Sashe 6
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai bayan Sallar La'asar wuraren biyar Baffa Dottiya ya dawo,shine inna ta aika Yabbale ɗan gidan Baffa Sanda da ya kira mata iyayen shi maza duka tana son ganin su,
Haka kuwa aka yi duk suka halarta kiranta,sai dai tsakanin Sanda da Bube ba wanda ya zauna kusa da ɗan uwan shi,kuma hakan be dame ta ba,illa daurawa da tayi da faɗin "nasa an kira kune dan na sanar daku lallai duk inda za ku nimo masu gini ku nimo,domin a gobe nake so a raba wannan gidan kashi uku ai ma ko wanne katanga,dan ba zan iya da wannan abin kunyar da kuke ƙoƙarin jawo min ba, gara a raba ya zamana ba mai shiga ɓangaren ɗan uwan shi"
"Yauwa Inna,wannan hukuncin naki yayi,dan gaskiya zama gida daya da kwartaye hatsari ne,dama kuma ko baki faɗi haka ba inada niyar aikatawa"
Baffa Dottiya ne da bai gane meke faruwa ba yace"wani irin Kwarto,sannan muna zaune lafiya ne yakawo batun rabon gida?ya tambaya yana kallon su,
Nan Inna ta kwashe komai ta sanar masa,ai kuwa mai zai yi banda dariya har yana tafawa,nuna Sanda yayi da hannu"yanzun kai ka rasa wacce zaka tsaya leke sai wannan mai kama da Kurbirgar(Muciyar tuwo)"
Nan take ran Baffa Bube ya ɓaci jin sunan daya kira matar shi,
Cikin jin haushi yace "ai gara nawa matar suffar muciya gare ta,ko ba komai mata ke rike muciya ba maza ba,kaga kenan ko tanan tana da suffar mata, akan matarka da take a tsaye kamar Garii (namijin bigimi),kuma wannan munafikin babu ni babu shi har abada kai har ranar tashin ƙiyama,ko zuri'a ta ban yarda ka kirasu da ya'yan ka ba,kamar yanda Ya'yan ka ba ya'yana bane har tashin duniya,Inna ki zama shaida
"Sai me dan kace haka,aikin banza,Allah na gode maka daka fara bani yaya baka yini juyaba,da na kashe kai na dan bakin ciki,kuma ko baka faɗa haka ba,dole haka zai faru saboda wannan shedaniyar da ka Aura,kuma ina mai tabbatar maka kai da kwanciyar hankalin iyali sai dai a lahira in ana yi kayi,dan na lura baka cikin masu rabo"yana gama fadar haka yaja dogon tsaki ba tare daya ce masu komai ba ya mike tsaye yana barin ɗakin,domin bazai lamince tozarci irin na yan uwan shi ba,
Ganin ya bar dakin ne yasa kowannen su ya tashi ya bar dakin cikin jin haushi ba tare da ko wanne su ya ma tsohuwar da ke zaune magana ba,kamar yanda ita ma bata ce masu kuci kanku ba.
Washegari da safe ko gama wayewa gari bai yi ba,sai gashi masu aiki sun zo wadanda Baffa Sanda ne da kanshi ya gaiyato su domin su kangemai shiyanshi dana matarshi,sannan yasa a kara buga masu Bukka,
A taikaice dai a wannan gidan rana bata faɗi ba sai da aka kange waɗannan shiyoyin guda uku,
Hakan ne yasa gidan aka ɗan samu kwanciyar hankali na kwana biyu,domin kowa na shiyan shi,
A tsakanin kwana biyun nan kuwa,sam Baffa Sanda ya hana Yayanshi shiga shiyan sauran ƙannen nasa,sai dai shi jauro yana shiga wurin yara ƴan uwan shi,kun dai san yanda yara suke,
Ana cikin haka ne Baffa Dottiya ya tattara kayansa da dabbobin sa wai zai tafi cirani,
A cikin su ba wanda ya damu da hakan domin su a al'adar su ba wani abu bane,
Cikin taimakon Allah kuwa suka bar gida shida matar sa wanda a lokacin Jauro yanada shikara biyu da rabi,
A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah dan wasa_wasa sai da Baffa Dottiya ya kwashe shigaka hudu a wurin yawon shi na kiyo daga nan garin zuwa nan garin kafin su waiwaye gida, tare da tarin Alkhairai domin kuwa a lokacin dabbobin shi na shanaye kaɗai sun tasarma garke biyu da yan kai,kamar yanda tumakai wato raguna sunkai garke daya,ya nada yara wadan da suke binshi kusan su huɗu,yana biyan su domin su tayashi kula da dabbobin shi,sai dai shi ya rigasu isowa gida dan su suna hanya,saboda rashin lafiyar matarshi shi yasa ya fara wutowa gada, wanda a lokacin abubuwa da yawa sun faru,kuma suna kan faruwa,domin kuwa Matar Baffa Bube a lokacin yaranta biyu,kuma tana dauke da cikin na uku,
Ko da suka dawo a shiyansu na da suka sauka kuma ita ma Halima lokacin cikinta na da wata takwas,wanda yake matukar bata wahala,kusan ko yaushe a kwance take ba lafiya,
A washegarin ranar da suka dawo ne taja hannun ɗanta suka shiga shiyan Inna Mari wacce ke shiya daya da Baffa Bube,domin kuwa duk cikin ya'yan ta tafi son shi,
A hankali suke tayifa har suka shiga shiyan wanda tun daga bakin kofar zaka fara jin hayaniya na tashin hankalin da ake yi,
Duk da hayaniyar da take ji hakan bai sa ta fasa shiga ba,
Sai ma kallon ɗanta da tayi "Har yanzun iyayen ka sunki suyi hankali"
Shima baice komai ba sai kallon ta da yayi,
Da sallamah ta shiga ɗakin Inna wacce take zaune tana sauraren bayanin da Binta ke yi "wallahi ba zan yarda ba,haka kurin ban haifarwa wata katowa ɗa na ba danta dinga jibgarshi ba,ba zan lamunta ba,haka jiya tsabar mugunta ina kallon ta data shigo kawo maki tuwo ta tunkuɗe Bakari,sai da kanshi ya bugu da tukunyar miya,na dai yi shiru ne kawai na kyaleta domin kar ka yi magana ace bakada kara akan dan fari,shi ne fa In faɗa maki Inna yau tana shigowa wai yaron nan Ɗan Fodiyo yazo da gudu cikin rashin sani ya buge ta,baƙi ga yanda ta daddage ta zuba mai Mari ba iya karfinta dan rashin imani,to wallahi ba zan yarda ba,ko dai adau min mataki ko kuma na dau ka da kaina"ta fada tana jijjiga jiki,
Ita ko Kande sai cewa tayi "kin daɗe ba ki dauki matakin da kanki ba,an gaya maki tsoronki nake yi,in banda rashin Albarka irin naki ke kika turo Ɗan Fodiyo ya zo ya bangajeni,yaro ina mai magana saboda rashin tarbiya sai cewa yayi ni ba ɗan ki bane da zaki min magana,har da hararata,ni tsaran shi ne"
Inna ce tace"to ba gaskiya ya faɗa ba Kande,ke uwar shi ce,ke ba uwarshi ɓace dan yaro ya faɗi gaskiya kuma sai kiji haushi,ke dai kawai ki fada wani dalili ne a kasa"kallon Binta tayi wacce take cika tana batsewa"ke ni ban iyawa da jarabarku idan ki nada yanda zakiyi da ita kiyi,me na cewa in dauki mataki,ku tafi na sallame ku ku bani wuri"ta fada tana nuna masu hanya,
Kande ce ta fara fita tana faɗin "sai ki yi duk abin da zakiyi domin dai nasan nafi karfin duka a wurin ki...
Kafin ta ankara sai ji tayi an wurgo mata marfin tukunya wanda bai tsaya a ko'ina ba sai saman goshin ta,nan take kuwa jini ya ɓalle,dafe wurin tayi tana kallon Binta wacce ke huci,
Kutmar uba,ai kuwa ba tayi katsa a guiwa ba tayi cikin Binta wanda nan take kokawa mai ƙarfi ya shiga tsakanin su,
Babu imani kuwa Kande ta shiga rusa mata kulli a ciki,wanda yake bai wuce wata uku ba,duka kuwa take har saida ta kaita kwance,
Dakin Inna kuwa duk abinda suke tana jin su sai cewa da tayi " Tsinannu sai ku kashe kan ku ai"
Ita dai da kyar ta mike tasan ko taje ba iya rabasu za tayi ba,domin ba daɗin jikinta take ji ba,
"Inna barka da safiya,"
"Ke raba ni da barka samun waɗannan tsinannu ba zasu bari na wayi gari lafiya ba"
"Inna bari in duba ko zan samu makota su zo su raba wannan faɗar"
Bata ce mata komai ba sai tabe baki da tayi,
Ta gefen su ta raba ita da ɗan ta suka fita,domin duk da tana kallon yanda jini ke diga daga goshin Kande kamar yanda jini ke gangara daga ƙasan Binta,
Bata iya sauri gashi kuma yanayin gidan fulani,daya can daya can,basu gida kusa da juna,dan haka kallon ɗan ta tayi"Jauro kayi gudu kaje ka kira duk wanda ka ci karo da shi "
"To inna na"
Da gudu kuwa yaro ya fita,cikin sa'a kuwa ya haɗu da matan Fulani su biyu suna ƙoƙarin shiga gida,rike hannun daya yayi cikin yaren fullanci yace,kuzo gidanmu Inna na tace in kira ko waye saboda ana faɗa,
Jin abinda yaron yace ne yasa suka bi bayan shi,ita ta masu jagora har shiyan Binta wanda zuwa lokacin duk sun jigata.....
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*9*
Ko da suka isa tuni Binta ta daɗe da suma sakamakon jinin da ya ɓalle mata,
Hankali su ya tashi sosai dan haka daya daga cikin matan ne tace bari ta je tama mazajen su magana tunda sunada mashin sai azo a tafi dasu Asibiti,
Duk amincewa suka yi da shawarta,dan haka da gudu tayi gida ta faɗa masu,
Da taimakon waɗannan matan ne aka ɗaura su a mashin aka yi asibitin dasu,sai dai Halima bata bisu ba,dan cewa tayi ita kam bata iya hawa mashin dan haka su tafi kawai,
A ranar dai ita Kande ta dawo,ita ko Binta sai da tayi kwana uku a Asibitin sai da tasha karin jini leda biyu,sannan ga ciki ya zube,
A kwana na uku ne da suka dawo Goggo Badejo ta zo,ɗan ita ma sau daya ta leka Asibitin,
Kallon Inna tayi tace "Inna ya kamata muje ki gaida Binta da jiki tunda ta dawo"
Kallan uku saura tayi mata"in gaida ita na me,ni na aiketa da zan mata sannu,ai da mutuwa tayi ni ba abinda ya dame ni da ta mutu Ɗa na aure zai ƙara,kuma ko yanzun tayi ta gama aure zansa yayi "
Bata ce mata komai ba ta tashi ta fita abinda,itama bata shiga dakin Binta ba sai tayi shiyan Baffa Dottiya wurin Halima,