← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 49

Sashe 27

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan murmushi ta sake kaɗan tana kara wani marairaicewa "dan Allah in za'a kawo abinci a kawo min mai nauyi kaji"

"Da kika yi sallah kin gaishe ni?

Ɗan zaro ido tayi" Lah,ai naga kana sallah ne shi yasa,"

"To dana fito fa?

Turo baki tayi amma data tuna abinda take son roƙon shi tuni ta mai da bakin" Ai dama yanzun zan gaishe ka,shine ka tare numfashi na"saukowa tayi ta tsugunna katsa,"Ina kwana ranka ya daɗe?

Gani tayi cikin sauri har yana zabura ya daga kafarshi dake a kasa ya hade da kirjin shi ya takure yana kallon ta a tsorace "Sumi?

" Na'am yallabai "

"Ba dai shirin kashe ni kike yi ba ko?

Dago kai tayi tana mai kallon rashin fahimta, shi kuma yana mata kallon zargi da tsoro,

"I know dos days is very easily to young lady like you to kill her husband shi yasa nake tambayar ki,what are you planning?me yasa da zaki gaishe ni kika tsugunna har da kirana yallabai?

Bude baki tayi galala tana kallon shi,can kuma sai ta sheke da wata dariyar tana nuna shi" Wai dama Fulani na tsoron mutuwa,i can believe it,Jauro,"

Ƙara matsawa yayi"mata abin tsoro ne"

"Kaga nifa dama so nake na tambaye ka akan ka ara min wayar ka na kira Mama,sai kuma ka mai da ni gidan da zan zauna in da zan rinka ganin mutane"

Shiru yayi kamar ba zai yarda da abinda ta faɗa ba,sai kuma ya saukar da kafa yana kyara zama,tare da miko mata wayar bayan ya cire key,

Murmushi tayi tana amsa,

"Amma dai daga yau karki ƙara kirana da yallabai,kuma in zaki gaishe ni karki ƙara tsugunnawa har sai ranar dana yarda daki"

"Kana nufin baka yarda da ni bane? Ta fada tana saka number Mama.

Bai bata amsa ba ya mai da hankalin shi kan TV.

Sai da tayi kira kusan sau hudu sannan aka ɗauka,ta san halin Mama tana iya ajiye wayar ma ta manta in da ta ajiye,
Lokacin da taji muryar Mama tana fadin Assalamu alaimun har wani ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe ido tamkar wacce ke gabanta haka take ji,

Jin ta kara yin sallamah ne yasa ta amsa tana kiran sunan ta"Mama na"

Daga inda take zaune tana iya jiyo yanda Mama ta zabura tana kiran Sunan ta"Sumayya,Sumayya ce!

Ji tayi kwalla ya ɗan taru mata a ido "ni ce Mama"

"Alhamdulillah Allah na gode maka,Sumayya kina ina,ina kuka je tun jiya an je gidan ku babu kowa gidan a kulle hankali na ya tashi Sumayya,ko dai ya maida ke ƙauyen su ne?

Dago kai tayi ta kalleshi,suna haɗa ido ya dauke kanshi,

" A'a Mama muna Matasa Hotel tare dashi, "
Dafe kirji tayi"na shiga uku Sumayya Hotel kuma,da auren ku,me zai kai ku in da ake ɗiban Albarka,ina shi Jauro yake"

Jin hankali ta ya tashi jin kalmar Hotel kawai da tayi yasa da sauri tace"Mama ba da wani abu bane,kawai dai ya kama mana daki ne a nan saboda yace katifar na zarnin fitsari ba zai iya kwanciya a kai ba shi yasa,amma ba wani abu bane,kuma yau ma zamu koma "

"Kin tabbata dai ko?

Murmushi tayi" Eh Mama,ina su Aisha?

"Ta tafi makaranta,kin yi waya da yayarki ne,domin ita ma hankali ta ya tashi"

"A'a amma yanzun zan kira ta"

"To ku dai yi ku baro Hotel ɗin nan domin bana son zaman ku a nan,dan kar Allah ya zo saukar da matsifa ya shafe ku"

"To Mama" Ta faɗa tana murmushi,daga nan sukayi sallamah,wanda yayi dai-dai da Kwankwasa kofar da akayi ya bada izinin shigowa,

Wannan karon ba matar jiya ɓace,cewa yayi ta kawo abincin nan a maimakon wurin cin abinci da zata kai,
Jera masu shi tayi a nan gabansu ta wuce,

Kallon plate din take tana kallon shi,da Aunty Amina zata kira,amma sai ajiye wayar ta yi "ina nawa abincin?

Kyara zaman shi yayi a kasa yana mata nuni da hannu,alamun gashi,

Nan take ta haɗe fuska " Amma na ce maka ni ba zan ci wannan jagwagwalon ba,"ta faɗa tana nuna soyayyen ƙwai da ruwan liptom da ke cikin ƙaramin kofi wanda ko madara babu haka kuma babu Biredi.

Ɗaukar cup daya yayi ya shiga kurba,"ai kin riga kin ci kudin karin safen ki tun safiyar jiya,in zaki ci wannan kaci,in kuma ba zaki kici ba is fine "

Yunwa take ji,ta yaya za'ayi wannan dan abun ya ishe ta,"ni ba zan ci ba"ta faɗa tana kauda kai,yayin da idon ta ke tara hawaye.

Bai kulata ba har ya kammala cin abinci shi,sannan ya dauki wayar shi data ajiye gefe,
"Zan iya maki taimako ɗaya" Ya faɗa yana tsayawa a kanta,

Share hawayenta ta shiga yi bata kula shi ba

"In dai har zaki je motsa jiki zan iya maki ordan duk abinda kike so"

"Ba naso,ba zan ci ba kuma ba zan je ba,mugu kawai"

"Oh tunda haka kika ce,to ai shike nan" Ya faɗa yana bar mata ɗakin ma gabaɗaya yayi wucewar shi.

Karfin kukanta ta ƙara tana jin ranta na ƙara ɓaci,wannan wani irin abu ne saboda Allah in banda ɗaukar alhaki,
Ta jima tana kuka anan zaune kafin ta ji ana kwankwasa ƙofa,
Kamar bazata tashi ba sai kuma ta Mike da sauri tana addu'ar akan Allah yasa abincin yasa aka kawo mata,

Tana buɗe ƙofar taga wani ɗan matashin saurayi a tsaye rike da madaidaicin akwati,
Cikin girmamawa ya gaida ita,

A takaice ta amsa tana mashi kallon lafiya,daga ina.

Turo mata akwatin yayi"gashi in ji sir Jauro wai a kawo maki ki ajiye mashi"

Amsa tayi ta shiga da Akwatin tana dunguran da shi nan tsakiyar falon cikin jin haushi,

Har ta zauna kuma kome ta tuna sai zuwa tayi da sauri ta buɗe akwatin wanda bata ga komai ba aciki sai kayan sawar shi,irin wanda ke bata haushi,

Ɗaga rigunan tayi tana ajiye wa gefe "in dai takamarka baka son cire kuɗi,idan na sadakar da kayanka ai dole ka saka kudi ka siya wasu" Ta faɗa a fili,

Gabaɗaya kayan ta kwasa cikin jin haushin mai kayan tayi waje da su,
Ta jima a bakin Get kafin ta samu wani Almajiri tsoho ta bashi kyautar kayan duka,
Ai kuwa ba karamin dadi da saka mata Albarka tsohon ya shiga yi ba,
Harda kakkabe hannu tana komawa ciki,

(Allah sarki wata ta taro Fitina ta yi kyauta da kayan Jauro)

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*35*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Komawa tayi ta kwanta tana juye_juye,dan lokaci ana niman ƙarfe sha-biyu na rana ne,
Ganin babu sarki sai Allah ne yasa ta tashi ta jawo kofin shafin da ya gama yin sanyi ta haɗa da wannan kwan ta ci,sannan ta iya tashi ta shiga banɗaki dan ta dauro Alwallah ganin lokacin sallah ya matso,tana cikin sallah ya shigo,
Taji shigowar shi dakin barcin su,sannan tana ji ya koma falo,
Aƙwatin da ya gani a gefe ne ya jawo ya buɗe,
gani yayi babu komai acikin shi,
Mamaki ne ya kamashi,to ina kayan shi da ya saka aka kawo suke,kodai Sule aƙwati kawai ya kawo babu kaya acikin shi,
Zaro wayar shi yayi daga cikin aljihu ya danna kira,
Tambayar kaya naji yana yi,sai kuma naji yayi shiru alamun yana sauraran abinda ake fada,sai kuma ya sauke wayar ya tashi ya koma cikin dakin inda ya same ta a zaune tana saman darduma tana jan carbi wanda da hannu take yi.

Zuwa yayi ya zauna a gabanta ya naɗe ƙafa,
"Ina kaya na da ke cikin akwati da aka kawo?

Ji tayi gabanta ya faɗi amma sai ta daure ta kauda kai kamar abin bai dame ta ba,
Saida ta karasa tayi addu'a ta shafa sannan ta kalle shi tace" Wasu kaya kenan ?

Nuni ya mata da falo "na cikin Akwati da aka kawo"

"Ohh waɗannan tsunmokaran?

Cikin jin haushin rainin wayonta yace" Kayan nawa ne tsunmokarai? Ya fada yana nuna kanshi,

Waro ido waje tayi tana dafe kirji "kardai ka camin waɗannan kayan masu kyau ne?"Oh My God,ni da ya kawo min akwatin na duba sai gani nayi kayan sun min kama da tsumma dan haka na kwashe na ba Almajiri "

Wannan karon shi kanshi zaro idon yayi cikin tsananin mamakin ta,because he can't believe cewa ta mai kyauta da kaya masu tsada haka,"kina nufin kayan nawa kika yi kyauta dashi?

Turo baki tayi"Sorry ai ni ban dauka masu kyau bane shi yasa"

Lumshe ido yayi yana sake wani nauyayyan ajiyar zuciya tare da busa iska ta bakin shi,
"Kin min kyauta da kaya? Ya ƙara tambayar ta dan ya tabbatar,

Kauda kai tayi sai kuma ta juyo" Yauwa ka mai da ni gida kaga daga nan sai ka dauko wasu kayan naka,kaga ni ma nan ba wasu kaya ne dani ba sai kala biyun daka siyo gashi hijabi ma daya ne"

Bai kula ta ba sai ma mikewa tsaye da yayi yana mata kallon ƙasa_ƙasa ya juya ya zai fita,
Har yakai tsakiyar dakin sai kuma ya juyo murmushi dauke a fuskar shi yace"karki damu,anjima zamu koma gida,dan ni ma nan din ya ishe ni"ya faɗa yana juyawa tare da barin ɗakin.

Shiru tayi tabi bayan shi da kallo,to me yake nufi,ko dai ya shirya mata wani abin ne,da dai taga kamar zai dau zafi,sai kuma taga ya share,
Karamin tsaki taja,a fili tace,ai in ba haka na maka ba da ba zaka yi tunanin mai da ni gida ba"
Wata zuciya ne yace mata to idan ya shirya maki wani abin fa,
Chapter 27 · 0% Book details