← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 66

Sashe 23

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Baba da innani duk sunajin abinda ke faruwa a tsakanin 'ya'yan nasu. hakama Amatallah tana jiyosu, sai hakan yasata kewar families d'inta, dajin sha'awar inama tanada k'anne ko yayye itama, ko babu komai ai zasu tattauna akan matsalolinsu suji sanyi, wannan tunanin ne yasata kuka sosai. motsin shigowar Nazeefa yasata saurin share hawayen tacigaba da shinfid'a bedsheet a kan katifar.
"Anty Nazeefa kin ganni har yau ban gama gyaran d'akinba".
Dariya Nazeefa tayi tana ajiye tiren hannunta, "inafa za'a gama mana gyaran d'aki, kunyi bulum keda Yaya a d'aki kamar bakwa gidan kunata shan soyayya".
Cikin zaro ido waje Amatallah tace, " kai Anty Nazeefa, soyayya kuma? Uncle nefa". 'tak'are maganar kamar zatayi kuka'.
Sosai Nazeefa take dariya, "yo Amatallah ai yanzun yatashi daga Uncle, yakoma miji, ba laifi bane idan anyi soyayyar. Kinsan kuwa bala'in dacewar da kukayi keda ya Muhammad? wlhy karki bari damarnan ta ku6ce miki, ya Muhammad garas yake tamkar wani d'an 30years, yandama yakeda k'aramin jikinnan wasu d'auka suke ma Anty maijidda ce babba, kofa ya Jabeer yafishi jiki. wama zaice ya Muhammad yanada mata biyu, koda yake uku fa yanzun". ta d'agama Amatallah gira.
Baki Amatallah ta tura gaba, " Anty Nazeefa kibari Dan ALLAH, nifa ALLAH Uncle d'inane" ta matso hawen dasuka taru mata a ido tunda Nazeefa tafara maganar.
Kusada ita Nazeefa ta zauna, ta dafa kafad'arta, "kiyi hak'uri Amatallah, nasan anan gaba kad'an zakiso ya Muhammad amatsayin miji ba Uncle kad'aiba. na tabbata saiya nuna miki soyayya maiban mamaki, dan soyayyar dayakema Yaya Isma'il duk zai tattara yahad'a da wadda yake miki, ya Muhammad yanama ya Isma'il k'auna maiban mamaki, to yakike zaton kuma kasancewarki matarsa jinin masoyinsa ya Isma'il?, gakuma ke kanki dama yanda yake sonki sosai tamkar 'ya'yansa. lokaci kawai muke jira na ganin hankalinku ya kwanta dagake harshi, dan har yanzu duk kuna cikin rud'anine na abubuwan dasuka faru, amma nabaku shekara d'aya zuwa biyu kacal, insha ALLAH sai kunzama abin kwatance a duniyar masoya. Ke dai kawai ki koyi yanda zaki zauna da matansa, dan gidan ya Muhammad zama akeyi namasu ilimi da kissa, kowacce jitake da kanta akan tayi karatu mai zurfi, saiki dage sosai akan karatunki, tunda inada tabbacin yaya bazai barkiba kema, zai maidaki makaranta, fatana dai kirage wannan sanyin naki, dan zama dasu Anty Aneesa sai jaruma, kuma mai wayo. Zan cigaba da baki haske a zaman mu, yanda kema zaki kwaci 'yancinki a hannun mijinki, harma kizama tauraruwa fiyeda kowa a zuciyarsa kinji".
Kai kawai Amatallah ta jinjina mata, tasaka hannunta biyu ta share hawayenta, sai dai k'asan zuciyarta tana tunanin yanda za'ayi ta zauna da Uncle d'in nata a matsayin miji, bayan zuciyarta tana girmamashi tamkar mahaifinta, tabbas maganar Anty Nazeefa gaskiyace, babu wanda zai kalli Uncle yace yakai shekarunsa, saboda k'aramin jiki da ALLAH yabasa, baza'a kirashi siririba, hakama bashida k'iba, sannan yana tsaka tsaki a tsawo, ba dogoba ba gajereba kuma........
Girgiza tan da Nazeefa tayi ne yasata sakin ajiyar zuciya.
Nazeefa tace, "kinga bar aikin mu karya tukunna ko".
" to".
Kawai Amatallah tace tamik'e, MacLean da brosh ta d'auka tafita.
Nazeefa tabita da kallo a sanyaye, tausayinta na kuma ratsata, a fili tace, "insha ALLAH zakiyi farin ciki a rayuwarki Khadija, nasan ya Muhammad zai kawo sauyi a duniyarki, ALLAH dai yak'ara baki hak'urin jurewa wannan jarabawa tarashin iyaye lokaci d'aya, kuma yakawo mana sauk'in rikice-rikicen dasuke sanadin wargaza farin cikinmu a k'asarnan. ALLAH ma yay miki gata ke, tunda yabarki da Ya Muhammad, a kwai yara irinki masu yawa dasuka shiga halin k'uncin rashin families d'insu ta sanadin irin wannan rikice-rikicen *SIYASA KO K'ABILANCIN*, amma rashin gata damasu tallafa rayuwar tasu yasasu shiga k'angin wahala da tarwatsewar rayuwar tasu suma, ALLAH ka kawomana iyakar wad'annan matsaloli dai."
Nace, "amin Nazeefa
____________________________
Tunda yafita sai Aneesa tafad'a gadonsa ta hau rusa kuka, tabbas sunada aiki agabansu, yarinyarnan bama ganinta yakeba a shekarun baya yasuka k'are, kullum zancenta na bakinsa, inaga yanzu ta dawo kusa dashi, tana amsa sunan matarsa kuma.
Tunda k'addara ta dawo da Amatallah Kano basu sake samun kan mijin suba, motsi kad'an yana gidansu, dasunyi magana saiyace yaje duba jikin babane, insunyi k'orafi akan Amatallah yace basuda tausayi.
Tasan yarinyar nabata tausayi, amma gaskiya tana matuk'ar kishin mijinta, taso ace daga ita sai shi da 'ya'yansu zasu rayu, amma tunkamma tazo gidan saita taras wata tarigata shiga, maimakon abarta taji da zafi d'aya, gashi kuma rana tsaka ankuma aura masa wata, k'aramar yarinya ma, sa'ar k'anwarta ta biyu.
Dolene ta d'auki mataki wajen ninka soyayya da kulawar datakema mijinta fiyema data dacan, dan tafison yasota fiye da kowacce acikinsu. jibafa tunda tayi sallar asubahi taketa kaida kawo wajen ganin tahad'a masa break fast mai rai da lafiya, saboda ganin kwana biyu bayacin abinci sosai saboda damuwar dayake aciki tarashin amininsa. (Duk da dama shi bamai yawan cin abinci baneba) Amma dan wulak'anci shine yafice wai sauri yakeyi, yanzu haka kuma yanacan wajen bak'ar yarinyar can.
saita kuma rushewa da kuka kuma.
Nace, ''bantan uba, Aneesa kinada aiki wlhy
, zan bama Xoxo kwangilarki
Ita kanta Fateema abin yabata mamaki, ganin yafita cikin fushi ko d'akinta bai kallaba, bayan kuma k'a idarsane duk Safiya zai shiga d'akin wadda ba itace da girkiba su gaisa, hakama idan yadawo aiki zai shigo miki, yaji ya lafiyarki keda yara, da darema kafin a kwanta zai shigo yamiki sai da safe yama yaransa addu'ar barci. Amma yau ko yaran bai sauraraba, saima k'arar bud'e gate da rufewa sukaji.
Cikin damuwa tagama musu shirin makaranta ta turasu wajen Aneesa suyi break fast, amma sai suka dawo suna sanar mata momyn batanan, kuma ko Saifudden ma ba'ama shirin school ba.
Tashi tayi tafito, ta lek'a 6angaren Aneesa batanan, har bedroom sai Siddiqa dake barci a kan gado, tad'anyi knocking k'ofar toilet amma shiru, saifudden ne kawai kwance afalo lullu6e da towel, da alama wanka aka masa ba'akai ga shiryashiba ma, dan ga uniform d'insa nan a gefensa da manshafawa da turare.
Kallon Sahib tayi tace, "Sahib jeka saman Abbu kagani kotanacan tana sharane".
" to Umma". Sahib yafad'a yana fita da gudu.
Babu dad'ewa ya dawo yafad'a mata tana d'akin Abbu tana barci.
"Barci kuma? lafiya kuwa?".
fita tayi tana fad'in " Abulkhairi tada Saifudden ka shiryashi ina zuwa".
Sai da tayi sallama kusan sau uku sannan Aneesa ta amsa.
Fateema tashigo d'akin idonta akan Aneesar.
"Momyn yara lafiya kuwa?".
Tashi Aneesa tayi zaune, tayi kwafa sannan tafad'ama Fateema abinda yafaru, dan aganinta wannan matsalace dazasu raba tare sukuma d'auki mataki akanta.
Fateema tace, " Humm momyn yara kenan, nimafa haka yaymin ranar da yarinyarnan ta farfad'o, gaya mikine kawai banyiba".
Aneesa takuma yin kwafa, tace,
"Wana mataki kike ganin zamu d'auka? inba hakaba yarinyarnan saitama kiremu daga kan 'yayanmu wataran, dan naga rawar jikin dayake akanta tayi yawa tunkanma tashigo gidan, raina mana hankali kawai akayi, za'ace wani babanta yarok'eshi ya aureta, wlhy dama can son yarinyarnan yakeyi, shima Baban nata ya gane hakanne shiyyasa ya k'ak'aba masa. nifa har mamakin yanda babanku yayarda yama Muhammad wakilcin auren nakeyi, bayan kuma yasan keza'ama kishiya".
Duk da maganar Aneesa ta k'arshe ta 6atama Fateema rai haka ta danne saboda kishi na cinta itama, tace, "miye shawararki to akai? Nasan dai Muhammad bazai ta6a sakin Amatallah ba, kodan k'aunar mahaifinta dayakeyi".
''Yo idan shi bazai iya sakintaba, ai ita saimu sata masa bore tace bata sonsa, ai dole dai ya barta ko".
" hakane, amma tayaya zamuyi hakan?".
''Muyi tunani na kwana uku, abinda kowa ya yanke saimu tattauna yiwuwarsa mugani kawai, koya kikace?".
"Hakan yayi d'in, yara sun shirya, ke suke jira karsu makara".
Mik'ewa Aneesa tayi suka sakko k'asa tare, a gaggauce suka bama yara break fast dan mai keke napep d'in dake kaisu makaranta yazo................
Nace, " humm, wai Fateema da Aneesa ne yau a inuwa d'aya
, lallai Amatallah da k'arfinta tashigo
Chapter 23 · 0% Book details