← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 49

Sashe 42

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin natsuwa suke cin abincin,kiranshi aka yi a waya,dan haka ɗauka yayi yana dan matsawa gefe daga inda suke,
Yana kammalawa ya juyo ya dauki cokali ya saka a pleat,sai dai maimakon da dibo taliya sai gani yati yayi ba komai a pleat din,

Kallon ta yayi ya kalli pleat din dake gaban ta,nashi ne kuma saura kaɗan ma ta karasa cinyewa,
Yama kasa ce mata komai,sai da ta kammala ta haɗa pleat din sannan ta mika ma Aisha"haɗa ki wanke harda tukunyar,sai ki share kicin din,yanzun zan zo nayi morping"
Amsawa tayi ta kwashi kaya tayi kicin,

"Me yasa zaki cinye min abinci? Ta gi ya fada.

" Ban koshi bane,kuma abincin yayi daɗi "

"Shi yasa nayi kaɗan ai"

"Wannan ai mugunta ne,kasan zai yi daɗi badan ka yi yanda kowa zai koshi ba,ni ko yanzun na samu ƙari ƙarawa zan yi"

"Kuma ba zaki samu ba"

Turo baki tayi"amma dai kasan hakkin ka ne ciyar da ni har sai na koshi,amma kai na lura sam baka son haka"

"Hakan ba matsala bane in dai har zaki rinka motsa jiki,"

Da sauri ta girgiza kai"a'a bana so,ba zan je motsa jiki ba,"sai kuma ta marairaice fuska ta matso in da yake"Jauro,dazu kace in bari mu dawo gida sai mu yi magana"

"Wanne?

" Na batun koyarwar"

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace"naji ki bari zan yi magana da wani me makaranta da na gani sakan layin mu,sabon makarantar gomnati ne,idan kin ce zaki je na cikin gari kullum nawa zaki rinka kashewa kudin abin hawa,idan kin yi lissafi a wata babu wani abunda zaki samu,amma idan anan ne kusa da gida ba zaki samu matsalar komai ba"

Cikin tsananin murna da farin ciki ta rungume shi"na gode sosai Allah ya biya ka"

"Kiyi Addu'a Allah yasa ki samu"
"In sha Allah zan samu"

Sai zuwa ƙarfe takwas sannan ya sallame ta akan zai kwana a wurin aiki ranar sai kuma tara na safe zai dawo,dan ya kwantar mata da hankali dan yaga ta fara fadin duk girman gidan su biyu kawai zasu kwana,tace karta damu,gobe da da zaran ya dawo zai kai ta gida ita da Aisha,shine fa ya samu suka rabu lafiya da murnar ta akan gobe zata gida.
Ganin ta wuce ne yasa ta buɗe firig ta beda masu kindirmon da tayi,tasa suger suka sha,
Sai zuwa goma sannan ta kashe komai dama tuntuni ta kulle ko ina,suka shiga suka kwanta,
*Asuba ta gari Sumy*

Washegari tunda Asuba ta tashi ta gyara gidan,ka kafin ƙarfe tara har ta gama har abin kari sunyi wanka,
Shi kawai take jira,
Bai shigo gida ba sai kusan goma da rabi,zuwa lokacin gaba ɗaya ji take ranta a bace,haushin komai take ji,
Ganin sha ɗaya tayi ne yasa ta zauna ta fara sharan hawaye,
Ita kuma Aisha tana buga Game a wayar ta,

Shigowa yayi da sallamah,ya nufe in da take zaune a kujeran madubi,
Riko hannun ta yayi kawai ya mikar da ita tsaye"Sorry I'm late,muje na kai ku"sai lokacin ya lura da fuskarta,
Subhanallah ta fada yana saka fuskarta a tsakanin tafin hannun shi"me ya faru,me ya same ki"

Kokarin saka kuka take,yayi saurin katse ta"Shiiiii,ya isa haka,nasan ni ne,amma ba gashi na dawo ba,kin ga mai da hawayen in ba haka ba kika bari fuskarnan nayi ya koma ja,to zamu fasa tafiyar,sai dai nasa a maida ita "

Da sauri ta share hawayen daya zubo mata"me ya saka daɗe,bayan kasan ina nan ita jiran ka"

Rungume ta yayi "shi yasa nayi sauri na dawo,domin nasan rigimatu na tana jira na,muje nasan Mama na nan na jira"

Daukar Hijabinta ta yi ta saka sai hakkin Aisha data mika mata,har sun shiga mota tace ya tsaya tayi mantuwa,komawa tayi ta dauko roban kindirmo ta dawo sannan suka tafi,
Ko jira ya gama parking dakyau ba tayi ba ta fita da gudu tana kiran sunan Mama tun kafin ta karasa shiga cikin gidan,

A tsakar gidan ta samu Mama tana wanki wance jin muryar mai kiran ta ne tasa ta tsaya tana kallon kofar gidan,

Tana shigowa ta taci birki a tsakar gidan tana wurwurga idanun ta don ganin ta ina zata ganta,ta daki ko ta kicin,idanun sune ya fada cikin na juna ai kuwa tsalle biyu tayi sai gata rungume a jikinta,tana dariyar farin cikin,
Ita kanta Mama dariyar take,
"To sake ni karki karasa ni"ta fada tana dago ta,
Suna kara haɗa ido kuma da Mama sai fashewa tayi da kuka ta kara rungume ta,
Dariya ta saka" A'a me kuma na kuka bayan gaki a kafaɗa ta"

"Mama naji kewar ki" Ta faɗa tana kara sautin kukan ta.

Daga bayan su suka ji ance"Mama to ni ba zaki rungume ni ba,ko dai ni baki ji kewata bane"

Murmushi ta sake"wane ni nace banji kewar Auta na ba,maza zo nan naji dimin ki"da gudu ta karaso ta rungume duka.

Wasu yara ne suka shigo da manyan ledoji suka ajiye suka fita,

Daki suka shiga ta faɗa kan gadon Mama tana mulmula "gado nayi kewar ka sosai,do you miss me"

"Mama Uncle Jauro na waje "

Salati ta saka tana kallon ta"dama tare kuke shine baki faɗa min ba"

"Nifa Mama mantawa nayi"

"Kin ga Aisha fita ki ce masa ya shigo"

"To Mama" Ta fita kuwa da gudu,sai gasu tare,
Sun gaisa cikin mutunci sosai ta masa godiya ta saka masa Albarka,
Aisha ya faɗa ma ta faɗa mata sai zuwa yamma zai dawo ya dauke ta,

Sun jima suna hira sosai na bayan rabuwa da irin kewar Mama da ta ji,
Ita ta karasa wankin ta kuma daura girkin rana wanda tayi dambun shinkafa,
Mama kuwa duk inda tayi tana bin ta da ido tare da godewa Allah,

Misalin karfe hudu na yamma ta idar da sallar kenan ko tashi bata yi ba saman darduma ta fara jin hayaniya tsakar gida da kuma kuka dake tashi,

Cikin sauri ta shafa Addu'a ta fito,
Tsayawa tayi a ƙofar daki tana kallon su domin tama kasa karasowa,
Aunty Amina ce rungume jikin Mama tana rusar kuka,
Kafafunta ko takalmi babu,kuskanta ya kumbura sutum dan idonta daya kamar zai rufe saboda kunburi,
Ga jikin ta dun satin duka ta ko'ina.........
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*51*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Cikin tsananin tashin hankali ta karaso inda suke tsaye,gabaɗaya ita kanta jikinta har rawa yake tsabar tsoron irin ganin halin da ƴar uwarta ke ciki,ga Mama tsaye ta kasa magana,gaskiya wannan abin yayi yawa,duk da yana dukanta amma na wannan karon na daban ne,
Zamewa tayi daga jikin Mama ta zauna a kasa tana cigaba da kuka,

Dagota tayi daga zaunen da take tana rike hannun ta tasaka ihu tana dafe hannu,
Da sauri ta saki mata hannu,tana jin hawaye na zuba daga idonta,bata taba ganin yayar nata cikin irin wannan yanayin ba sai yau,
Cikin dubara ta taimaka mata ta tashi suka shiga dakin Mama,wacce suka bari tsaye ta kasa yin komai,

Zaunar da ita tayi kan ga,ɗan kwalin kanta ta cire tana kokarin goge mata hawaye,sai dai tana kaishi saman fatan fuskarta ta saka ƙara tana kauda kai,dan ko'ina aka taɓa a jikinta duk ciyo yake mata,

Ajiye ɗan kwalin tayi gefe tana share hawayen ta,dole ne ta zame masu ƙarfin guiwa,ƴar uwarta tana bugatar wacce zata kwantar mata da hankali ta fahimci ciyon da take ji,
"Aunty Amina" Ta kira sunan ta,

Dago kunburarrun idanun ta tayi ta kalle ta,
"Aunty Amina me ya faru,ba zan tambaye ki wa ya maki wannan ɗanyen aikin ba,dan nasan ba zai wuce Baban Amir ba,me ya faru?
Chapter 42 · 0% Book details