← Book details Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 66

Sashe 52

Siyasa Ko Kabilanci Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

biyu sukayi shirin tafiya, tabasu alkairin da Uncle yabata, itama tahad'a da nata, Fateema ma ta had'a musu kayan suna, Aneesama ba'a barta abayaba, tare suka fita dasu Anty maijidda, sukaje suka gaida su Ammi sannan Nazeefa tarakasu tasha suka hau mota. Gida kam yazama dagasu sai su, su Anty badiyya ma da inna Nafi suna kammala suyar Nama suka tafi. Amatallah da Aneesa suka kuma dagewa suka k'imtsa gidan tsaf, daganan Ama... takoma gefe tana kallon Aneesa data kasa zaune takasa tsaye saboda yau miji a hannunta yake. Duk abinda Aneesa keyi Amatallah k'arin ilimine a wajenta, tsaf take k'ara karantar komai da nazarinsa, tanaji a ranta itama lokaci yayi daza'a dama da ita. ( lol.) ************ Alhmdllh, su Uncle sun sami hallarar inda zasu gudanar da meeting d'insu. Su 12 suka halarci wajen, dukda ba iyakarsu kenanba, akwai wad'anda suka yanki form kusan su 26, to amma su sun ware kan nasune amatsayin shugabanni wad'anda zasu tattauna akan kafa k'ungiyar, dukansu masu ilimine, kuma babu Inda zasu shiga ba'a dama dasuba a k'asar. Alhaji Sabi'u ya gudanar da addu'oi kafin su fuskanci abinda ke gabansu. An tattauna da mahawara mai zurfin gaske, sukace dole Uncle ne zai shugabanci k'ungiyar, Dan shine yafi cancanta da hakan, kodan k'ok'arinsa da k'yak'yk'yawar manufarsa. Ya nuna musu shifa baya buk'atar shugabancin, Dan haka abama Alhaji Sabi'u ko Alhaji Murtala mai daura. An dad'e ana tata6urza akan sudai shid'in sukeso, kuma harsu Alhaji Murtalan. Dolen dole Uncle ya kar6a wannan shugabanci, Alhaji Sabi'u mataimakinsa, saikuma Alhaji Murtala mai daura sakatare, saikuma wasu muk'aman dasuka biyo baya irinna ma'aji da dai sauransu. Tun anan suka fara wasu tsare-tsaren, kamar yad'a manufarsu ga matasan dakuma jawo hankalin masu zuciyar taimako domin zuba sadak'atujjariya a bitalmanin k'ungiya, saikuma bud'e wasu businesses k'anana dazasu tallafi k'ungiyar wajen samun kud'in shiga dadai sauransu. Anan take kowannensu yay alk'awarin bada gudunmawa dai-dai k'arfinsa, dan haka aka bama ma'aji damar bud'e Account da sunan k'ungiya dan a fara zurara kud'in dasuka tara, ansama k'ungiyar sunan *_YOUTH AWARENESS FORUM_*, bayan ankawo sunaye daban-daban dai suka tsaya akan wannan d'in. Uncle dake jawabi yabisu da kallo d'ai-d'ai yana murmushin jin dad'in had'in kan daya samu nasu, bayan yayi doguwar godiya agaresu yad'ora da fad'in "to Alhmdllh 'yan uwana, yanzufa saimunyi hak'uri da juna, muji muk'iji, mugani muk'i gani, karmu d'auka wannan yak'in namu zai zama mai sauk'i, dolene zamu fiskanci k'alubale daga matasan Kansu, dan basu ganin irin wad'annan abubuwan a yankinmu, sannan akwai marasa son gaskiya dazasu fara sukarmu, musammanma jam'iyun siyasa, amma wannan bawai damuwa baneba, dan mud'in bawai 'yan siyasa baneba, amma munason mukawo sauyi akan yanda siyasar kejan ragamar rugujewar matasanmu damu kanmu, inhar kace zaka tara al'uma koyin wani Abu mai k'yau da amfani arayuwa dolene kayita fuskantar k'alubale, wani mai dad'i, wani maicin zuciya, wanima harkaga yata6a iyalinka. abu nagaba shine mu tsaftace harshenmu, muringa sanin kalmomin dazasu fito a cikin bakunanmu, danfa ayanzu komai namu zaizamto abin ajiyewa ga 'yan jaridu dakuma al'umma, sai lokacin damuke hangen nasa ayi amfani da wannan a 6ata mana suna kocin zarafinmu. Saikuma mu kammu muji tsoron ALLAH karmu kasance munafukan juna kokuma fidda wani sirri Na k'ungiyarnan, yin hakan zai iya zama illa agaremu, muyi hak'uri da juna domin ALLAH, duk Wanda ya sa6ama wani yakirasa ya sanar dashi a fiskanci juna tunda mud'in ba yara baneba. a yanzun kiranyenmu zai farane daga kan matasa masu shaye-shaye, dan anfi samun nasara akansu wajen haddasa rikice-rikicen *SIYASA KO K'ABILANCI*, yanzu dai gashi an kad'a tamburan siyasa, kuma naga gangar shaid'an tafara aiki a jikkunan matasanmu, dan haka zama bai ganmuba kenan, zuwa nanda kwana uku saimuyi zama Na musamman akan wannan matsalar, mu tattauna da duba hanyar data kamata mubi koya kuka gani?". Gaba d'aya sunyi ma'am da zancensa, sunkuma yabama k'ok'arinsa, Alhaji sabi'u ma yatashi yay jawabi, daganan kowa daki-daki yayi nasa, kafin taro yatashi cikin addu'ar samun nasarori da fatan alkairi waa juna.............. _kuyi manage da wannan, ban yini a gida baneba._ One luv my sweet fan's *_ya rabbi ka gafartama iyayenmu_* [1/19, 8:33 AM] Aysha Galadima: *_Typing *_HASKE WRITER'S ASSO..._* _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce _gaisuwa da fatan alkairi, *Dan mom and Sani Ilyasu*_
Chapter 52 · 0% Book details