← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 49

Sashe 13

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya ya kuma yi"ai ina jin yaren ka sosai tunda mahaifina Bahaushe ne,kaga taho mu shiga mota,ma karasa hiran a gida"
Shi ya buɗe mashi gidan gaba ya shiga kafin ya maida kofar ya kulle sannan ya zagaya ya shiga mazaunin Direba ya ja muto,
Shi dai kalle_kallen shi kawai yake yana baza ido yana kallen mutane masu wucewa,har suka isa wata unguwa mai kyau wanda tsarin gerin gidajen ma abin kallo ne,
Har dakin daya tana da domin shi ya kaishi,tare da nuna mashi banɗaki da wurin wanka sannan ya fito"kayi wanka ka canja kaya sai kazo mu ci abinci"

Amsa mashi yayi yana komawa banɗakin,dan ba karamin kashi yake ji ba tun cikin jirgi,

To fa,tsayawa yayi yana karewa lafiyayyen bayin kallo,tare da shiga duniyar nazari,
Dube_dube ya fara yi ko ta ina zai ga in da ake tsugunnawa,dan bayin a share yake tas,har wani kyalli yake,ko ina fari kamar daki,
Idanun shi ne suka sauka akan wani dan net na roba,wanda idan ruwa ya zube a kasa yake bi ta wurin ya wuce,idan kuma datti yayi yawa a wurin ruwa baya wucewa,sai an cire roban an wanke,
Dan haka ganin kaman dan rami ne a wurin yasa ya saka hannu ya cire roban yana leken ramin"kai gaskiya matsugunnin nan yayi karami,"ya faɗa yana kyara saitin tsugunnin shi a wurin, cikin kwanciyar hankali ya gama juye abinda ke cikin shi a wurin,
Sai da ya kammala sannan ya dauki butan daya ciki da ruwa dama ya tsarkake jikin shi,

Sauran ruwan da yayi tsarki da shine ya shiga juyewa a wurin,sai dai gani yayi abu ko motsi bai yi ba,
"To shi kuma ta yaya zan saka ya wuce ce" Da sauri kuma ya juya tare da daukar bokitin wanka ya kunna panpo,sai da ya cika da ruwa ya jawo ya juye a wirin,sai dai a maimakon yaga ya wuce,sai gani yayi yama kara tasowa sama,bai da alamun sauka,
Kara cika wani bokitin yayi ya juye,nan ma shiru babu labarin wucewar kashi,
Shiru yayi tare da Daura hannayen shi duka biyu saman Kwankwaso yana tunanin ta yaya zai saka wannan kashin ya wuce ta ɗan wannan kwararon....

*Fans sai ku ba Jauro shawara*

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*18*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Shikam yasan ba shida zaɓi daya wuce yaje ya nasar da ɗan Alhaji ya zo ya taimaka mashi su saka wannan najasar wucewa,dan haka fitowa yayi daga cikin daki ya shiga ƙwanƙwasa mashi kofar dakin shi,

Fitowa yayi "lafiya Jauro,kana buƙatar wani abu ne?

" Ɗan Alhaji nayi bahaya kuma yaki tafiya sai yawo yake saman ruwa"

"To muje na nuna maka yanda zaka yi"
Bin bayan shi yayi suka shiga cikin dakin shi,tun daga shiga ban ɗakin wari ya fara busu shi,yana buɗe bayin ya dawo baya da sauri yana dariya tare da jawo kofar,

"Ai Jauro yaushe aka ce maka anan ake bahayar,"

"To yanzun ya zan yi ɗan Alhaji?dan shi sam tunanin shi bai bashi cewa akwai wani abu a bayin ba wanda zai iya tsugunnawa a kai ba,dan shi kam tunda yake a rayuwar shi bai taba ganin ban ɗaki haka ba.

" Zo muje bandaki na na nuna maka yanda zaka gyara naka"

Bin bayan shi yayi suka koma nashi dakin har banɗaki,nan ya shiga nuna mai asalin inda ake kashi da yanda ake kora ruwa ya wuce da yanda zai wanke bandakin da kuma yanda zai yi amfani da kayan wankewar dake jere acikin bayin har da ma na wanka,"yanzun kaje ka duba bayan ƙofar ka zaka ga abin shara da kuma abin kwashewa sai ka yi amfani dasu ka kyara bayin idan ka gama sai ka yi wanka"

"To na gode Ɗan Alhaji"
Fita yayi daga ɗakin ya koma nashi,yanda ya nuna mashi kuwa haka yayi,sosai ya wanke bayin ya kuma buɗe window bayan,yana kammalawa yayi wanka sannan ya canja kaya,

A washegari da taimakon Ɗan Alhaji ya kammala komai na makarantar,sannan suka bashi umurnin fara daukar darasi a kowani lokacin a kuma bangaren daya zaɓa wato Pharmacy,
Ba karamin farin ciki yayi ba,
Sosai ya mai da hankalin shi akan karatun shi,da yake shi din mutum ne me ƙwaƙwalwa yasa komai yake zuwa mashi da sauƙi,
Sai dai ta bangaren abinci wanda da farko ya so ya ɗan samu matsala saboda yawan ciye-ciye wanda yake jawo mashi zawo,sai da Ɗan Alhaji yayi da gaske kafin ya fara sassauta ma cikin shi,
Rayuwar shi a wannan kasar ba karamin daɗi yake mai ba,domin babu abinda yake Missing daga gida ko mutanen gida,
Sai dai lokaci-lokaci suna gaisawa da Alhaji Abubakar,
Sai da yayi wata biyu kafin dan dole Ɗan Alhaji ya saka ya siya waya,wanda sai da kyar sannan ya iya sanin ma yanda ake amfani da ita,dan ko da ma idan sunyi waya da Alhaji Abubakar bai san ma ta yanda zai kashe kira ba,
Da wannan sabuwar wayar ne yasa Alhaji Abubakar ya turo mashi number Moha,suka yi Vedio call harda ma Malam Liman,
Da Moha ya buƙace ko ya kaima ƴan gidansu su gaisa ne,sai cewa yayi a'a ya bar su,dan yasan ko an kai masu ba abin arziƙi zasu faɗa mashi ba,to aciki wama zai ce aba.

A hankali rayuwar shi ke tafiya a wannan ƙasar cikin nasara yayin da kwanaki ke tafiya zuwa shekaru,yana aji uku ne ɗan Alhaji ya kammala nashi karatun ya dawo gida,wanda da kyar suka rabu a wannan ranar dan ba karamin shakuwa suka yi ba,

Dama kuma tun ɗan Alhaji na nan suke kasuwanci wanda suke turo kaya Nijeriya ana sai da masu,kuma yana aiki a wani babban shago wanda ake biyan shi,

Da wannan kuɗin ne ya biya ma kanshi kudin shiga wata makaranta a England in da anan ya zaɓa domin yin master's degree din shi,
Kuma Alhaji Abubakar bai hana shi ba ɗan ba karamin Alfahari yake da yaron ba,ya dauke shi tamkar ɗan shi,

Rayuwar shi a England ne ya so ya sauya,
Haduwar shi da wata yarinya mai suna Jesica,ita ta fara buɗe mai ido da kananun romance,wanda daga baya idanun shi suka buɗe,
Sai dai in da Allah ya taimaka shine bai taɓa zina ba,duk yanda yakai ga romancing mace sai dai a tsaya anan,
Yayi ƴan mata kala-kala wan da shi kanshi bai sai iyakarsu ba,
Jauro mutum ne mai matukar wayau sosai,wanda duk wayou mace bata isa ta ci kuɗin shi ba,duk wani karairaya da zata mai,sai dai yace wani dare ne jemage bai gani ba,sai kuma idan shi yayi niyar baki,

Ko da ya kammala karatun shi a England bai dawo gida ba,wata makarantar ya nima a Saudiya wacce ita wannan ta islamiya ce kuma karatun shekara biyu ne,hakan yasa ya karɓi aikin makarantar su ta dauke shi a England din,sai dai zai masu aiki ne a Branch din su dake Saudiyya,
Zaman shi Saudiya yasa ya kara samun ilimin addini sosai,tare da shiriya,ya zama wani ustadz dashi,
Duk tsayin shekarun da ya kwashe yana yawo a kasashe bai wuce a cikin wata huɗu yayi waya da su Baffa sau biyu ba,
Amma Malam Liman kuwa har yasa an rushe gidan ahi an yi mai ginin zamani ba tare da ya bari mutanen gidansu sun sani ba,haka ma Moha yayi aure tun tuni domin har yana da ƴa,ba karamin Alkhairi yake samu a hannun Jauro ba ban bai manta dasu ba.

Wasa_wasa sai da Jauro ya share shakara takwas a kasar waje,hudu a China biyu a England,biyu a Saudiyya,
Ya tafi yana da shakara goma sha bakwai ya dawo yana da shekara ishirin da biyar,

Ko da zai dawo sai da ya fara bin jirgin da zai sauka Dubai daga nan ya hau na Ethiopia,sai kuma wanda zai sauka a Abuja,sai da yayi kwana biyu a Abuja kafin ya shigo Minna domin a kwai wasu takardun da yayi Submitting,
Ba karamin murna Alhaji Abubakar Imam yayi ba da ganin yanda yaron ya kara jirma da wayau,duk da lokaci lokaci yana kai mai ziyara,
Sai dai kusan ta ɓangaren saka kaya babu abinda ya canja dan gane dashi,
Baya son cire kuɗi ya siya kaya masu kyau na fitar raini ya saka,ya fi gane ya ta saka kaya kamar wanda ba shida shi,Alhalin kuɗin dake cikin asusun bankin shi Allah kaɗai yasan yawan su,
Ko da zai shiga ruga bai je masu da wani kayan karya irin na azo a gani ba,dan wallahi yasan halin mutanen su,
Tunda yana jin labarin komai a bakin wadanda yake waya dasu,

Yayan Baffannin shi duk sun girma sun zama samari manya dasu,dan Yabbale da ɗan Fodiyo tuni sunyi aure har da yara,
Amma sai dai abin mamaki babu abin daya canja dangane da zaman mutanen gidan,sai karo wulakanci da suka yi,
Dan yanzun Ya'yan Baffa Sanda basu isa su bi ta gonar Baffa Bube ba su wuce,kamar yanda shima ya'yan shi basu isa subi ta cikin gonaki Baffa Sanda ba.

Inna Mari tsufa ya ƙara kamata sosai,sai dai in da Allah ya taimaka kunsan jikin Fulani da kyau,tunda yawanci da danyen madara suke fara karin safe,

Basu wani damu da dawowar shi ba sai ma cewa da suke wai ya gaji da yawon duniyar da ya tafi ya dawo,
Su Moha ne da ƴan gidan su Malam Liman kawai suka yi farin cikin ganin shi,wanda Malam Liman harda hawayen daɗi,

Kwanan shi biyu da dawowa ya samu kira daga Abuja wanda yasa dole ya tattara yatafi,
In da ya samu labari mai daɗi,a kan ya samu aiki a wani babban general Hospital na Gwagwalada,sun bashi babban matsayi a Lab din,
Chapter 13 · 0% Book details