Sashe 36
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Katseta tayi cikin jin haushi da hasala "na manta baya? Na manta baya da kika ce Aunty Amina,to gaba fa idan na manta bata,ya riga ya cuce rayuwar mu tun daga lokacin daya auri kawar mahaifiyar mu wacce bata san Allah daya bane,a gaban ki kin ga irin wulakanci da tozarci da maifiyarmu ta fuskanta saboda shi! An raba ki da mutumin ƙwarai dake ƙaunar ki,an haɗa ki mugun Azzalumin miji,kullum cikin duka da tsangwama,saboda kawai uwar mu ra haɗiye zuciya ra mutu!to bari kiji in ke kin manta ni ban manta ba,ranar daya buɗe baki a ban mahaifiyar mu yace mata daga ke har Yayanki ba kuda amfani a gare ni,domin in da ace a maza kika haife su da nayi Alfahari da su,amma kin haifamin abinda ba zasu amfana min komai ba,a lokacin da na isa shiga makaranta ki sakani yayi,da kudin sana'ar ta na shiga Boko,har na gama primary zan iya tuna sau nawa ya taɓa ban kudin break,haka ma secondary School,har izuwa NCE din dana yi,a lokacin da nake ganin na na kai matakin da zan iya dafa ma mahaifiyar mu,a wannan lokacin ya ƙara daƙile komai ya aura min mutumin da bai san daga ina yake ba,
Amma da yake Allah ba Azzalumin kowa bane,sai gashi yanda suke fata bai samu ba,ke kalli halin da kike ciki amma amma har kina batun wani a manta baya,to ba da ni ba,"
"Sumaiya a dai rinka yafiya,domin ko Allah yace ina tare da masu haƙuri"
Kallon uku saura kwata tai mata, tare da turo mata wani babban leda "kinga ga leda nan ki kwashe kayan, ku,na Aisha kuma ki barmin su anan,batun Baba kuma ki kyale ni dashi"
"To uwa ta"
Jin sallamah a bakin kofa yasa suka juya tare da amsa mashi,
Sai da suka gashi izinin shigowa sannan ya shiga
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*45*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
"Ƙanina barka da dawowa,"
Murmushi yayi yana ɗaukar Amira dake mai oyoyo "na dawo Auntyn mu," Ya faɗa yana kallon ta yanda tayi dai_daya daga ita sai towel daga dukkan alamu daga wanka ta fito,
Mintsinin ƙafarta ta fara tana mata alama akan ta gaida shi,
"Baby Sumy ya jikin naki?
" Da sauƙi "
"Kin sha magani kuwa?
" Na sha "
Kallon Aunty Amina yayi"Aunty na ku fito na kai ku gida dare na yi,"
"To gamu nan fitowa"
Falo ya koma yana jiran fitowar su,
Ganin ya fita ne yasa ta juyo cikin jin haushi ta kai mata duka"ke wai me yasa ba zaki taɓa yin hankali ba"
Ihu tayi tana shafa wurin"haba mana Aunty Amina,to ni me nayi miki,kike cin zali na"
"Me yasa da Mijinki ya shigo baki gaida shi ba,haba mana Sumaiya,"
Turo baki tayi tana kumbura fuska,"kawai dai haushi na kike ji saboda naki ba Baban ki tsaraba "
"Sumaiya ni fa ba dan haka bane,kawai so nake naga kin san darajan mijinki tamkar ko wace macen kirki,dan Allah ki sauke kanki ki fuskanci rayuwa,yanzun fa kika gama faɗa min ba zaki bani kunya ba,"
"To ni me zan mishi" Ta faɗa a shagwabe,
Dafe kai tayi "ohhh ni Allah na gode maka,wai sumaiya ina amfanin ma littattafan Hausa da kike karantawa,dana Turanci?
" Ai waɗannan littafi ne kawai Aunty,wannan kuma zahiri ne,akwai banbanci,is not easy "
"Na sani,amma ke a tunanin ki me fa'idar karanta littafi?
" Dan nishaɗi "ta faɗa kai tsaye.
Girgiza kai tayi" Kin yi kuskure kuwa da kika dauke shi a haka,"
"Kamar ya? Nifa wani lokaci kona fara karantawa sai na bar shi,wasu sun cika saka maganar banza"
"Haka ne,amma ke ba da maganar banzan zaki yi amfani ba,sai ki dauki na kirki,bari na faɗa maki abinda baki sani ba,yana da kyau kome zaki yi a rayuwar ki ya kasance kina da dalilin yin shi,misali kamar karanta littafin Hausa,yawanci mutane suna ɗaukar shi ne kawai for granted,saboda nishaɗi,amma kuma da zasu duba sakon dake kunshe a cikin littafin zasu amfana dashi sosai,a cikin littafi mutane da yawa ke fuskantar rayuwa,a cikin littafi wasu ke gyara zamantakewar su da mazajen su,a cikin littafi wasu ke sanin yanda zasu kara samun kusanci da Ubangijin su,wasu da iyalansu,wasu kuma suke iya banbance abu mai kyau da mara ƙyau,wannan sabon Allah ne,wannan kuma halak ne wannan kuma Haram ne,na tabbatar da yawancin abubuwan wallahi wasu basu san su ba,sai idan an rubuta shi a littafi sai ki ji mutum yace,ohh dama haka abin yake,ko kuma kiga mutum na cikin matsala ya rasa mafita,amma Albarkacin wannan littafin Hausa cikin sauki ya samar ma kanshi masalaha,shi karanta littafi bawai yana koyarwa bane akan ka ɗauki mugayen ɗabi'un dake ciki bane wadanda ita marubuciya ta rubuta ne domin misali,kawai abin da ake so shine ka dauki abubuwa masu amfani dake ciki wadanda zasu amfanar da kai,kabar marasa amfani,
Masana sun tabbatar da cewa duk wani abinda kwakwalwa zai iya tunani hannu ya rubuta to tabbatar zai iya faruwa kokuma ya faru,,
Misali kamar kiga ace ta faɗa ruwa kaɗa ya haɗiye ta amma bata mutu ba,in ke baki gani ba,to wasu sun gani ya faru a wani garin ko wani ƙasar,
Dan haka ina son kiyi tunani ki samar ma kanki mafita, ta hanyar kula da mijinki da sauke duk wani karya da girman kan dake damun ki,dan Allah sumaiya "
Sauke numfashi tayi "insha Allah"
Dazun ma haka kika ce amma gashi ko wucewa banyi ba kin karyata maganar ki"
"Aunty da gaske nake wannan karon"
Mikewa tsaye tayi tana daukar ledan dake hannun ta,"na gode sosai Allah ya ƙara maku fahimta ke da kanina,"
Bata ce komai ba ta amsa ledar tayi falo dashi,
Girgiza kai kawai tayi tana mata addu'a a zuciyarta,
Har bakin motar da zai kai su dashi ta raka su ita da Aisha sannan suka koma ciki,
Alwalla suka yi sannan suka yi sallah,tana Idarwa ta saka doguwar riga wara nauyi,
Aisha ce tace "Sumaiya muje ki kunna nin kallo"
"Wato dai ke ba zaki daina kirana da Sumayya ba"
Turo baki tayi"to me zan kira ki"
"Aunty Sumayya mana zaki ce"
"Babu daɗi wallahi Sumayya yafi daɗi"
Duka takai mata"kaji shegiyar yarinya,babu kunya ki ce kiran suna na gatsau yafi maki daɗi?
Ihu tasa tana komawa gefe"shi yasa bana son ki nafi son Aunty Amina"
Zaro ido tayi tana nuna kanta"yanzun kinfi son Aunty Amina akai na "
Jinjina kai tayi ,
"Saboda me?
" Saboda kina cin zali na,shi yasa da kika yi aure nake ta jin daɗi "
Salati ta saka"yanzun Aisha in da mutuwa nayi ma haka zaki rinka jin daɗi "
Shiru tayi kawai tana kallon ta,
Cikin jin haushi ta mike tayi kanta zata daka,
Ita ko ganin haka yasa ta mike tayi falo da gudu tana ihun kiran sunan Mama,
Kasancewar ita ma ba nauyi ne da ita ba yasa cikin sauki ta kamo ta,
Ihu ta fara"nafasa kwanan ki mai da ni gidan Mama wacce bata duka na,ba zan yi hutun ba tunda duka na zaki rinka yi"
Jin tace haka ne yasa ta rungume ta maimakon dukan ta da zata yi da"haka mana Aishan Mama,waya faɗa maki dama dukan ki zan yi,kawai dai wasa nake maki,dan na kwada ki"
Make kafaɗa tayi"ni dai na fasa kwana "
"Ke nifa wasa nake maki,kin ga zauna na kunna maki kallo,zaki sha Ice cream?
Jin an ambaci ice cream yasa da sauri ta gyaɗa kai"
Shafa kanta tayi "yauwa Autar Mama," Ta faɗa tana zaunar da ita sanan kushin sannan ta dauko mata ice cream ta kunna TV,
"Wani tasha kike so?
" Ki samin na Baby "
Kunna mata tayi sannan ta zauna itama tana shan nata tana kuma janta da hira,
Sai da yakai su har gida sannan ya dawo,shima zama yayi a falon yana hiran shida Aisha dan ita madan tunda ta gaida shi ta kawo mai abinci bata kara ce mashi komai ba,
Ganin ƙarfe goma saura ne yasa ya ɗauki Aisha ya kai ta ɗakin ta ya kwantar kan gado sannan ya dawo in da take ya zauna,"kina buƙatar wani abu ne "ya faɗa yana kallon ta.
Cikin basarwa tace" Ko na faɗa samu zan yi? Ta faɗa cikin yanayin tambaya.
"Kika sani"
Mikewa tsaye tayi"ni Barci nake ji sai da safe "
"Allah ya tashe mu lafiya,I Love you"
Jin abinda ya faɗa ne yasa ta juyo ta kalle shi cikin mamaki,
Murmushi ya sakar mata,yana ƙara maimaitawa "i Love you"
Da sauri ta juya ta shige daki ba tare data ce komai ba.
Faɗawa tayi kan gado gefen Aisha tana sauke numfashi "kome ya shiga kanshi yanzun kuma ohho" Addu'ar Barci tayi ta tofe jikinta dashi sannan ta tofa ma Aisha tana ja masu bargo,
Washegari da safe tunda suka yi Sallah ita da Aisha suka koma suka kwanta,
Da ya dawo masallacin ya leka yaga lokacin suna sallah shima dakin shi ya koma ya kwanta,
Wayar da aka mashi daga wurin aiki ana nimanshi shi ya tada shi,
Wanka yayi ya shirya sannan ya shiga dakin ta,
Cikin barci taji ana kiran sunan ta a hankali,
Da kyar ta buɗe Ido saboda ji take kamar mafarki take,"tashi muyi magana "
Mikewa zaune tayi,tana kallon shi da idanunta masu cike da barci,
"An kira ni wurin aiki,amma ba zan daɗe ba zuwa ƙarfi goma zan dawo,dan ina son mu fita,dan Allah kafin in dawo kiyi kokarin ku shirya ke da auta"
Da kyar ta iya cewa "To" ta koma ta kwanta,
Har ta lumshe ido sai kuma ta buɗe,
Idanunta ne suka sauka cikin nashi,daya kure ta da shi "zaka fita baka yi break fast ba"
Bai san sanda ya saki murmushi ba,lailai Allah ya fara ratsa zuciyar Sumaiya, "idan na je office zan ci"