← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 49

Sashe 41

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kallo ya bita yana jinjina ma rigima irin nata,to yanzun in banda ita me abun kuka anan,
Ba yanda ya iya bin bayan ta yayi,

Har ya doshi dakin sai kuma ya dawo baya jin shesshekar kuka daga cikin falon,
Tsayawa yayi a tsakiyar falon yana kalle_kallen ta inda zai ganta,dan shi dai sautin ta kawai yake ji amma bai ganta ba,
A hankali ya fara bin ta inda sautin ke fitowa,a tsakan kayan kallo da show Glass ya ganta zaune ta haɗe kai da gwuiwa,
Tsayawa yayi ya rike Kwankwaso kafin ya tsugunna a gabanta,"Sumy Baby"

Kin amsawa tayi ta juya gefe tana ƙara sautin kukan ta,

"Why ar you crying?
Nan ba kin kula shi tayi,
" Ok faɗa min me kike so"

Ba tare data dago ba tace"ni ka ƙyale ni,tunda baka dauke ni da muhinmaci ba,i am trying to be nice to you, amma kai baka so"

"Duk duniya babu macen da nake bata muhimmanci irin ki,and I know that you are trying to be nice,and I appreciate it"

Katse shi tayi"to ni ban gani ba,in da ina da muhimmanci ai dana tambaye ka da ka faɗa min a binda ke damun ka in a nice way,but you confounded me"

"Kiyi haƙuri bai kamata ba,bana son na saka ki cikin damuwa ne"

Dago fuska tayi tana kallon shi"do you love me?

Tambayar ma nata wanna karon dariya ya bashi,sai dai a maimakon yayi dariyar sai ya saki murmushi,
"I always do love you,and I will always be loving you for the rest of my life"

Haka kawai kuma sai ta tsinta kanta da sakin murmushi,ganin yana kallon ta ne yasa ta saisaita kanta,sannan ta tace "to ni ka tambaye ni"

"Me zan tambaye ki?

" Ko ni ma ina sonka,and if I can continue living with you?

Girgiza kai yayi "A'a ba sai na tambaye ki ba"

Zaro ido tayi"saboda me?

"Saboda nasan amsar"

Nan da nan ta bata fuska tana shirin saka wata rigimar "Jauro but this is not fear,ni fa na fara tambayarka amma ni shine ba zaka tambaye ni ba,is not fear"

"To naji tsaya,bari na tambaye ki,do you Love me?ya fada yana kure ta da kallo.

Murmushi ta sake tana kyara zamanta,daga tsugunnen da yake ta jawo hannun shi " Zauna kar kafanka yayi tsami "
Zama yayi yana tankwashe kafa,tare da ƙara maimaita mata tambayar "do you Love me"

Girgiza kai tayi"A'a,i do not love you,"
Ganin yanda yayi shiru ya zuba mata ido ne yasa tace"I just tell you what is in my mind,but don't worry i can live with you forever,but if you continue to be good,and maybe some day i will love you"

Murmushi ya sake saki tunda ta fara magana,

"Are we good?ta faɗa

"Yes"

"Ok to faɗa min dazu tunanin me kake yi"

Hannun ta ya saka cikin nashi,ya sumbata "ina tunanin iyaye na ne,dazu in da ace suna raye da muka ji gida,da a dakin ta zaki sauka,babu wanda zata bari ko da harara ya maki,iyaye mutane ne masu muhimmanci wanda da yawa basu sanin haka sai sun rasa su,naso ace na rayu da nawa iyayen,da wallahi sun ga gatan da basu taba tsammani ba,gashi dai yanzun ina da duk wani abinda dan adam ke buƙata a rayuwar shi,sai dai ba ni da wanda zai saka min Albarka,that's very very painful,dan haka ki kyautata ma iyayen ki lokacin da kike da damar haka,ma'ana lokacin da kuke tare,ba sai lokaci ya kure ba,how I wish zan iya ganin su,nayi rayuwa dasu ko da na kwana daya ne, da n.....

Rungume shi tayi a jikinta tana shafa bayan shi,"is ok,na san kasan Allah baya barin wani dan jin daɗin wani,in da kuwa yana yi,da bai raba tsakanin uwa da ɗa ba,da bai raba masoya ba,shi Allah mai yin duk yanda yaso ne,a kuma sanda ya so,Kuma ko yanzun lokaci bai kure ba,kama da damar da zaka masu babban kyauta wanda suna can amma kuma suna maka Addu'a,suna mai Alfahari da kai da abinda ka mallaka "

Dagowa yayi yana ƙara rike hannun ta"faɗa min,me zan yi,me zan yi da zan saka masu farin ciki"

"Ka sani mana,ga ba Sadakatu Jariya ba,sadaka mai gudana,misali gina rijiyoyi in da ake matsalar ruwa,gina masallaci a inda ake da buƙatar haka,misali cikin ƙauyuka za'a bincika,ko kuma kananun unguwanni,ga kuma Islamiya,duk kana ina yi da niyar duk wani abin Alkhairi da aka gudanar Allah ya kai lada gare su"

Rungume ta yayi sosai,
Jin matsar yayi yawa yasa ta saka ihu tana fadin ya sake ta,

Dariya ya fara"na gode sosai Sumy,nasan da haka amma kuma wannan tunanin bai taba zuwarmin ba,na gode Allah ya maki Albarka "

"Amin" Ta faɗa tana mikewa,"yau me za'a dafa "

"Kaji gulma dama kina tambayata me zaki dafa ne?

Turo baki tayi,kafin tayi magana yayi saurin faɗin" Kin ga mai da fushin yau ni zan mana girki da kaima"

"La da gaske,dama ka ita girki ne?

" Uhmm,yau zaki ci girkin maza,"

"To me zaka dafa mana"

"Chinese food"

"A'a ni dai bana so,ba dai wanda suke saka Tana da tsutsa ba" Zaro ido tayi tana rufe baki da tafin hannun ta"ba dai kana cin tsutsaba,and you Kiss me"

Dan shiru yayi kamar me tunani "to wani lokacin dai na kan dan ci kaɗan"

"Tsutsan,?

" Ummm"

Da gudu ta buɗe bandakin da ke falon ta shiga kakarin amai,

Dariya yake,domin duk daukan shi wasa take,sai dai kan ya Ankara har ta fara sheka amai,
Da sauri ya bita bandakin,ya shiga shafa bayanta "wasa fa nake maki,ban taba ci ba,ni fa a England nayi karatu ba a China ba,"

To abu ne ya zo ba control dan haka sai da tayi Amai sosai,

Shi ya taimaka mata ta dawo falo ta zauna tana sauke numfashi,
Gabaɗaya duk ya shiga damuwa,dan bai ɗauka abin zai yi serious haka ba,
"Kiyi haƙuri sumy duk ni naja maki"

"Is ok,amma dai kar ka ƙaramin irin haka bana so"

"I promise ba zan ƙara ba"

Mikewa tayi "muje na ga yanda zaka yi girkin"

Murmushi yayi yana rike hannun ta,"ai kuwa zaki gani".....
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*50*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Kicin suka shiga,jawo mata kujera yayi yace ta zauna,
Kallon shi kawai take tana jira taga yanda zai yi,kila ma ko gas bai iya kunnawa ba,
Gani tayi ya buɗe kwandon da suke ajiye Albasa ya dauko babba guda ɗaya,sai kayan miya Fresh su koren tattasai da mai kalam green da ruwan ƙwai,sai Attarugu da green beans da carrot,ya hada a karamin kwando ta wanke sosai ya cire dattin da kuma ya'yan ciki,
Daga tsayen da yake ya cikin kwarewa ya yayyanka su kanana,ko wanne ya ajiye a gefe,sannan ya daura madaidaicin tukunya a kan gas ya tsiyaya man gyaɗa dai dai wanda zai isa,kafin yayi zafi taga ya buɗe ledan taliya guda daya ya raba biyu ya mai da rabi inda suke ajiyewa,wanda zai yi amfani dashi kuma ya kakkarya gida huɗu,suba kanana ba su ba manya ba,
Albasa kaɗan yasa a man sai tafarnuwa karamin ɗaya,suna soyuwa ya kwashe ya zuba a karamin pleat,

Mikewa tsaye tayi da sauri tayi in da yake tsaye,ganin amaimakon ya zuba yankakken kayan miya amai ya soya ta shine ya zuba taliya amai yana soyawa,
"Jauro me haka kake yi,ba a soya taliya,kayan miyan can zaka zuba"

Juyowa yayi ya kalle ta yana ci gaba da juya taliyar,"ke dai kawai ki zauna ki jira,idan har baiyi dadi ba nayi Alkawarin kai ki gidan abinci ki ci duk wanda kike so"

"Amma k... "

Maida ita yayi ya zaunar inda ta tashi "ki yarda da ni,zauna"
Ba yanda ta iya komawa tayi ta zauna tana jiran taga ikon Allah,soya taliya,bari dai taga iya gudun ruwan shi,

Tana kallo har saida taliyan ya soyu kamas,sannan ya kwashe a kwani kwando,ya sauke tukunyar ya rage man,sannan ya kawo green beans ya soya na ɗan wani lokaci tare da yanke yanken da yayi,ya kwashe da ban,sannan ya kara zuba ruwa madaidaici ya rube,
Firig ya buɗe ya dauko naman Kazan dake dungule a leda ya wanke ya yanka kanana sosai,sannan ya zuba a tukunyar tare da kayan kamshi da magi,minti goma ya buɗe ya zuba wannan soyayyen taliyar ya juya sosai,ya rufe,sai da ya kusa tsotsewa sannan ya kawo kayan miyan daya tsoya ya juye aciki ya kara juyewa,

Tuni ta fara hadiye miyau jin yanda wani irin kanshi ke dukan hancinta,sai dai haushin ta daya idan ta duba tukunyar da kuma yawan taliyar sai taga ita kanta ko duka aka juye mata ba lallai bane ta koshi,balle su har rai uku,

Tana kallo ya rage wuta sosai,
Sannan ya kwashi kayan da yayi amfani dasu ya wanke tas ya kife,
Zuwa lokacin girkin ya gama tsotsewa ya sauke, wasu pleat din ya dauko ya raba abincin kashi uku ta zuba ma kowa sannan ya saka a babba tire ya kai falo ya dawo ya dauki lemun kali babba guda daya da cup sai cokali,
"Ranki ya daɗe muje ko"

Tashi tayi tabi bayan shi,"bari na kira Aisha"
"Ok"
Ba jimawa sai gashi sun dawo tare,
Zama suka yi suka yi Bismillah,diba tayi a cokali takai baki,
Kallo ta yake,yana jira yaga Reaction din ta,

Lumshe ido tayi ta bude tana lasan lip dinta,murmushi ta saki"duk da ƙanshin mai matukar jan hankali ne,kamar yanda kyanshi ke da daukar hankali saboda yanda ka tsara,ban ɗauka daɗin zai kai haka ba,gaskiya yayi daɗi sosai,na kuma yaba "

Bai bata amsa ba sai murmushin dake fita daga fuskar shi,
Chapter 41 · 0% Book details