Sashe 37
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shi kenan Allah ya tsare"ta faɗa tana maida idanunta ta lumshe tare da kara jan bargo.
Murmushi yayi yana barin dakin.
Tashinta da Aisha ke yi ne tana faɗin yunwa take ji shi ya tada ita,
Idonta ne ya sauka kan Agogon daya nuna mata ƙarfe tara da minti ishirin,
Ai bata San sanda ta fado kasa ba,
Jan hannu Aisha tayi suka shiga bayi tare,maklin ta saka mata a sabon brush data buɗe mata ta bata,ita ma ta saka sannan suka yi,
Hitan ruwan zafi ta kunta ta zuba mata yanda zai ishe ta a bokiti tace tayi wankan bari ta haɗa abin ƙari,
Indomi ta dafa masu sai ruwan shayi,sai da ta karya sannan ta shiga wanka,
Ta fito ta na saka kaya ta ji maganar shi da Aisha wacce tuni ta shirya cikin riga da wondo da aka kawo mata tsaraba,
Kallon agogo ta kuma yi,goma da minti sha-biyar,
Jin shigowar shi ne yasa ta juyo tana kallon shi,
Takowa yake gabanta "Sumy na kin yi kyau"
"Na gode'
Mayafin ta dake gefe ya ɗauka ya mika mata" Muje "
"Kai ba zaka shirya bane" Ta faɗa tana kallon shi da wannan shigar nashi da ta tsana.
Washe baki yayi"ai ni a shirye nake"
Turo baki tayi"a haka"
Shima ƙara kallon kanshi yayi"eh,kinsan dazu na saka kayan nan kuma basu yi komai ba"
Ƙara turo baki tayi tana yin wurgi da gyalen hannun ta kan gado"to ni dai in dai wannan kayan zaka saka ba zanje da kai ba sai ka dawo "
"To yanzun ya kike son in yi,ok to bari na canja"
Har ya juya sai kuma ta dakatar dashi da sauri,durowan kayanta ta buɗe ta dauko jakkan ta mika mashi,
Amsa yayi"na menene wannan "
"Kayan dana tsiyo maka ne a England da muka ke shopping,"
Amsa yayi ya buɗe jakkan yana dubawa,baimasan sanda ya shiga sake murmushi ba,"na gode Sumy"
Ɗaukar jakkan yayi ya fita dashi,bai jima ba sai gashi ya shigo cikin shigar bakin wando da da riga Sky Blue ba laifi yayi kyau,
Yana shigowa ya shiga washe baki"kinga Sumy nayi kyau ko?
Nuna mashi kujerar madubi tayi"zauna anan"
Zama yayi ta dawo gaban shi ta tsaya,"me zaki yi Sumy Baby?
Bata bashi amsa ba ta dauko karamin Kum da mayukan kai,ta shiga shafa mashi a suman shi da duk ya naɗe,hand dryer da ta siyo ta dauko ta jona,nan ta shiga aikin gyara mashi suma,kafin kace me sai gashi suman ya kwanta a kanshi har daukar ido yake tsabar yanda yaji kyara,
"Kanada sheba?
Cikin jin daɗi yace" Eh bara na dauko maki "
Da sauri ya koma dakin shi ya dauko mata,amma Digital ne,dan haka a hankali tayi amfani dashi ta kyara mashi fuska tas,duk gashin da ke fuskar a yamutse ta fitar dashi,sai dan sajen data bar mashi,
Kallon fuskar shi yake a madubi tamkar yanda take yi,ta cikin madubin yake sakar mata murmushi"Sumy Baby kinga yanda nayi kyau sosai ko? Na gode Allah ta maki Albarka,"
"Amin"ta amsa tana yaba yanda kyara ke kyara mutum,ɗan wani tunani ne ya faɗo mata,nan take ta sake murmushi,wato ganin yanda fatan shi ke a murje saboda Jauro baya cin ƙazamin abinci,zai iya kashe ma kanshi ko nawa ne dan ya koshi,sai dai ko Mai na shafa bata tunanin yana da na Arziki,dan haka sai ta saka ya koma shafa Mai mai tsada ta yanda cikin kankanin lokaci zai washe ya dawo dan gayu (A zuciya ni ma nace Allah yasa dai kar a siya mashi Man bilicin)
"Ni dai ka tashi mu tafi tunda an gama kaga sha ɗaya har tayi"
Mikewa yayi ya dauko mata kyalen da ta yi wurgi dashi ya mika mata "mu je ko"
Tare suka fito sannan ta kashe kayan Kallo suka fita,
Shi ke jan motar tana zaune a gefen shi,sai Aisha dake baya,
Sunyi tafiya mai nisa a cikin gari kafin tace"ni kan kamar hanyar gidan ka ji "
"Ashe kina gane wuri"
Zaro ido tayi"ba dai kashin kajin zaka kai ni na kwashe ba?
Dariya yayi yana dauke hanyar wurin in da taga sign Board an rubuta EL WAZIR,(Littafi na mai zuwa)
Cikin unguwar suka shiga,tun daga bakin layin take kallon wani irin makeken katanga wanda sai tafiya suke da mota amma basu kai ƙarshen shi ba,
Nuna mashi katangar tayi"nan ina ne,ko kamfani ne?
"A'a gida ne"
Cikin mamaki tace "gida kuma,amma naga kamar yayi rabin unguwar ai,yanzun akwai mutane ciki?
" A'a mutum ɗaya ne ina ga a ciki"
Mamakin ta ya ƙara karuwa,tana juyawa baya dan kara kallon katangar da suka bari"duk wannan katon gidan,to ai wannan yaci rabin unguwar,to waye a ciki?
Kai tsaye ya bata amsa da "EL WAZIR"
Shiru tayi tana maimaita sunan a zuciyar ta,tana kuma mamaki,jin yayi parking a ƙofar wani gida ne yasa ta ɗaga kai tana kallon ƙofar madaidaicin gidan,
"Gidan abokin aiki na ne,matarshi ta haihu ku shiga ku mata barka " Mika mata wani babban leda yayi"wannan ki bata,da kin ce mata matar Jauro ce ke zata gane"
"Ok " Ta faɗa suna fitowa daga cikin motar,
Kamar yanda ya faɗa haka tayi,ai kuwa matar ma ba wata babba bace,ta kuma ji daɗi sosai,gata da fara'a,
"Kiyi haƙuri bamu samu halartar bikin ku ba,lokacin ina fama da ciki"
"A'a babu damuwa nasan wata rana ke ma zaki zo"
Cikin sakin fuska tace"insha Allah "
Wata yar budurwa ce ta shigo gidan ta zauna tana sauke numfashi,
"Lafiya Zainab? Hajara ta tambaya,wato mai Jego,
" Ke dai bari na gama sauke numfashi,wallahi Aunty Hajara Salmanu bai da hankali, kin San Me ya faru "
"A'a sai kin faɗa "
"Katangar gidan EL WAZIR ya je ya jingina dashi yana ɗaukar hoto,na faɗa mashi sunan shi gawa,domin ba'a taba koda katangar gidan WAZIR mutum ya kwana lafiya,gani yake kamar wasa nake yi,Allah kaɗai yasan iya adadin mutanen da suka mutu"
Zaro ido tayi"shikan wani tsautsayi ya aike shi,Allah yasa yana da sauran shan ruwa"
Kallon su tayi"waye EL WAZIR ,bani labarin shi"
"Ke rufa ma kanki Asiri,domin irin su ba'a bada labarin su,hakan hatsari ne amma dai mutum ɗaya ce zata iya sanar dake waye shi"
"Wacece ita"
"JIDDARH UMAR"
"Ina zan same ta dan gaskiya so nake na San komai"
"Ki bari duk randa nazo har gidanta zan kai ki"
"Kafin nan dan Allah ina da tambaya,shin wannan EL WAZIR din hala tsoho ne"
Tare suka haɗa baki wurin bata amsa"Yaro ne ƙaramin da bai wuce shekara Ishirin ba"
Wannan karon mamakin ta ya kasa boyuwa,sai dai kafin ta kara sako masu wata tambayar,sai ga mikin Aunty Hajara ya shigo yana faɗin "Amarya wai ki fito ku tafi Jauro na jira"
Murmushin dole ta kakalo domin Allah ya gani taso ta ƙara jin wani abin,
Ya ta iya,haka dai tai masu sallamah ta shiga mota suka tafi,
Sai dai wannan karon ta wata hanyar yabi cikin unguwar sai gasu sun bullo bakin titi ba tare da sun bi ta wurin gidan EL WAZIR ba(coming soon),
Sunyi tafiya sosai kafin ta gane inda suka dosa,bata dai ce mashi komai ba har aka buɗe masu Get suka shiga,
Sai dai maimakon taga sun tsaya wurin rannan sai gani tayi sunyi tafiya mai nisa daga wurin kafin ta hango wani Flat,nan ma suka wuce sannan suka isa wurin wani lambu mai matukar kyau,
Parking yayi ya fito sannan ya buɗe mata ita ma ta fito ita da Aisha,
Rayawa take a ranta,in dai har aiki ya kawota tayi ai kuwa sai ta shuka mashi rashin mutumci,sai dai kuma wurin ya burge ta sosai,ga iska mai daɗi dake kadawa............
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*46*
*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*
Ganin sun tsaya kalle_kalle ne yasa yace"mu je "
Da sauri ta bi bayan shi,har cikin lambun in da ta hango wasu tsofaffin Fulani zaune suna hutawa saman Dardumai,
Sallamah tai masu tamkar yanda shima ya yi,ta cire takalmi ganin ya cire,
Murmushi duk suke sakar masu kafin daya daga su yace"Ƴata Bismillah kara so nan ku zauna,
Karasawa suka yi ta zauna kusa da Jauro,cikin natsuwa ta gaida su,suna amsawa,
Wani mutumin ne ya zo ya gaida su,kafin Jauro ya juyo wurin Aisha "zaki sha daran shanu? Ya tambaye ta,
Da sauri ta gyaɗa kai,
Murmushi yayi ya juyo kan mutumin dake tsaye" Muntari kai ta ka tatsar mata madara mai zafi"
"To angama"
Hannu ya mika ma Aisha "kanwata taso mu je" Tashi ta yi ta bi shi,
Kara cewa yayi"ka zagaya da ita in akwai abinda take buƙata ka bata "
Nan ma amsa mashi tayi da angama.
Hira suke janta dashi sama sama,suna kuma saka ma rayuwarta Albarka wanda hakan ba karamin daɗi yake mata ba,
Jauro ne yace masu zasu je su ɗan zazzaga kafin su tafi,
Dan haka sallamah ya masu tare da faɗa masu sai zuwa yamma in ya dawo,
Suna fitowa lambun tace"iyayen ka na da kirki"
Murmushi yayi"na sani"
Tabe baki tayi,"to ina kuma zamu,naga sai tafiya muke"
"Siyar dake zan je yi"
Kallon shi tayi"ka taɓa ganin in da mutum ya saida kanshi "
"Kamar ya"
"Bar shi kawai"
Murmushi yayi domin ya fahimci me take nufi,
"La kalli shanaye da yawa"
"Mu je ki gani"
Cikin zumudi tabi bayan shi suka je wurin,sai dai dan nisa kaɗan da wurin suka tsaya tana kallon su,manya da yara,
Ba tare data kalle shi ba tace"Shanayen nan sun kai guda nawa?
"Suna da yawa"
"Ina son na san wanda nake Aure,shin zaka bani damar haka?
Wannan karon juyowa yayi yana fuskantar ta,sai dai ita bata kalli shi ba,hankalin ta ya kan dabbobin da ke gabanta.
" Tunda har kin buƙata me zai hana "
"Wannan gidan gonan na waye?
" Nawa ne"