← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 49

Sashe 22

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zamu gani" Ya faɗa yana mikewa tare da faɗawa kan katifa,
"Ummm umm"ya faɗa yana mikewa da sauri daga kan katifar da ya hau,

" Sumi me ke wari haka"ya fada yana nuna mata katifar,

Kin bashi amsa tayi wanda ganin hakan ne yasa ya yaye zanin gadon gabaɗaya ya tsaya yana kare ma katifar kallo,
Dafe ƙwanƙwaso yayi yana jinjina kai,
"Sumi bazan iya kwanciya akan wannan abun ba,ke ma sai dai kiyi haƙuri dan ba zan bari ki kwanta a ƙazanta ba,this is bad" Ɗaukar katifar yayi ya fitar dashi falo ya jingine,sannan ya dauko babban tabarma ya shimfida tare da shimfida zamin gadon a sama,kallon wurin yayi yana bata fuska "kai ina,gaskiya ba zan iya kwana a kasa ba Sumi" Ya fada yana kallon ta,

Ganin ba tada niyar bashi amsa ne yasa ya ciro wayar shi dake Aljihu yana danne danne ya fita,

Ajiyar zuciya ta sauke tana addu'ar Allah ya sa ya bar gidan ne,sai dai ko mintinu biyar ba'a yi sai gashi ya kuma shigowa,
"Sumi kici wannan kazar mana,gashi tana hucewa"

"Bazanci ba"

Wannan karon babu Alamar wasa a fuskar shi yace"ba dan ni na siya ba kuma ba dan ki ci ki baya ba na siyo,domin ni ba na cin naman kaza,kuma ba zan yi asaran kudi na ba,idan kuma har ba ki ci ba to wallahi kinga can"ya nuna mata saman tabarma"to sai ya mana kaɗan ni da ke,na baƙi minti goma"yana gama fadar haka ya juya ya fita.

Tabbas a yanda taga yanayinsa da gaske zai aikata abinda ya faɗa,kallon tabarman tayi,wane ita,haka kurum taurin kai ya ja mata bala'i.
Jawo plate din tayi ta saka hannu a hankali ta fara ci,tun tana ci a hankali har ta buɗe ciki ta ci dayawa dan wanda ta ci yafi rabi,sannan tasha lemun tana jin wani irin sanyi a zuciyar ta,domin abinci ma rahama ne,

Shigowa yayi ya kalle ta ya kalli plate ɗin "tashi muje"

A tsorace tace"ina?

Dafe goshinshi yayi"please Sumi na gaji tashi muje mu nime wurin kwanciya gobe ina da aiki bana son taurin kai I know you know that I will never hurt you"juyawa yayi ya fita yana ɗaukar wayar shi dake kara,taji dai yana faɗin gani nan fitowa.

Mikewa tsaye tayi tana jan tsaki,"to ni kuma ko ina zai kai ni,ko dai yaya ne ta Allah ba taka ba,da wani broking English din shi "ta faɗa tana fitowa,
Ganin baya falo kuma baya tsakar gidan ne yasa ta fito kofar gida in da ta ganshi tsaye jikin wani hadadden mota baƙi wanda daga dukkan alama sabuwa ce dal
Yana ganin fitowar ta ya katse kiran da yake yi tare da mai da wayar Aljihu ya buɗe mata gidan gaba tare da faɗin Bismillah"

Kallon shi take tana kallon motar cikin mamaki,wannan kuma motar waye,sannan ina zasu je,
Sai dai babu me bata amsa kuma bata son ta bada kanta ta hanyar tambayar shi,dan kar yaga kamar tsoron shi take,shi yasa a hankali ta tako ta shige yayin da ya maida kofar motar ya rufe,shi kuma ya zagaya ya shiga mazaunin direba tare da tada motar yana mata key,

Sam bata zata cewa shine zai ja motar ba,dan bata da tabbaci akan iyawar shi,cikin tsananin tsoro ta damki hannun shi dake saman giyar motar,tana waro ido tare da fadin.....

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*30*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

"Ba dai kai ne zaka ja motar ba?

Kallon hannun ta dake saman nashi yayi," Baki yarda da mijinki bane?

Da sauri ta jinjina kai alamar eh,

"Kenan kin yarda ni mijinki ne" Ya fada yana sauke hannun shi dake saman key din motar ya daura saman nata ya shiga shafawa a hankali,yana wani tsare ta da ido,

Da sauri ta zame hannun ta daga saman nashi tana sai_saita zamanta"har abada "

Bai bata amsa ba ya kara tada motar ya shiga tukawa a hankali yana kallon yanda ta lumshe ido bakin ta na motsawa a hankali,daga dukkan alamu addu'a take yi,

Sai da ya fita cikin unguwar ya hau saman titi sannan ya shiga sharara gudu da ita kamar zai bar gari,saboda dare ne ba cikowar ababen hawa,
Sai ta ɗan buɗe ido kamar zata mai magana sai ta maida ta rufe dan bata son raini,
Ji tayi ya ce a hankali ya kara rage gudun kafin kuma ya faka motar a wani wuri,

A hankali ta buɗe ido tana kallon in da suke,wani babban Store ne ya tsaya wanda taga an rubuta B.Y

"Kina buƙatar wani abu,na ci ko na sakawa?

Girgiza kai kawai tayi,

" Ok to ina zuwa"ya fada tare da fita daga cikin motar,ya shiga Store ɗin,
Ya kai mintuna goma sha-biyar kafin ya fito wani na binshi da manyan ledoji a hannun,
Buɗe but din motar yayi yaron ya saka kayan a ciki kafin ya rufe,bata san ko nawa ya ba yaron ba,ta dai ga ya ciro kuɗi ya mika mashi, sannan ya shigo motar,

"Sorry Madam Jauro"ya fada yana ta da motar,ta dauka babu nisa,amma sai gani tayi yana ta zura gudu,tun tana kallon hanya har ta gyara kanta ta fara barci dan ba ƙaramin gajiya tayi ba,

Daga Unguwar Tunga inda aka kai ta zuwa Bosso Road ba karamin tafiya ba ne,sai dai ba Bosso yayi da ita ba yankan hanya yayi ta Bahago ya bullu dasu ta Zarumai sai gasu a wani Katafaren Hotel mai suna MATASA,
Hon daya yayi me gadin wurin ya buɗe mashi ya shiga da motar,
Har yayi parking bata sani ba,dan haka fita yayi daga cikin motar ya shigar cikin reception,sai da ya gama komai ya biya kudi ya amsa key sannan ya fito ya dawo in da ya bar ta,
Kashe motar yayi sannan ya zagaya in da take,
Tsayawa tayi a gabanta bayan ya buɗe motar,
Ajiyar zuciya ya sauke yana ƙare fuskarta kallo,Sumayya fara ce sosai irin tas dinnan,sai dai kuma rashin wadata shi ya ɓoye kashi saba'in daga cikin kyan da Allah ya mata,
Murmushi yayi ya saka hannu a hankali ya fito da ita ya mai da ƙofar motar ya rufe da ƙafa,sannan ya fara taku da ita tamkar wanda ya dauko yarinya karama,bawai kuma dun baya jin nauyinta ba,a'a sai dan jikin shi ya saba da aikin wahala kuma yana da juruya shi yasa,dakin su shine na 75,dan haka da yana buɗe ƙofar ya kwantar da ita saman kushin,ya kyara mata kwanciya sannan ya fita,
Ba jimawa kuma ya kara shigowa da waɗannan Ledojin dazu ya ajiye a gefe ya koma ya kulle ƙofa,

Toilet ya shiga yayi wanka,yana fitowa ya ɗauki waɗannan Ledojin ya buɗe,dogon wando da riga mai dogon hannu ya ciro sabo fel a cikin ledan,ya saka,sannan ya fito falo in da take kwance,
Dakin da ya kama babban dakin VIP domin babban falo ne harda kicin a ciki,da kuma dakin barci,babu abinda babu a dakin,

Tsugunwa yayi a gaban ta yana kallon yanda take barci cikin kwanciyar hankali,saboda dazun a asibiti an mata har da Alluran barci,

Yasan taji daɗin barcin nan amma dole ta tashi ta yi wanka sannan ta canja wannan kayan,

Cikin barcin ta mai daɗi aji kamar ana tsotsar mata baki,kara gyara kwanciyar ta tayi ta juya tana fuskantar sama,
Ita bata masan wata damar bane ta bashi,dan haka hayewa yayi samanta ya mata runfa,
Yayin da ya saka harshen shi a ƙarshen labbanta da kuma Gum dinta yana mata tafiyar tsutsa da tsinin harshen shi a wurin,
Jin wani abu na bin ƙwaƙwalwar kanta yana yawo a sassan jikin ta ne yasa tayi wani irin mika tare da mirginawa,ai kuwa sai gasu a ƙasa sun fado yayin da ita ke kwance saman jikin shi,domin dama ba wai ya hau saman jikin ta bane dafa kushin din yayi shi yasa da tayi mika suka faɗo,

Duk da saman jikin shi ta faɗa amma sai da ta danji zafi,dan haka da sauri ta buɗe ido tana kofar tashi,tare da kiran sunan Allah,

Ji tayi an riƙe mata Kwankwaso wanda hakan ne yasa ta kalli kasa,

Zabura tayi da sauri ta Mike tsaye tana waro ido "me kamin?

Mikewa tsaye shima yayi yana dafe baya" Ko dai me kika min,"sai kuma ya saki murmushi yana kallon ta,"na doge Baby Sumi "

Tsoro ya fara bata"dame fa"ta faɗa ita ma tana tsare shi da ido.

"Oh bakisan me kika min yanzun ba?

" Me na maka?

Dan dariya yayi yana kallon ta,"dama bayan mun iso ne naga kin yi barci,to shine na dauko ki na shigo da ke,ni kuma naje nayi wanka na shirya kamar yanda kika gani,ina fitowa falo domin ta da ke kiyi wanka shine fa kawai naga kin tashi kin rungume ni kin shiga kissing dina kina wani shafa ni,

Ihun da tayi ne ya katse shi,"wallahi karya kake min,ni ne na shafa ka har nayi kissing ɗinka,wallahi ba hali na ba ne,ya aka yi to na ganni a saman ka"ta faɗa cikin muryan tashin hankali da kuka,

Shima waro mata matsakaitan idanun shi yayi"to ai ke kika danne ni,ni kuma ina ƙoƙarin tashi,Allah ya so ni so kika yi fa kiyi Repping dina ki min fyaɗe,"

Da gudun ta kara so in da yake tsaye ta shiga dukan shi da hannun ta a kiji tana saka kuka "wallahi karya kake min,sai dai in kai ne kake son kamin fyaɗe,kuma sai na rama sharrin da kamin"

Bai dakatar da ita ba sai ma cewa da yayi "ni ne fa wanda ya kama yace zai rama,har balle kissing dina da kika yi ba tare da kin ni me izini na ba,ina iya yafe ko wanne amma banda wannan"
Chapter 22 · 0% Book details