
Chapter 42 · 0% Book details