← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 66

Sashe 18

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

sheaik jafar Mahmud Adam tambayar nan, irin wannan amsar naji kuma yabada) amma ALLAH bai haramtaba, saboda masalahar gudun yad'uwar zinace-zinace yasa malamai sharhantawa". " kai kumama ai shekarunka basukai adamun ba har irin haka". A raunane uncle M.A yace, ''baba shekara 47 fa". Da sauri Innani ta juyo ta kalleshi, baba kuma yay guntuwar dariya. "Muhammadu kai yanzu shekarunka 47?". "eh mana baba, koma nafine?". 'Yaya maganar a raunane'. Yanzun kam ba baba ka d'aiba, har Innani sai da ta murmusa. "Lallai Muhammadu, to ai ko auren namu baima kai 45 ba sai a watan jibi, kuma awatan da aka kawo zainabu gidannan a watan tasamu cikinka, wannan lissafin kane dai kawai". " to Amma baba a takardar haihuwata ai hakane". "Yo Muhammadu takardar haihuwa ba kaine kaima kankaba lokacin dazaka sakandire, koka mantane?. lokacin da aka haifeka zainabu a rogo ta haihu, Dan ana goyon ciki a lokacin, tun cikinka Na wata bakwai akazo aka tafi da ita can, sanda tadawo min nan kanada wata biyu da kwana 26 a duniya, sannan ana arba'in biyu idan mace ta haihu tana wankan jego. "Na dai manta taka mai-mai miya faru karon haihuwarka, amma an haifeka da shekara 1 aka kifar da gwamnatin gawon, Murtala ya hau mulki, sai dai bana mantawa abinda nake ganin zan iya k'iyastashi da haihuwarka lokacin dai an cireka a mama da kwanaki 6 obasanjo yazama shugaban k'asa a mulkin soja ko zainabu?, da wannan kawai zan iya k'iyastawa gaskiya, saika bincika shekarun kagani". Innani tad'an gyara tsayuwarta a jikin bango, batareda ta kalli Uncle M.A ba tace, " hakane Malam dan bazan mantaba har shi ubasanjo ya sauka ba'a dawomana dashiba, har sai da iya ta rasu, dan munma fidda rai akan zai dawo wajenmu, nama haifi maijiddah har da cikin Barirah". "Wannan gaskiyane zainabu, dan haka saika lissafa kaga shekara nawa ya kama, ka had'a da shekaru biyu kafin mulkin shi Ubasanjo d'in". Waya Uncle M.A yaciro a aljihun gabar rigarsa, Dan yau ba babbar riga yasakaba, ya d'anyi danne-danne sannan ya d'ago yana kallon baba, yace, " baba 44 fa kenan". "To shekarunka kenan Muhammadu, kaga kuwa ba kai tsufan daza ace kagagara auren Khadija ba, kumama duk muture maganar shekaru, ai mahaifinta yasan daliln cewa kaine kadace ka aureta, kodan nagartarka, dukda yasan yawan shekarun naka ko. kuma koda shi baiyi hakanba ni zan aura maka ita da kaina, kaine kafi kowa sanin ciwonta, da yadda zaka kula da ita domin kwaranyewar damuwarta, ko Jabeeru ban yarda dashiba akan hakan, sai ka kwantar da hankalinka wajen kula da amanar da Sama'ila yabar maka, ALLAH yay muku albarka". "amin baba". Nasiha baba yamasa sosai, itama Innani tayi tata, sanan yamusu sallama yafito.
Chapter 18 · 0% Book details