Sashe 3
Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Muhammad buhari ya mulki Nigeria daga 31 December 1983 zuwa 27 August 1985. General Ibrahim badamasi babangida IBB, ya mulki Nigeria daga 27 August 1985 zuwa 27 August 1993. Chief Earnest shoneko General Sani abacha, yayi shugaban Nigeria a 1993-1998 General Abdussalam Abubakar, ya mulki k'asar a 9 ga June 1998 zuwa 5 ga may 1999. Alhaji Umaru Musa 'Yar Aduwa, yayi shugaban k'asar daga 29 may 2007 zuwa ranar 5 may 2010. Goodluck ebele Azikiwe Jonathan 2010-2015. Muhammad buhari a yau kuma a mulkin farar hula. ________________ Alhamdullah, wannan shine tarihin k'asarmu ta gado a tak'aice, Wanda keneman k'arin bayani, zai iya kwakwkwaran bincike ga masana, nidai iya abinda ALLAH yabani ikon tattarowa kenan a taskar masanan. *yanzunne labarinmu zai fara kai tsaye*. Plartoar state (jos) Shima jihace data kasance a cikin yankin Arewa, sai dai tanada yawan k'abilu, sannan d'auke take da mabiya addinin Muslim's and Christian's. Wannan yasaka yawan k'abilanci da rikice-rikice a yankin, mafiya yawan rikicin kuma *_SIYASA KO K'ABILANCI!_* ke haddasasu, amma bada wani nisaba saikiga yazama Fad'an *ADDINI*, shiyyasa al'umar wannan yanki ake yawan musu kutse wajen haddasa fad'ace-fad'ace. Jos tana d'aukeda manyan k'abilu kamar haka. Afizere, Afo, Alago, Anaguta, Amo, Ankwel, Bashiri (bashirawa), akwai kuma mafi yawan k'abilar Hausa fulani ma a jihar. *Khadija Isma'il Uba (Amatallah)* Itama tafitone daga wannan k'abila ta Hausa Fulani, wadda sanadin cirani ya tilasta musu maida jihar jos asalin jiharsu ta haihuwa, wadda zasu iya bugar k'irji su kirata k'asar kaka da kakanni....... *_ALLAH ka gafarma iyayenmu [1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing *_HASKE WRITER'S ASSO..._* *_SIYASA KO K'ABILANCI_* _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce ____________________ *_Number 3_* ____________________ ........Amatallah wai mikike tunani haka? tun d'azun kin saka abinci gaba kina jagwal-gwalasa kink'i kici?. d'ago manyan idanunta tayi tana kallon Amminta, ta janye idanun nata saboda kwalla dasuka ciko, muryarta na rawa tace, "ALLAH Ammi na k'oshine". " Amatallah banason shashanci fa wallahi, mikikaci dakika k'oshin? kofa abincin rana baki masa cin arzik'iba, lauma batafi hud'uba kika ajiyemin kika fita wai kina saurin islamiyya, shine yanzu zaki cemin kin k'oshi kuma........?". "Miya farune kuma?". 'Baban Amatallah dake fitowa daga d'akinsa yay tambayar'. Daga Amatallah har Amminta kallonsa sukayi. Ammin tace, ''abinda kasanine kullum dai, maganar cin abinci". Guntuwar dariya yayi, yak'arasa cikin falon inda Amatallah ke zaune jikin kujera, a kujerar data jingina ya zauna, " haba mamana nikad'ai, ci abincin mana, babufa k'yau zama da yunwa, a haka kikeson zuwa hutun kano gidan Uncle d'in naki kuma?". "Baba zanje, amma ALLAH na k'oshi". 'Tayi maganar tana matso hawayen datake mak'alewa tun d'azun'. " subahanallah mamana, kuka kuma? kinga tashi ki maida abincin kitchen, kizo ga fura dana saya miki lokacin dazan dawo aiki". Murmushi tayi tana share hawayenta, tamik'e da sauri tanufi kitchen da fleet d'in abincin. Binta yayi da kallo yana murmushin shima. Ammi kuma tace, "wallahi kaine ke saka yarinyarnan duk wata ta6arar datakeyi, nidai ina tuna muku halin rayuwa, kuma gidan wani zata". a k'ufule tayi maganar tana shigewa bedroom d'inta. Baba yabita da kallo kawai yana girgiza kai, yasan gaskiya take fad'a masa, to amma bashida za6in daya wuce gatanta tilon d'iyar tasa, wadda tundaga kanta haihuwa tamusu adabo, shekara kusan 19 kenan amma ko 6ari matar tasa bata sake yiba. ajiyar zuciya ya sauke saboda motsin zaman Amatallah akusa dashi. Tace, " baba nad'ako, nagode sosai, ALLAH yak'ara bud'i". "Amin mamana, ALLAH yay miki albarka kinji". ''Amin baba". Hirarsu suke d'anyi itada babanta, dama kullum haka sukeyi, sai dai yau hirar tasha banban data kullum, Dan yau duk akan abinda yafarune d'azun Amatallah take sake tisama baban nata labarin, muryarta kawai zata tabbatar maka har yanzu a tsorace take. Ammi ma fitowa tayi tazauna, har kusan 10:30pm suna hira, kafin su tashi kowa yanufi d'aki yayi shirin barci. Wata sabuwa Amatallah takasa barci, abinda yafaru d'azun yafara dawo mata dalla-dalla, saita ringa ganin su zike tsaye akanta da wuk'a, da sauri ta kunna fitilar d'aki, tashiga kalle-kalle, amma babu komai, duk da haka kasa barcin tayi, sai can cikin dare barci ya figeta. A firgice ta farka ta kwalla wata razananniyar k'ara, saboda mafarkin datayi su zike sunzo har gida zasu kasheta. K'arar tace ta farkar da iyayenta, arazane suka nufo d'akin, tana ganin su tafad'a jikin Amminta tana kuka, jikinta sai rawa yakeyi. Abu kamar wasa k'aramar magana tazama babba, Amatallah takasa barci, takuma hana iyayenta, tun suna d'aukar lamarin wasa har ya fara basu tsoro, Dan Amatallah harda sumanta, kafin asuba kuma zazza6i yama jikinta rijif, maganarta ko fita da k'yau batayi. __________________________ A gaggauce ta taimaka masa ya kimtsa cikin jallabiya Brown mai gajeren hannu, ya d'an fesa turarensa sannan suka sakko falon k'asa, yaran suna zaune suna kallon wani program na yara a wata tashar larabci, duksun maida hankalinsu sosai a tv n. dan har Abbun nasu yak'araso cikin falon basu saniba, jin jina kansa kawai yayi yana kallonsu da murmushi. Matarsa ta ajiye k'aramin kwano mai d'auke da dabino a agabansa, sai ruwa a jug na glass. Kallon dabinon yayi sannan ya kalleta, "no, nifa naci dabino a mota, bani ruwan dai". Ruwan ta tsiyaya a k'aramin Kofi ta mik'a masa, ya kar6a yana mai fad'in " jazakallahu khairan my wify". "Amin Nurrina". Sai da ya shanye tas ya ajiye kofin, yana anbaton " Alhamdullah". Tace, "saura abinci kuma". " okey, had'amin, bara na duba jikin Saifuddeen". Bai jira amsartaba yanufi 6angaran amaryarsa. Tana zaune a falonta, nono take bama Siddiqa, gefenta kuma ga wani yaro zaune yana kuka da Kofi k'arami a hannu, da alama tsaresa tayi dole yake shan abinda ke cikin kofin. Sallamarsa ce tasaka yaron k'ara k'arfin kukansa, itakuma tad'ago kai tana kallonsa da amsa sallamar. Da d'an sauri yak'araso falon, kusada yaron ya zauna, "Saifudden miyafaru kuma da kuka haka? mi kika masa?". A sanyaye tace, " nikam mizan masa dear?, tea kawai nace yasha nabasa magani shinefa yake wannan kukan iskancin, kadai san Saifudden ai".