← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 66

Sashe 22

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Fitowar Shehu daga d'akinsa yana mik'a da hamma, babu zancen rufe baki a tsarinsa, dagashi sai gajeren wando da vest.
kallonsa sukayi suduka.
Uncle M.A ya had'e fuska yana kallonsa, cikin daka tsawa wadda bata hana muryarsa fita da sanyiba yace, "kai! Shehu!, wane irin iskancine wannan? zaka fitoma mutane tsakar gida da boxer? kamar kai kad'aine a gidan?".
Shehu ya yad'an Sosa k'eyarsa yana duk'ar da kansa, " kayi hak'uri Yaya, ni bansan kana gidanba ai".
"Lallai kam, wato sai ina gidanne zakayi shigar mutunci? Nazeefa da Amatallah ba k'annenka baneba? kai bakajin kunyar su ganka a haka? to ni abindama nakeson na sani, sai yanzu katashine kokuwa?".
Nazeefa tayi saurin " fad'in ALLAH Yaya sai yanzunne yatashi, da asuba babu irin bugun da ya Jabeer bai masaba amma yak'i bud'ewa, hakama innani".
Harararta Shehu yayi, amma baice komaiba.
Cikin matuk'ar 6acin rai Uncle M.A yace, "wai Shehu mikakeso kazamane kaikuwa? Wannan wace irin rayuwace kaza6ama kanka? gwargwadon iko kowa k'ok'ari yake dakai agidannan kan kazama mutumin kirki, amma gakanan tamkar wanda bakin iyaye ke d'auniya dashi? yanzufa ka kalli agogo kusan 7:30 amma bakayi sallar asubahiba, amatsayinka na matashi mai lafiya, ko baba dake kwance yana jiyya kullum saiyabi jam'i a gida, kaje kayi tayi wlhy, rayuwarkace, idan ka gyara kaine zaka anfana, idan kabari ta lalace asararkace, shekarar k'arshe kake a makaranta amma yanzu haka yau kunada exam, kana kwance kana barci k'ilama ko karatu bakayiba?".
" Yaya nafayi, dad'ewama danayi ina karatunne yajamin makara.....
"Rufema mutane baki kafin na sa6a maka kammanni wlhy, ina k'ofar gidan su Rabi'u kazo ka wuce kaida abokanka kunata warin sigari, nasan baka ganniba ai, kuma koda na dawo gida kwance na iskeka kana barci zakace wani karatu kayi. walhy Yaya idan yaronan bai tsallakeba wannan karon karka kuma 6ata kud'inka akansa, banza kawai Mara amfani wa kansa bare waninsa".
Jabeer ne mai maganar cikin k'unar rai da bak'incikin halin d'an uwan nasu daya biyema abokan banza suna shashanci.
"Abinda dama na yanke kenan Jabeer, ka duba shekarun da yaronnan ya d'auka a makaranta, tunfa Nazeefa na ss2 a secondary, gashi harzata kammala degree d'inta tareda dashi, k'ilama takuma barinsa....
''Dan ALLAH Yaya karkace haka, insha ALLAHU zan dage nabar jami'a wannan year d'in, kodan naga kunyi farinciki, kuyi hak'uri Dan ALLAH, kucigaba damin addu'a".
ALLAH sarki, d'an uwa rabin jiki, sai kuma tausayinsa ya kamasu, a raunane Nazeefa tace,
" please ya Shehu ka canja mana, kodan k'ok'ari da Yaya Muhammad keyi a kanmu kullum shida ya Jabeer, ga halin da baba yake ciki, ALLAH abinda kakeyin nan yana k'ara saka damuwa a ciwon baba, kai abin baya damunka ne?".
''Ya za ayi ya damesa Nazeefa? tunda duniya da abokan banza na kaimasa yanda yake buk'ata, ALLAH ya shiryeka Shehu, kawuce kaje kai Salla rana na kumayi, ni bara na wuce kasuwa".
"Yaya nagama karin kumallo fa, kazauna kaci dan naga yanda kafito da safen nan dawuya idan kayi a gida".
"No auta, karki damu, ina saurine yau kayanmu suka iso, gashi zanje office yau, inada meeting da lecturers".
Bai jira cewartaba yabama Jabeer hannu sukayi musabaha ya fice.
Dariya Jabeer yayi yace, " auta kema kinsan Yaya da abinci aii, nidai bani nawa na d'ora natai aiki".
Itama dariyar tayi kawai tanufi ketchin.
Abincin kowa ta zuba takaikai musu, sannan ta d'auki nasu itada Amatallah.
Chapter 22 · 0% Book details