Sashe 9
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dago kai yayi ya kalle su yana sauke ajiyar zuciya,
,"Halima ta riga mu gidan gaskiya,Allah ya karɓi abinshi "
Ji kake wurin yayi wani tsit na ɗan lokaci tamkar babu mutane a wurin kafin Manu yace"ni fa Innar Jauro nake magana"
Dafa kafadarshi yayi "kwarai kuwa ita,ni kaina na kasa yarda gani nake kamar a ko wani lokaci tana iya dawowa bayan da hannuna na saka ta acikin kabari"
Yakubu ya fashe da kuka yana salati,domin su biyun sun kasance yan dakin ta sosai na tsayin shekaru huɗu da sukayi yawo,
Sosai yaran suke jajanta rashin Uwar dakin nasu,
"Ina roƙon wani alfarma mai girma a wurinku"
Duk mai da hankali kanshi suka yi, "muna jinka uban ɗakin mu"
A jiyar zuciya mai ƙarfi ya kara sauke,yana jin wani irin ciyo da raɗaɗi mai kuna yana taso mashi daga ƙasan zuciyar shi,
"Alfarman da nake nima babba ne wanda bansan ko zaku iya rikewa ba ko ba zaku iya riƙewa ba,abu ɗaya na sani shine na yarda daku har cikin zuciya ta,ba ni da wanda zanba amana sama daku,idan har kunci amana ta Ubangiji na kallo domin ni saboda yarda na bayar,idan kuma Allah ya baku ikon rikewa Alhamdulillah,
Ina so ku dauki Shanu garke ɗaya,raguna da tumakai rabin garke,ku tafi da su "
Duk kallon mamaki suke mai,"mu tafi dasu ina,bayan gashi mun dawo gida,yanzun lokacin damuna ne ai ba rani ba"
"Haka ne,sai dai kuma ina da dalilina na yin haka,Manu ba ni da lafiya sosai,ako wani lokaci komai na iya faruwa dani,ƙila ana iya kwantawa dani ba'a tashi da ni ba,
Abinda nake matukar tsoro kenan,
Saboda ƴan uwana,nasan da zaran bana raye zasu karbe komai na dukiya ta daga hannun ku,nasan ba zasu ajiyema ɗana komai ba,kuma koda ya girma ba bashi zasu yi,
Shi yasa nake son ku tafi dasu,ku yi nisa dasu,in so samu ne kuna iya komawa dasu nahiyar ku ta Niger daga nan har zuwa sanda Jauro zai mallaki hankalin shi,"
Yakubu ne yace "uban gidana kamar nan da shekara nawa kenan?
" Yanzun shekaran Jauro shida,yana ƙoƙarin shiga na bakwai,dan haka nan da shekara Goma sha biyar"
Duk kallon mamaki suke mai,dan basu zata zai ja da nisa ba,
"Amma kana ganin bai yi yawa ba"
"A'a bai yi yawa ba,sannan bana son ƴan uwa na su sani,kawai in so samu ne ku yi yanda nace sannan ina son ku tafi tun kafin gari ya fara haske dan bana son su san iya adadi abinda kuka tafi dasu"
Allah sarki,a haka suka karɓi wannan amanar da Yakubu da kuma Manu,sannan cikin wannan daren suka bar rugar da taimakon shi Dottiya,suna mashi fatan samun tsawon rai don coyon hanta mai tsanani yake fama dashi wanda yayi chronic sosai.
Washegari da safe da kanshi ya shirya Jauro kuma ya raka shi har gidan su Moha inda zasu tafi Boko da keken shi,
Bayan ya dawo ne ya tafi shiyan Bube wurin Inna domin sanar da ita isowar shanayen shi.
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*12*
Sallamarh yayi yana shiga cikin ɗakin nata,
Amsawa suka yi suna matsa mashi dan ya samu wurin zama,
Saida ya fara gaida Inna Mari kamin ya juya ya gaida su a jam'i,sannan ya zauna,
"Nikam Dattiya me ke damun ka ne,naga duk ka lalace"cewar Baffa Sanda.
" Babu komai,"
"Amma ka yi kaman wanda ke cikin rashin lafiya" Wannan karon Bube ya tambaya,
"Ya dai kamata ka cire Halima arai haka nan,tunda kasan dai wanda ya mutu ba shi dawowa,dubi yanda ka kanjame,ai da irin wannan tunanin da zai iya hallakaka gara kawai kayi aure ko zaka rage tunani"
Shiru yayi yana kallon Inna,ko fa sati ɗaya matarshi bata gama cikawa da rasuwa ba,amma shine har take dauko mai batun wani aure,ya tabbata idan da yarta ce ta mutu ai ba zata ce ma mijin yar yaje yayi wani aure ba,
"Inna shanaye na sun iso da daddare"
Washe baki ta hau yi"kai abu yayi kyau,anjima kuwa zan saka yara su kaini naje na gani"
Kallon ta yayi yana mamaki hali irin na Uwar su,"ke da kafarki ke ciyo,ko ina baki iya zuwa shine har zaki iya zuwa ganin dabbobi,ko da yake dabbobi ne ai sunfi mutum daraja "
Duk shiru suka yi,domin sun fahimce inda zancen nashi ya dosa,
"Yanzun Dabbobin ka sunkai nawa Dottiya,nasan sunyi Albarka? Baffa sanda ya tambaya dan kawai ya dauke shirun da ɗakin yayi,
" Garke daya ne da guda dari biyu,sai tumakai gudan saba'in"
Duk kallon mamaki Inna da Bube suke mai"amma nan kace min shanayen ka sun wuce garke biyu, bancin tumakai"Cewar Bube kamar a hasale,
"Na dai faɗa ne kawai amma iya abinda nake dasu kenen,ko dai basu yi Albarka bane?ya faɗa fana kallon su shima,dan bai gama fahimtar in da suka dosa ba da wannan tambayar da kuma zafin rai na Bube,
Sanda ne yace" A'a abu yayi Albarka,kai da ka wuce garke daya,babu laifi ai,Allah ya saka masu Albarka,idan munbar nan zamu je mu duba su"
Bai basu amsa ba sai ma tashi da yayi ya bar su a dakin.
A haka dai yaci gaba da lalla rayuwar shi yayin da duk safiya idan an idar da sallah zai kai Jauro wurin Malam liman ya ɗauki karatu zuwa ƙarfe bakwai na safe kafin ya dawo ya tafi Boko,nan ma in ya dawo zuwa ƙarfe hudu yake sake tura shi islamiyan yamma,
Ana cikin haka ne suka wayi gari da tsananin tashin hankali a wannan gidan,wanda shine yayi sanadiyar sauya rayuwar Jauro,ya mai dashi daga sama ya dawo kasa sannan a ƙasan ma ya kife,wato rasuwar Mahaifinshi Dottiya,wanda suka kwanta dashi sai dai basu tashi dashi ba,
Mutuwar ta shiga mutanen gidan sosai har balle tsohuwa Inna Mari,wacce rabon da amata rasuwa tayi kuka irin haka tun mutuwar mijinta,
Sunyi Jimami na tsayin kwana uku kafin su wassake,
Allah sarki Jauro,duk da yana yaro yanda yayi kuka a mutuwar mahaifinsa bai yi a lokacin daya rasa mahaifiyar sa ba,domin kuwa a lokacin mahaifinsa ne ke dauke masa kewar Innar sa,baya bari yayi kuka rashinta,
Yanzun kuwa yana wurin ƴan uwan mamarshi ne da suka zo gaisuwa,
Randa aka gama sadakan uku kuma da zasu koma suka roƙi Inna Mari Alfarma ko zata basu dama suna son su tafi da Jauro ya zauna a wurin su,
Har fa matar nan ta amince,sai ga Baffa Bube ya shigo a jigace har yana kumfar baki,kan cewa me yasa za'a basu Jauro su wuce dashi,ai suma suna da halin da zasu iya riƙe shi,kuma shi zasu dinga gani suna tuna ɗan uwansu,dan haka su tafi kawai shi zai rike Jauro a hannun shi,
Babu kalan rokon da basu mashi ba amma ya rufe ido yaƙi,karshe ma sai bin bayan shi Inna Mari tayi,
Wannan abun yaba ƴan Uwan mahaifiyar sa haushi,akan irin maganganun da Bube ya masu,wanda yaja suka yi fishi tare da Alkawarin basu kara tako ƙafar su inda suke,sai dai in Allah ya raya Jauro da kanshi zai zo ya nime su ta yanda basu isa su hana shi zuwa ba,
Da wannan bacin ran suka wuce,domin dama su burinsu su dauki ɗan ƴar uwarsu su riƙe saboda sun san irin zaman da ake yi a wannan gidan,
To sai gashi abin bai yuba,sai dai kawai su bishi da Addu'ar Allah ya raya shi,ya bashi haƙuri da juriyan zama a cikin waɗannan mutanen,wannan kenan.
Bayan wucewar su ne Inna ta kalle shi "to yanzun kai Bube ka nada in da zaka ajiye yaronnan daka hana a tafi dashi,ka dai san halin matar ka da bakin hali,"
"To Inna ba sai ya dinga kwana a dakin su Ɗan Fodiyo ba,ai yaron da wayonshi tunda ba kashi zata dinga wanke mai ba,abinci kuma wanda kowa yaci haka zai ci,to me aciki,kenan baki gane me mutanin nan suke nufi ba,so suke yanzun da sun karbe shi zasu ta da fitinar a raba gado a basu nashi su tafi dashi gaba ɗaya,shi yasa na hana"
Kallon shi tsohuwar keyi"to nikan in haka ne me zai hana a kira Malam liman a gobe yazo ya raba gadon nan kowa ya huta,"
Turbune fuska yayi "A'a ba sai an ƙirashi ba,ki bari ni zan kira malami na zai zo ya raba da kanshi,ko a cikin gari ba karamin babban malami bane"
"To shikenan hakan ma zai fi,yanzun dai sai ka faɗa ma ɗan'uwan ka,saboda yasan abinda ake ciki"
Haka kuwa aka yi,a ranar su da basu magana da juna sai gashi saboda abin duniya suka shirya,
Washegari da kansu suka je suka dauko wannan malamin a cikin gari,
A dakin Inna aka zauna za'ayi rabon,bayan sun je sun kirga dabbobin,wanda suke garke daya da guda Dari biyu,
Sai tumakai guda saba'in,
Kaso na farko da aka fara yi,shine Baffa Bube aka bashi shanaye guda dari huɗu,shima Sanda aka bashi Dari huɗu,ya rage dari huɗu,shi ma aka bama Jauro dari biyu,Inna Mari guda Dari,sauran ɗari,aka ba Goggo Badejo guda talatin,sai Goggo Halira ita ma guda talatin,ya rage guda Arba'in,Malam mai rabon gado ya ɗauki guda goma sha-biyar,ya rage ishirin da biyar,aka ba Inna Kande guda Goma,Inna Binta ma goma,ya rage biyar,aka ba Yabale guda ɗaya,Dotti ɗaya,yaran Baffa Sanda kenan,sai Ɗan Fodiyo daya,Bakari daya,yaran Baffa Bube,
Ɗayan daya rage kuwa za'a sai da a raba kudin kowa a bashi,
Tumakaima irin rabon da aka masu kenan wanda a ƙarshe Jauro ya tashi da guda goma.