← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 49

Sashe 38

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waɗannan Dabbobin fa?

" Duk wani abinda kika fara gani tun daga bakin Get har karshen katangar gidan mallakina ne"

"Idan har kanada wannan Arzikin me yasa ka aure ni a haka,na tabbatar da waɗanda suka baka aure na basu san komai ba dangane da kai,me yasa ka ɓoye masu ni ma kuma ka ɓoye min"ta faɗa tana juyowa gabaɗaya suna fuskantar juna.

"Iyayen ki basu buƙaci su da susan haka ba,mu je ki ƙarasa ganin wurin"

Bin bayan shi tayi suka fara takawa yana nuna mata ɓangare_ɓangare na gidan gonan.

Sakawa yayi aka cire masu ƙaton kifi guda daya sai kayan miya da aka zuba masu a bayan mota,harda kwai kiret biyu,
Kallon shi tayi"ina buƙatar madara"

Shima sakawa yayi aka kawo cikin ƙaramin jarka.

Mota suka shiga suka bar gidan gonan da A'isha wacce ki ji kamar kar a wuce, saboda kayan daɗin da ta ci,

Tunda suka fito bata ce mashi komai ba har suka yi nisa,

Ɗan kallon ta yayi"ki yi haƙuri idan har faɗa maki da banyi ba ranki ya baci,
A lokacin gani nike baki shirya sanin ko ni waye ba,
Gobe idan Allah ya kaimu zamu je ƙauyen mu ki gaida iyaye na"

"Ni kuma nawa iyayen yaushe zanje na gaida su"

"Naga wasu Amaren suna kaiwa wata hudu ko shida kafin su je gaida iyaye"

Cikin jin haushi tace"ba dai ni ba,ƙila gara su suna da wayar da ako yaushe suke ra'ayin jin muryan iyayen su sana iya ji,amma ni ko waya nace a ara min ko kallo na ba'a yi, dan haka karka fara wannan tunanin "

Bai bata amsa ba dai yaci gaba da tukin shi,
Gani tayi ya shiga Obasonjo complex,"ina zuwa"ya faɗa bayan yayi parking a cikin,

Bai wani jima ba sai gashi ya dawo hannun shi rike da leda,yana shigowa ajiye mata ledan yayi saman cinyan ta"ina fatan zaki zauna har na wata huɗu kafin ki je gida,tunda yanzun kin samu abin jin muryar su"ya faɗa yana ta da mota,

Ciro kwalin dake cikin ledar tayi,
Aikuwa kwalin yawa ne wanda taga samfarin IPhone ne,gashi an saka Iphone 12,
Kallon shi tayi ta kuma kallon wayar,"nawa ne? Ta tambaye shi cikin mamaki.

"Ummm"

Cikin sauri ta dauka ta maida mashi saman cinyar shi "to ni dai bana so in dan kaki bari na naje gida ne har na tsayin wata shida wallahi ba ni so"

Bai kula ta ba yaci gaba da tukin shi har suka isa gida,wanda ba karamin kule ta yayi ba,dan haka yana yin parking ko tsayawa ya buɗe mata bata yi ba ta buɗe murfin motar ta fita ba tare data kulle mashi motar ba.

Aisha ce ta taya shi suka kwashe kayan dake bayan boot zuwa kicin,
Sannan ya kunna mata kallo,

Dakin ta ya shiga in da ya same ta kwance saman gado tana faman rusa kuka,
Girgiza kai yayi ya ƙarasa in da take,kiran sunan ta ya shiga yi amma ko kula shi bata yi ba,
Zama yayi a bakin gadon yana ajiye kwalin wayar dake hannun shi,

"Amma ke kika faɗa da bakin ki"

Filon dake gefenta tawurga mashi.

Cabewa yayi,yana murmushi "to shikenan na fahimta," Mikewa tsaye yayi zai tafi"karki manta gobea da wuri zamu fita "

Cikin kuka tace"wallahi ba inda zan je,tunda ba zaka kai ni gida ba"

"Iyayen nawa ne ba zaki gai dawa ba?

Kin kula shi tayi ta ci gaba da kukan ta,

Ƙara zama yayi" Shikenan naji zaki ki gai da su"

Wani zabura da tayi ta Mike shi kanshi sai da ya matsa baya,

Nan take ta shiga share hawaye ta tas tamkar ba ita ta gama kuka ba,"da gaske,yaushe zan je? Ta tambaya cikin murmushi.

Kallon ta yake cikin mamaki,"nan da wata biyu "

Kafin ya gama rufe baki tuni ta kara fashewa da kuka wanda yafi nada ƙarfi dan wannan karon har darda filollukan dake kan gado ta shiga jifa dashi,"wallahi ban yar da ba,ni dai ban yarda ba wata biyu yayi nisa"

Da gangan ta shiga shureshi da ƙafa, har sai da ya zame daga kan gadon,

Kallon ta take tamkar wata me Aljannu "kin ga ya isa karki ji ma kanki,ki bari idan zan je mai da Aisha sai mu je tare"

Bai ga sanda ta tashi ba sai jinta da yayi a jikin shi makale tana dariya,"na gode sosai Jauro,na gode "

Shiru yayi yana sauraron bugun zuciyar shi,so yake ya tabbatar da yanda yake ji ko yanda zai ji,
Sai dai zafin jikin da yake ji a cikin kashi dari kashi arba'in ne yayi saura,dan haka ba sosai zafin ke ratsa shi ba,

Cikin tsananin farin ciki ya cire ta a jikin shi,dan baya buƙatar ta san meke faruwa,

"Ɗaga ni ya isa haka,kafin na canja ra'ayi"

Da sauri ta sake shi tana dariya,

Daukar kwalin wayar yayi zai wuce dashi,
Cikin sauri ta rike ledar "ina kuma zaka je min da waya?

" Cewa fa kika yi baki so"

"Da yaushe kuma na ce haka,kaga bani waya ta" Ta faɗa tana fizge ledan,

Girgiza kai yayi kawai yana barin ɗakin yana tunanin irin tarbar da zasu samu a ƙauye,Allah dai yasa kar ta jawo mai abin magana,
Dan dazu suna gidan barka ake sanar dashi cewa sun sako Baffa Sanda amma yana Asibiti shima,dan haka gode can zasu fara zuwa kafin su tafi ƙauye......

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*47*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Tunda taga ya bar dakin cikin farin ciki ta faɗa kan gado tana rungume wayar,buɗewa tayi a cikin kwalin sannan ta saka a caji,
Ganin lokacin sallah yayi ne yasa tace Aisha ta tashi suyi sallah,sai da suka idar sannan ta koma kicin,abubuwan da suka dawo dashi ta adana ko wanne in da ya kamata,shi kuma madaran shanun,juyewa tayi a wankakken tukunya sannan ta daura a Gas,tana tsaye har ya tafasa daya sannan ta sauke,ta koma daki,sai bayan mintuna sha-biyar sannan ta dawo ta juye a wani karamin roban fenti sannan ta wanke tukunyar,

Allah_Allah take wayar yayi caji ta saka number Mama da Aunty Amina ta kirata,she can wait to call them with her new phone,ai kuwa Mama ta shiga uku da kira.

Da daddare miyan farfesun kifin da suka dawo dashi tayi suka ci da tuwon shinkafa,

Washegari kamar yanda ya tsara ƙarfe goma suka nufe Asibitin IBB in da a can Baffa Sanda ke karɓar treatment,

Adaidaita ya zo har kofar gida ya dauke su zuwa Asibitin,
Suna fitowa a Adaidaita ya amsa basket din abincin dake hannun ta"Idan mun shiga ki gaida kowa cikin girmamawa"

Baki buɗe take kallon shi"kana nufin banda tarbiya?

"Nifa ba haka nake nufi ba,kawai dai b...

Cikin jin haushi ta fisgi hannun Aisha" Kaje kawai na fasa shiga gidan mu zan koma Mama ta ƙara ban wani tarbiyya "

Da sauri ya ajiye basket din dake hannun shi ya riƙo nata hannun,kallon Aisha dake kallon su tayi,yana lumshe ido,sam baya son suna nuna hali a gaban wannan yarinyar ƙarama,saboda yaran yanzun baki gare su,

Jawota gaban shi yayi"come on Sumy,why do you always want to take a fight with me,i know you know that is not what I mean,please not now ok"

Kara hasala tayi "ohh is that what you support to say,wato ni ce mai son tsokanar ka faɗa bancin ka kirani da mara tarbiyya ko,shi ne zaka faɗi haƙa"ta karasa faɗa tana shirin saka kuka

Dafa goshen shi yayi yana lumshe ido,shi ya zai yi da rigimar wannan yarinyar,shi kwata_kwata yanda ta ɗauki lamarin ba haka yake nufi,
Jawota jikin shi yayi ya rungume tunda bashi da option kafin ta tara mai mutane,
Shafa bayanta ya shiga yi"ok I am sorry that is my bad,I'm not to say that to Queen Sumy,kuma ni nasan kina da tarbiyya sosai,idan da ba dan tarbiyyar ki ba ai ba zan yarda na aure mace wacce ba irin ki ba,"

Kokarin kwace kanta take yi ya kara rungume ta "in baki ce kin hakura ba bazan sake ki ba"

Jin ya ce haka ga kuma Aisha a tsaye yasa da sauri tace"na hakura sake ni"dan tasan shi babu ruwan shi ba kunya ne dashi ba,

Sake ta yayi"are we good?

Hararan shi tayi kafin ta bashi amsa sun ji daga bayansu ana daɗin "Jauro kai ne?

Duk juyawa su kayi suna kallon matar wanda kallo daya zaka mata ka shaida zamowarta cikakkiyar Bafulatana,

Murmushi ya sake yana karasawa in da take tsaye daga dukkan Alamu wucewa za tayi," Goggo Halira ni ne,ba dai tafiya za ki yi ba?

Itama murmushi ta saki"wallahi tafiya zanyi dan tun da safe nake nan,"

Karasowa in da suke tsaye tayi,cikin girmamawa ta duka ta gaida matar data ji ya kira da goggo,

Amsawa tayi tana kallon kyakkyawan yarinyar "wannan kuma wacece,ƴar nan ki yi hakuri ban gane ki ba"

Dariya yayi"to Goggo ai yarki ce"

Kallon shi tayi,ganin yana mata dariya yasa ta gane"Oh Oh Oh Amarya ce ashe"daga ta tayi daga duken da take,

"Kinga kyale wannan dan nawa taso mu koma ciki,da tafiya zan yi amma na fasa," Ta fada tana jan hannun ta suka yi cikin Asibitin.

Wani daki ne suka shiga wanda a kalla marasa lafiya shida ne a ciki,

Wanda suka tsaya shi daga Dattijon dake kwance yana barci sai wata mata wacce daga dukkan alamu ƙila matar shi ce,
"Kande ga matar Jauro ta zo duba ku"

Kallon ta matar ke yi daga sama har kasa tamkar yanda ita ma take kallon matar,gaida ita tayi da me jiki,
Chapter 38 · 0% Book details