← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 66

Sashe 26

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Amatallah kam yau lectures d'in yammane da ita, shiyyasa saida tayi girki ta tafi school, basu fitoba sai around 6:pm, a gurguje tamasu Rita sallama tashiga napep d'in dasuka tare mata, dansu a hostel suke, yau kuma Fa'iza ma batazoba, maybe jikintane dan cikinta yafara tsufa.
Ana kiraye-kirayen sallar magriba Amatallah ta shigo gida, babu kowa a falon dan haka tashige 6angarenta kawai. hijjab kawai tacire ta tashiga toilet dan d'auro alwala.
Koda aka idar da sallar magriba bata fitoba, dan fargabar had'uwa da Aneesa, da akayi sallar isha'i sai kawai tashigama wanka, tana fitowa ta shafa mai kawai tasaka bak'ar jallabiya. Yunwa takeji sosai, bataci abincin ranaba tafita, harta kai k'ofar fita tadawo falonta kuma, tayi haka yafi sau uku kafin tayi ta maula ta fito.
Tana fitowa yara Na sakkowa daga sama suda Nazeefa, da gudu suka iso gareta suna mata oyoyo, duk rungumesu tayi tad'auki Siddiaqa da itama tashiga rubibin 'yan uwanta.
Sannu da zuwa Nazeefa Tamata, tace, ''badai sai yanzuba?".
"A'a Anty Nazeefa, tun magrib nadawo, kuna cikine shiyyasa. Ashe 'yan tafiya sun iso?".
" kina fita suna isowa, dan inaga daga kaiki ma ya Jabeer yawuce ya d'akkosu".
''Ayya bara Na shiga Na gaisheta to".
"Okey, kishiga tana ciki".
Cikeda fargaba Amatallah ta nufi 6angaren Aneesa d'aukeda Siddiqa, d'ayan hannunta kuma tarik'e Ummita.
Muryarta nad'an rawa tayi sallama, Aneesa dake zaune a falo tana fiddoma Siddiqa kayanta ta amsa.
Shigowa Amatallah tayi, Aneesa ta d'ago ta kalleta, sukaima juna kallon ido cikin ido, kowannensu saida yaji fad'uwar gaba, amma Amatallah saitamata murmushi.
Yayinda Aneesa ta kauda idonta, fuskarta kadaran kadahan, ba ad'aureba bakuma a sakeba kamar ta Amatallah.
" bismillah ki zauna". Aneesa tafad'a tana zuge zip d'in jakkar kayan Siddiqa.
Zama Amatallah tayi a d'ofane saman kujerar kusada ita, ta d'ora Siddiqa a cinyarta, yayinda Umminta ta ra6u da jikinta itama, cikin dauriya tace, "ina yini, kundawo lafiya".
" lafiya lau, yamuka sameku?".
"Lafiya lau Aunty".
Daga nan kuma falon yay tsit, sai dariyar Siddiqa da Ummita kema wasa.
Kusan mintuna uku babu Wanda yasake cewa komai, sai kuma Aneesa ta katse shirun da fad'in " ya karatu?".
Amatallah tace, "Alhmdllh Anty".
''Masha ALLAH".
daga nan kuma suka sake yin shiru, kowa da abinda yake kissimawa a zuciyarsa kan d'an uwansa.
Mik'ewa Amatallah tayi tace, " bara mu barku Ku huta ". Bata jira cewar Aneesa ba ta fice.
Aneesa tabita da kallo tanamai jin wani irin kishi a k'asan ranta, dukda tafi Amatallah haske da hanci Dan Aneeaa farace, koma nace k'yau, hakan bai hanata jin zafintaba da fargabar had'a miji da ita.
Amatallah kam babu komai a ranta, sai dai ta kula halin Aneesa ya banbanta sosai da Fateema, a ranta tace ALLAH yabani ikon zama da kowannenku lafiya nidai.
Nace, " amin Amatallah".
A canma Fateema ta isa Dubai lafiya, sun rungume juna ita da mijinta cikin kewar junansu, tun a mota yake nuna mata yayi matuk'ar missing d'inta, sai shafa cikinta yake yana kissing wuyanta.
Itadai murmushi kawai takeyi da mamakinsa, saikace ba yau wata matar tabar wajensaba.
Koda suka isa gida dakansa yamata wanka, yakuma ciyar da ita abinci, daga nan kuma aka koma soyayya
su Uncle fa babu dama, dole matanka suyita tsula kishi a kanka
_____________________________
Abubuwa suncigaba da faruwa, wasu masu dad'i wasu marasa dad'i.
Zaman Aneesa da Amatallah dai sai a hankali, babu wani kulawa babu kuma gallazama juna, dan ba gargad'in wasa Uncle yayma Aneesa ba akan zaman lafiyar gidan, yakuma tabbatar mata inhar yaji wani Abu daban ita zai hukunta, tunda itace babba.
Itama Amatallah bai k'yaletaba, yamata gargad'i sosai.
To Alhmdllh babu dai wani gagarimin Abu daya faru, dan kowaccensu na gudun 6acin rai, kuma ma ga Nazeefa, duk abinda yafaru a gidan takan sanarma yayanta.
Rashin zamanma da Amatallah ke samu a gidan saboda makaranta saiya kuma sauk'ak'a wasu abubuwan.
Duk ranar asabar kuma suka had'u suduka sutafi gidansu Innani su yini a can.
Jikin babama Alhmdllh, dukda ciyone Na tsufa dai.
Masha ALLAH zuwa yanzun kam su Alhaji Muhammad baifi sauran 1month su dawo Nigeria ba, kuma Alhmdllh yasamu nasarori sosai akan abinda yaje nema.
Yanzu haka kam shirye-shiryen dawowar suketayi.
Tunda kwanakin dawowar Uncle M.A yazama 10days Anty maijidda tazo gidan, wasu kayan gyaran fata masu k'yau dana gashi ta kawoma Amatallah, ta nuna mata yanda zatayi kullum indan zata kwanta, sai wasu turarurruka masu masifar k'amshin tsiya, Na wanka dana gashi, ga mayuka masu k'yau da k'amshin tsiya,
Sosai tama Amatallah gargad'i akan tadage karta saka wasa a amfani dasu, sannan tace taringa shan fruits kullum safe da yamma, ga Nono shanu mai k'yau dana rak'umi tace tasaka a fright tanasha shima safe da yamma, sai kuma had'in Zuma da kayan k'amshi da mazar kwaila, shikuma da yamma kawai tanashan 3spoon.
Godiya sosai Amatallah tamata, dukda bata fahimci dalilin Anty maijiddar Na bata wad'annan kayanba, bakuma tasan ma'anarsu bama, tadai d'auka Na gyaran fatane dakuma murjewar jiki.
Duk yanda Anty maijidda tamata bayani haka ta dage sosai. aifa dandanan Amatallah tafara sauyawa, fatarta harwani shek'i takeyi, dama ga bak'inta mai k'yaune, k'amshi kam ba'a magana aii, ko da ga nesa ta giftaka saika jishi, su Goodness k'awayenta kullum cikin tambayar miya canjata haka sukeyi?.
Itadai sai dai kawai tamusu dariya bata cewa komai, dan har lokacin basu ta6a sanin tanada aureba, duk zatonsu Uncle datake yawan ambata shike rik'onta dai, Fa'iza cema taso ta d'an d'agota amma saita doje.
Fa'izan tace aibabu damuwa, inma tanada auren ai zasu sanine watarana.

Aneesa ba wani ganin Amatallah takeba sosai, shiyyasa bata kulada canjawar datayiba, sai dai k'amshin datakeyi kwanan nan yana d'aukar hankalin Aneesa, harma take mamakin ina Amatallah tasamo wannan k'amshin haka?.
Sai dai batada mai bata amsa, dodele tai gum da bakinta.
____________________________
*_RANA BATA K'ARYA_*
yauce ta kama ranar dawowar su Uncle k'asarsu ta haihuwa, tunda asubahi Aneesa aka tashi tafara gyaran 6angarensa, saida taga komai yad'au haske da shek'i, hakama tadawo babban falon gidan, 6angarentama haka, Nazeefa dai nata kallon ikon ALLAH, Amatallah ma batasan hidimar da akeyiba, tunda tayi salla takoma barci, sai wajen 7:30 ta tashi tayi wanka, ta shirya kamar yanda Anty maijidda takira ta Umarceta.
Bata dade da kammalawa ba Jabeer ya kirata akan tafito yazo d'aukarta.
Mamakine ya kamata, dan tasan yaudai babu school, dan Asabar ce.
Tana cikin mamakin saiga Nazeefa ta shigo itama cikin shiri. Kallonta Amatallah tayi tace, "Anty Nazeefa tare zamu fitane?".
''Eh".
Cewar Nazeefa.
" ina zamuje to, ko wajensu innani?".
"A'a, kedai kiyi sauri ki shirya, dansu Ya Muhammad k'arfe 5pm zasu sauka, somuke kafin 3 mu dawo kuma.
Amatallah batace komaiba tak'arasa shiri ta fito. shiru taji falon, dan haka ta tambayi ina yara?".
Jikin motar suka k'arasa Nazeefa tana fad'a mata suna gidansu wajen innani, Aneesa kuma tafita itama.
Mota suka shiga Amatallah Na mamakin wannan Abu, ina kuma duk zasuje abar gida shiru haka?, amma koba komai tayi murna, dama batason Uncle ya iskota agidan..................
Nace, "humm, Amatallah kenan, zakiyi bayani dalla-dalla-dalla da bakinki
One Luv my sweet fan's
*_ALLAH ka gafartama iyayenmh
[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_*
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
____________________
*_Number 17_*
____________________
Uncle M.A bai baro gidan Alhaji Sabi'u ba sai da suka tsara abubuwan masu yawan gaske, harda mutanen daya dace su tuntu6a domin samun had'in kansu a tafiyar.
Bayan sun kammala tsare-tsarensu Alhaji Muhammad yaymusu sallama yataho bayan ya ajiyema yara kud'in shan Chocolate's.

Daga gidan Alhaji Sabi'u gidansu yawuce ya gaida iyayensa, nanma yad'an dad'e sannan yataho da burin zai koma da daddare.
Harya tada mortar ya kashe, waya ya d'auka yafara laluben Number Amatallah yana murmushi.
Rabonsa da ita tunda yaje jos, kullum yakira saiyaji wayar a kashe, idan kuma sunyi waya da kawunta kunya yakeji yace yahad'ashi da ita.
Cikin sai'a kuwa yau sai Number tashiga.
Amatallah na zaune a tsakar gida itada Anty Sadiya da wata yarinyar makwaftansu Asiya tana mata kitso, Anty furera kuma nata kai kawo a tsakar gida tana girkin rana.
Game Amatallah keyi a waya hankalinta kwance, jefi-jefi takan saka baki a hirar Asiya da Anty Sadiya.
Kirane ya shigo wayar, wannan ne kuma karo na farko da aka kirata, dan ita mantawama take da wayar, tunda Uncle yabata suka gama gani ta kasheta. Bata kuma kunnawaba sai yanzu dataga games a wayar Asiya ta d'akko ta tura da films.
Number babu suna, shiyyasa ko kad'an batayi zaton Uncle baneba.
d'agawa tayi tareda manna wayar a kunnenta tace, "hello".
d'an lumshe idanunsa yayi ya gyara zama sosai da kwantar da kansa a jikin kujerar motar. Amatallah takuma fad'in " hello wanene?". cikin Nutsuwarta tayi maganar.
d'an murmusawa yayi sannan yamata sallama cikin sassanyar muryarsa datake matuk'ar so.
Bata buk'atar k'arin bayani kam, danta ganesa. saita samu kanta da fargabar amsawa.
Sai da Yakuma maimaita sallamar da cewa "My Best! Bak'ya jinane?".
" inaji Uncle, ina yini".
"Bazan amsaba, dan kinmin babban laifi my best, Wanda kuma kika cancanci hukunci mai girma da tsauri".
Amatallah ta marairaice murya kamar zatayi kuka, " wayyo ALLAH na, minayi Uncle?".
Chapter 26 · 0% Book details