← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 66

Sashe 58

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Dangin Aneesa sunji dad'in ganinta, dan haka aka musu tarba ta musamman itada boss d'inta, sai haba-haba akeyi dasu.
Kwannan Uncle biyu kuwa ya dawo bayan ya zagaya dangin Aneesa yamusu alkairi dai-dai k'arfinsa, yabarota itada Saifudden da Saheb da Siddiqa, yasha dai shagwa6a randa zai taho wajen Nessar sa, haryaji tamkar karya taho ya barta.
Hakadai yataho cikeda kewarsu. yakumazo ya iske wata tarbar ga Amatallah wadda ta mantar dashi kewar Aneesa.
Rayuwa tacigaba da shurawa, da gari ya waye sai dare yayi, saikuma wata safiyar.
Ansaka ranar auren Jabeer da Asiya k'awar Amatallah, ashe dama tun a wajen bikinta suka jone, Amatallah tayi murna sosai, koba komai tasamu 'Yar uwa akusa, Nazeefa ma an saka tata ranar da saurayinta Mubarak, sai shehu da zaliha k'anwar Fateema, wata 5 kacal indan munkai da rai.
Governor yabasu damar ganinsa ranar Monday 11am, dan haka suka tsara masu zuwan su 5 kawai. Uncle, Alhaji Sabi'u, Alhaji murtala, Alhaji Maina saikuma shi Alhaji Isa d'in.
*********
Sun sami tarba mai k'yau daga governor dan yanajin dukkan ayyukansu na alkairi, kuma duk d'insu yana musu kallon mutane masu mutunci da sanin mutuncin jama'arsu, sunci abinci a tare kafin sushiga abinda ya kawosu.
Governor yayi murmushi tareda jinjina musu "tabbas kun burgeni sosai, kuma ina marhabin da wannan k'udiri naku, nakumayi alk'awari taimaka muku nima nasaka hannu a tafiyar domin cigabanmu muda yankinmu, wannan taimakon bata fuskar SIYASA zanyishiba, zan yishine amatsayina nad'an k'ungiyar, kuma atake anan nima za'a bani form nacike dan zama a member na k'ungiya".
Atare sukayi na'am da nuna farincikinsu.
Yacigaba da fad'in " ga shawara, mubar maganar kar6ama k'ungiya kwangila domin neman kud'in shiga, dan hakan zaibama wasu damar yad'a farfaganda na nuna k'ungiyar SIYASA ce, bayan kuma naji mafi yawan bayananku na nuna kuba 'yan SIYASA bane, bance kud'in dazan bada zasu rik'e k'ungiyarba, amma zasu taimaka sosai wajen tallafa k'ungiyar takafa wasu sana'oin dazasu ringa kawo kud'ad'en shiga, sannan nayi alk'awarin saka matasan wannan k'ungiya a guraben aiki masu yawan gaske, dakuma guraben karatu awasu jami'oin arewaci da kudanci, wad'anda basuda buk'atar karatun kuma zamu tallafa musu da jari a gwamnatance, ina fata kun gamsu da hakan".
Duk mun amince mai girma gwamna, fatanmu ALLAH yashige mana gaba, yakuma cigaba da dafa maka acikin ayyukanka na alkairi, ALLAH yayta kawo mana shuwagabanni irinku masu zuciyar zinari a k'asarnan".
Dariya governor yayi, "Alhaji Muhammad Ahmad Labbo kune yakama ayi addu'ar yawaitarku acikin al'umma, dankune zinarai masu zuciyar diamond, da yankinmu sunada irinku tuntuni daba a sami damar kassaramu irin hakaba, ALLAH yak'ara muku tsawon rai da lafiya".
Duk suka amsa da amin, Uncle dai 'Yar dariya kawai yayi, azuciyarsa yace amin d'in.
Kafin subaro suka bama governor form yacike, shima saida yabiya naira dubu d'aya kamar kowa, sannan yarubuta musu zunzurutun kud'in na gudunmawarsa, suka rabu akan yana jiran takardun matasa d'ari biyar, dan nema m
usu aiki, damasu neman gurbin karatu, saikuma masu sana'oin hannu.
Sunyi godiya sosai da k'yak'kyawar addu'a agareshi, suka baro gidan cikin d'unbin farinciki da yabama halin dattako irin na wannan governor.
******
Watan Aneesa guda tadawo Nigeria, cikeda abubuwan tarin alkairi daga family nata, tsaraba kowa da sunansa.
Daga Fateema har Amatallah sunyi kewarta, dan haka ranar dawowarta sukai mata tarba ta musamman, itama tayi kewar tasu, abin sha'awa suka rungume juna cikin nuna d'okantuwarsu.
Mai gayya mai aiki kam aibama a maganar irin kewar Aneesar dayayi, ranar kam su Ama... Sai suka zama 'yan kallo dan Aneesa a sabuwar amaryarta tazo.
Rayuwa tacigaba da shurawa, su Uncle matsalolin sun ragu musu, dan yanzu sunada kud'in a hannu, ga governor yacika alk'awarinsa na tallafawa matasan da guraben aiki dana karatu, sai k'ananun sana'oi na hannu, wad'anda kuma sukeda sana'oinsu aka kuma musu wani tsari na taimakonsu, kafin kace mi ayyukan wannan k'ungiya sun ratsa birni da k'auye, harsun shiga wasu jihohin arewacin k'asarnan, inda su Uncle suka wakilta amintattunsu dake a jihohin.
Abin kunya abin bak'in ciki sai wasu many an k'asar 'yan SIYASA da wasu yankuna na K'ABILUN kudanci suka fara sukar wannan KUNGIYA, da kiranta 'yan rajin raba kan matasan K'ASA, hakan baita6a damun su Uncle ba, dan ayyukan nasu sunfara fad'ad'a zuwa wasu yankunan na KUDANCI, dukda basu samun goyon baya sosai agaresuba, sukan nuna K'ABILANCINSU akan manufofin k'ungiyar kai tsaye.
Saidai kuma abinda zai birgeka matasan dake cikin halin hau na rayuwa sai suka dunga danno kai abinsu, suka ajiye maganar wata SIYASA ko K'ABILANCI agefe guda, Kan kacemi suma 'yan kudancin sun fara k'arfi acikin k'ungiyar.
Hakan bak'aramin tada hankali wasu 'yan SIYASA yayiba, dan yanzu matasan dasuke sakawa a BANGAR SIYASA da basu kwayoyin maye da makamai sunfara gagararsu, ganin matasanma yafara musu wahala, ba'a cika k'ofar gidansu neman MAULA, bare su sami damar hura hanci da watsa ma 'yan tsaki tsaba.
Idan sun taro matasan nan sukuma saisuyi can, sunce yanzu sun daina dafama k'artin banza baya, su turasu sai mota tatashi ko d'ani a gagara basu, saima akoma ana zaginsu da fad'a masu suna 'YAN TA'ADDA, to wannan lokacin yawuce yanzu.

Alhamdullah anyi za6e lafiya kuma angama lafiya, dukda zuwa yanzun su Uncle basu gama samin kammala kan matasanba suma sun taka rawar gani a za6en, dan sun nusar da matasan wad'anda yakamata su za6a dansu tallafa musu.
Hakan kuwa ya razana 'yan siyasar, dan haka bayan duk sun d'are muk'aman sai suka fara jan matasan a jikinsu ana basu wasu manyan muk'amai.
Hakan yabama su Uncle damar cigaba da yad'a manufofinsu dakuma dunk'ule matasan a waje d'aya, suma Kansu gwamnatocin sunyi k'ok'arin bama su Uncle wasu muk'amai amma su Uncle d'in suka nuna basa da buk'atar hakan, su aikinsu dabanne.
'Yan siyasarfa sun fara canja takunsu akan matasan k'asar dan sun kula zuwa yanzu kan matasan yagama waye, bakowanne raini zasu d'aukaba, kuma suna son komawa za6e nagaba, Wanda take-taken matasan yana k'ara ankarar dasune akan sushiga hankalinsu, inba hakaba kuma su antayoka k'asa daga kujerar taka.
A gurguje please
*_3 years ago_*...............
Chapter 58 · 0% Book details