← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 66

Sashe 49

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Murmushi tayi tareda shafa fuskarta tana fad'in my Uncle I love you so much, lallai ka cancanci kowacce mace ta haukace a kishinka, hummm wani sirrin saidai *RUHI* kawai".
Dahaka ta koma bedroom d'in ta gyara, ta tartare kayanta a ledar ta ajiye gefe. Saidaifa wlhy bazata iya fitaba, to dawane idon zata kalli jama'a?.
Nazeefa takira wai Dan ALLAH tazo.
"Nazo namiki mi? yarinya kima sakko idan zaki sakko, ai gidan babu mutane sosai".
" please Anty Nazeefa, ALLAH bazan iyaba inajin kunya".
"Meyasa baki biyo mijinkiba, kinga shi gashina yanata gaisawa da dangi, kuma mai hotoma ya Jabeer ya kawo, gakuma 'yan jos nan su Anty Sadiya sun iso yanzunan".
" da gaske Dan ALLAH Anty Nazeefa su Anaty furerane?".
"ALLAH kuwa, gasuma Suna gaisawa da Yaya a falonki........."
Ai tuni Ama....ta manta dawata kunya bare abinda yafaru da ita, dukda tanad'anjin zafi hakan bai hanata sauka dad'an guduntaba, wannan yasa duk kallon k'urillarka bazaka gane mitake cikiba. Ta wuce su anty maijidda Afalo.
Duk dariya suka saka mata, har Aneesa kasa daurewa tayi ta dara, (a ranta tana kuma jinjina tsantsar k'uruciyar Amatallah).
Anty maijidda tace "k'uruci kenan dangin hauka".
Nanma dariyar dai akayi, kishiyar Anty maijidda tace nikam tana birgeni, ko kad'an batada damuwa Amatallah wlhy".
Aneesa tayi murmushi tace, " gaskiya tanada hak'uri, tunda babu mai cewa tamasa wani Abu Mara k'yau a gidannan wlhy, ALLAH dai yacigaba dabamu zaman lfy".
Gaba d'aya akace amin.
Kowa yasan Aneesa tanada kishi, amma macece mai fad'ar gaskiya da mutunci idan taso, gashi bata iya wulak'anta dangin mijiba, ita kowa natane, duk sharrinka wlhy bazakace kazo gidan ta wulak'antaba, ko Fateema datake 'Yar uwarsu jininsu iyaka dai kenan, (kishine dai kam ba'a cewa komai a wajen Aneesa
). amma kam tanada fada sosai wajen dangin mijinta dana kishiyarta, (zatayi kishi kam dake, amma danginki komai a mutumce)................
One luv my sweet Fan's
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu_*
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_*
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce
____________________
*_Number 32_*
____________________
Amatallah Na shiga ta cikukuye Anty Sadiya dake kujerar farko, "fad'i take oyoyo anutys d'ina, saikuma tasaki Sadiya takoma kan Anty furera da Asiya.
Uncle dai murmushi kawai yake zubawa, yaji dad'in ganin Amatallah a farinciki, kullum haka yake fatan ganinta, bayason ta yawaita kukan maraici.......
Maganar Anty furera ta katse masa tunani.
" uch Amatallah, wai yaushe zakisan kin girmane?".
"Babu rana Anty furera". Amatallah tafad'a tana dariya, suka had'a ido da Uncle, gira yad'an d'aga mata.
Ta kauda idonta tana murmushin itama.

Humm yau Amatallah fa ba'a magana, tana nanik'e da Aunty's d'inta sunata shan hira dabata labarin jos.
Suma sunji dad'in yanda sukaga ta murje tayi k'yau, hakan ya nuna musu hankalinta ya kwanta, Alhaji Muhammad yarik'e amanar d'an uwansa, dukda sunga kamar batada walwala sosai, amma jin dad'in ganinsu Na k'ok'arin danne hakan, babu Wanda ya tambayeta damuwarta cikin su, tunda sunsan zaman aure saidai hak'uri, komin San da kukema juna dolene wataran a k'untatama juna, bakomai ake samu 100% ba.
Ansha hotuna kafin Uncle yafice sabgar gabansa.
Ita ta rakasu d'akin maijego Uwargida, taci gayunta cikin had'ad'd'iyar shadda popul, hakama jaririyar anmata gayu, Ummita tana nanik'e da ita, saikuma wasu daga cikin danginta dake cin abinci, wasu kuma hirarsu sukeyi.
Duk suka gaisa a mutunce.
Fateema ta kalli yanda Amatallah tayi k'yau cikin kwalliyarta, k'ok'arin danne kishinta tayi kamar yanda ta saba, tayi murmushi tana fad'in Anty yara kinyi k'yaufa, kamarma kece mai jegon".
Murmuahi Amatallah tayi, ta 6oye fuskarta jikin Ummita dake kan cinyarta tace ''kai Anty kecema ai sarauniyar k'yau d'in, kinganki kuwa?".
Dariya wad'anda ke kusadasu sukayi, abin kuma ya birgesu tamkar ba kishiyoyiba.
Aneesa tashigo itama ta cakire cikin less jaa, tayi k'yau sosai, fleets takawo saboda bak'i, itama Fateema saida ta tsokaneta wajen yaba kwalliyarta.
Aneesa ma ta danne zuciyarta da kishi tayi murmushi tana fad'in "lallaima Umman yara, bakiga kankiba kenan keda Antyn yara?, karfa Ku rud'a mana Abbun Abulkhairi wlhy".
Sosai akeyin dariya a d'akin, kasancewar Aneesa a tsaye take sai kowa yaji maganar datayi.
Sosai suka birge kowa, (har nimafa
, sainaji ina sha'awar kishiya amma ta yini d'aya
lol).
Cikin girmamawa Aneesa tafara gaida su Anty furera.......
Amatallah ta katseta dafad'in " Anty Aneesa zafasuzo Ku gaisa".
Murmushi Aneesa tayi (saboda taji dad'in wannan girmamawa, damafa Aneesa akwai son girma
) tace, "to shikenan, bara naje Na jiraku, dama an bani sak'o nabaku keda Umman yara".
Atare sukace to, Fateema ta kalli Aneesar tana fad'in mu taso kenan?".
"A Ku k'arasa tu kunna, nima akwai abinda nakeyi."
Okey.
Su Anty Sadiya sund'an dad'e a 6angaren Fateema kafin suje 6angaren Aneesa ma, anan Aneesa ta had'a musu abinci, takumace anan zasuyi sallah.
Godiya sukai mata da k'ara yaba kirkin kishiyoyin Na d'iyarsu Amatallah.
Aneesa da Fateema da Amatallah kam sunacan saman Uncle, Aneesa tasanar dasu
cewa Uncle yace zaizo da bak'ine wai da la'asar, " yakuke ganin zamuyi kenan? Yace yakiraki baki d'agaba Antyn yara".
Amatallah tace, "Na manta wayarne a d'akina mukaje 6angaren Anty".
" okey, yanzu miye shawarar abinda za'a tanadar musu?".
Fateema tace, "kai Abbun Abulkhairi ma dai akwai kwak'ule-kwak'ule, yanzu Dan ALLAH d'azun dazai fita ba'a gabanki Na tambayi kozaiyi bak'iba a jiye musu abinci?, amma yace a'a". Tayi maganar tana kallon Aneesa.
" to yazamuyi umman yara, kinsanshi dai ai, yanzu kawai mu nemi solution, Dan yace bak'infa Na kunyane. Antyn yara bakice komaiba fa?".
Murmushi Amatallah tayi, "to Anty mizance, Abinne Na Uncle saishi, yanzu kawai inaga ayi jaloff d'in shinkafa mana, ahad'a da tuwon shinkafa ko semo...., tunda ga masa za'a kawo daga idansu Innani kamar yanda naji su Anty maijidda nafad'a. Kobaiyiba?".
" yayi kuwa sosai wlhy, akwai zo6oma, dukda muma munada namu mutanen, sai a d'an d'iba kad'an".
''Shikenanto, dama yace shehu zai kawo drinks da ruwa asaka musu k'ank'ara". Cewar Aneesa kenan.
Amatallah tace, "to inhakane ahad'a da kunun aya".
Fateema tace, " amma har ayi? Yanzufa biyu saura, kumafa 4 yace?".
"Walhy har ayi Anty, aigasu Anty Nazeefa ga Asiya duk zasu taimaka mana da aikin".
" to shikenan, gasuma Ramla nan, aikin mi sukeyi, duk saisu had'u ai su taimaka muku, (k'annen Fateema ne suma, amma duk da aurensu).
Sund'an k'ara shawarta abinda zasu k'ara dashi sannan suka sakko k'asa.
Chapter 49 · 0% Book details