Sashe 34
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu jimawa kuwa sai ga yaro ya dawo wai bayanan yanzun ya fita,
Cewa yayi yaron yaje ya amso number shi,
Aikuwa sai gashi ambashi a rubuce ya kawo mai,
Bai bata lokaci ba ya shigar a wayar shi sannan ya danna kira,wanda kara biyu yayi aka ɗauka,
Sallamah yamai suka gaisa sannan yake sanar dashi mijin kanwar matar shine Jauro,
Kasancewar sun taɓa haɗuwa sau daya sai kuma ranar ɗaurin aure "ohh Jauro ya kake ya gida,ya kuma Sumayya da fatan tana lafiya?
" Lafiya kalau,dama wata Alfarma nazo nima a wurin ka"
Dan shiru yayi yana nazari a zuciyar shi,dan wallahi in dai kudi ne bazai ba shi ba koda rance ne yanda gari tayi zafin nan,
Nan take ya rage fara'ar fuskar shi"ina jin ka"
"Yauwa dama in babu damuwa so nake ka bamu aron Aunty Amina ita da yara su je ma Sumayya yini,dan ba ta da lafiya idan ta ganta kuma zata ji daɗi"
Ajiyar zuciya ya sauke jin ba abun da yake tunani bane "a'a babu damuwaJauro,sai dai ni ba ni da kudin motar da zan bata har zuwa ƙauyen ku gaskiya"
Jinjina kai yayi,yana mamakin mako irin na mutumin,gashi dai yana da rufin asiri dai dai gwargwado,sai dai kullun cikin kiran babu yake,
"Ok babu damuwa dama ni ma gani a ƙofar gidan na dauka kana nan ne shi yasa nazo da kaina"
"To ba damuwa hakan yayi,"
"Na gode sosai,sai anjima"
"Yauwa" Ya faɗa yana kashe wayar.
Shikuma wani yaron ya ƙara aikawa akan yaje ya ce ana sallamah da Aunty Amina in ji Jauro.
Ko mintina uku ba'a yi ba sai gata ta fito da sauri har katon hijabin da ta saka yana tadiyeta,
Karasowa tayi inda yake baki buɗe "Jauro kaine?ina sumaiya?
Murmushi ya sake" Tana nan tana jiranki,"
Dan dakatawa yayi"kamar ya,tana nan dai lafiya ko?
Wannan karon dariya yayi kaɗan ganin yanda tayi "karki damu tana lafiya,kinga shiga ki fito da yara,mun yi magana da mijinki yanzun ya yarda na kaiki wurin ta"
Murmushi ne ya baiyana a fuskarta saɓanin da datsoro ke mamaye a fuskarta,"la yau zani na ga sumaiya,to bari nayi sauri na karasa shiri"
Jinjina mata kai yayi,
Har ta juya sai kuma ta ƙara juyowa
Dan Allah ka jira ni karka tafi,
Cikin tabbatarwa ya jinjina mata kai.
Cikin sauri ta karasa yin abubuwa da zata yi, Allah yasa week end ne duk yara na gida,dan haka tare suka fito suka same shi cikin mota zaune yana jiran su,
Ita kanta tayi mamakin ganin shi da mota,dan haka ta yi tunanin kila na abokan shi ne ya ara,
A maimakon taga sunje wani wuri sai gani tayi sun shigo cikin unguwar su,kasa daurewa tayi "A'a Jauro ni kan Sumayya tana gida ne?
" A'a so nake mu ɗauki Aisha mu tafi da ita "
Dariya tayi"kace dai ana ji da Sumayya,yau mama sai tayi farin ciki "
Shima dariyar yayi,
Aunty Amina ce ta shiga da kanta ta fada ma Mama,sannan tazo tace ya shiga su gaisa da Mama,
Ba karamin daɗi yaji ba da irin addu'ar da Mama ta mai,har da zai wuce ya ajiye mata dubu biyar,
Ya kuma roƙi dan Allah ta bari Aisha tai masu week end a can,
Cikin sauki ta amince,dan so take ko ba komai ta san halin da ƴar ta ke ciki,sannan Sumayya ma zata ji daɗi,
Haɗa mata kaya tayi kala biyu a leda baki ta bata,sannan suka wuce,
Surutu kawai yaran ke yi a mota wanda hakan ba karamin daɗi yake mashi ba,yana fatan wata rana yaga yaransu tare da sumaiya,
Ita dai Aunty Amina kallon hanya kawai take yi ta yanda nan gaba ko da zata je zata iya gane hanya,
Sai dai gani tayi suna bin hanyar lafiyayyen titi,har suna iso Estate ɗin,kafin taga sun yi parking a bakin kofar wani babban gida madaidaici,
Fitowa yayi ya buɗe get ya shigar dasu har wurin ajiye mota kafin ha juyo yace"ku fito mun iso, bari na kulle get "bai jira cewar su ba ya koma in da ya kulle get din sannan ya dawo inda suke tsaye suna kallon gida,
" Muje Aunty Amina "
"To ta ce tana ƙara kallon ko'ina,"
Buɗe ƙofar falon yayi suka shiga yayin da wani ni'ima taccen kanshi da sanyin AC ya masu maraba,
Su dai bin bayan shi suke yi har ƙofar wani daki"Bismillah muje tana ciki"
Tare suka shiga,inda har yanzun take kwance saman lafiyayyen gado tana sharan barci,dan har ta yaye bargon dake jikin ta,
Wani irin sanyayyan ajiyar zuciya Aunty Amina ta sauke,dan sai yanzun hankalin ta ya kwanta,dan wallahi da jinin ta a kumba yake,
Karasawa tayi da sauri in da take kwance wanda kafin ta isa ma har yaran sun rigata rugawa da gudu sun faɗa kan Sumayya suna kiran sunan ta da suke kiranta dashi wato Ummin mu,suna jijjigata,
Shi kuma Jauro ya karasa kansu yana sauke su daga jikinta"karku karya min mata bata da lafiya "
Dariya Aunty Amina ta saka"ni dai banga alamun ciyo ba nan sai dai raki irin na sumaiya "
Jin nauyin an danne ta da hayaniya ne yasa ta buɗe ido,
Ai da sauri ta zabura tana rungume Samir,"da gaske kai ne?
Jin an saka dariya ne yasa ta juyo,bata masan sanda ta ture Samir ba ta sauko da gudu tana rungume Aunty Amina dake mata dariya,
Ganin haka ne yasa ya juya ya bar dakin fuskar shi dauke da murmushi.
"Aunty Amina anya ba mafarki nake ba"
Dan mintsininta tayi,
Ihu tayi tana shafa wurin,
"To kinji ba mafarki kike ba,mijinki ne ya dauko mu"
Aisha ce ta hau buga kafa "Aunty Sumayya ni ce kaɗai baki so da baki rungume ni ba"
Dariya ta saki na farin ciki tana jawota jikinta ta rungume ta"yi haƙuri autar Mama ban ganki bane"
Shigowar shi ne ya katse su,yana ajiye manyan ledojin dake hannun shi,"Aunty dan Allah idan tayi wanka sai ta fara cin wani abu anan akwai ledan magani ki cire mata tashi,"
"An gama ƙanina" Ta faɗa fuskarta dauke da murmushi,
Kara fita yayi,
"Kai tunda baki iya bani wurin zama ba ni kan bari nayi karan banin zama kan kushin"
Dariya tayi tana jawota suka zauna kan gado "duk cikin murnan ganin ku ne"
Jin motsin leda ne tasa Aunty Amina juyawa tana fi ɗin "Amira bana hana ki taɓa abinda ba'a aiki ki ba,wa yace ki taɓa ledar "
"Kai Aunty Amina ki kyale ta, kawo na buɗe maki"
Ita da Aisha ce suna dauko ledojjn,
"To kinga har da ƙaramar uwa ma tana son abun cikin ledar"dariya suka saka,
Ciro kayan kwalamar dake ciki tayi ta zuba masu a gaba," Aunty Amina bari naje na yi wanka"
"Ok sai kin fito ki dai yi sauri dan yau kan akwai hira"
Da sauri ta shige bayi tayi wanka tana jin karfin jikinta na ƙara dawowa ga kuma farin ciki da take ciki,
Tana fitowa ko mai bata shafa ba ta saka doguwar riga na jallabiya ta dawo ta same su,zama tayi suka ci kwalamar tare harda Aunty Amina suna yi suna hira,
Sannan tasha magani,
"Aunty Sumayya ki kunna mana kallo,naga kayan kallo a falo"
Mikewa tayi"to muje"kallon Aunty Amina tayi"ina zuwa Aunty "
"A'a bari na taso ni kan ki kai ni naga gida da kyau"
"To mu je"
Tare suka fito ta kunna ma yara TV, sannan suka fara shiga kicin,
Buɗe baki da ido tayi"masha Allahu,kai kai kai,Sumaiya,wannan duniyar duk kicin ne,"
Dariya ta shiga yima Aunty Amina,ganin irin santin da take yi,
"Kicin ne mana Aunty Amina,ga wurin girki"
"Kai Alhamdulillah Allah mun gode maka,waɗanda suke tunani zamu sha kunya su ne da kunya,dama Jauro na da irin wannan dukiyar shine ta ɓoye mana? Dazu kinga kuwa a irin motar daya dauko mu?Allah na gode maka hutu yazo"
Tabe baki tayi tunda ta ji ta ambaci sunan shi,"muje mu gani dan nima ban ga gidan ba"
"Ke da gidan ki kice baki gama gani ba"
"Jiya fa muka dawo daga England"
"Kai Sumayya ban da karya"
Juyowa tayi "wallahi da gaske nake,muje dai mu gama gani,amma akwai labari"
"Shi kenan muje,amma har na matsu mu je"
Sun zagaya gidan sosai dan ita kanta tayi santin gidan sosai,kafin su dawo cikin dakin ta,
Zama tayi kan gado tana nishi,
"Ke ni bani labarin me ya faru bayan mun kaiki wancan gidan,"
Ajiyar zuciya ta sauke,sannan ta shiga bata labarin tun daga kaita da sukayi da zamansu a Hotel har zuwan su England da dawowar su,"Aunty Amina har yanzun na kasa sanin asalin waye nake aure,na kasa sanin halin shi,me ya mallaka menene a rayuwar shi,shi din wani irin mutum ne,har yanzu na kasa sani,wani lokacin idan yayi wani abun ki na ganshi da wani abun har mamaki yake ban,na rasa gane inda rayuwar shi ya dosa"
Ita karan kanta nazari take yi "to wannan gidan fa?
" Da fari da muka zo ya ce min na shi ne,daga baya dana matsa mai yace wai na ogan shi ne"
"Amma ke a naki hasashen ta kike gani"
"Ina ganin na shi ne kawai,dan a yanda na lura yana da kudin kawai bai son nuna wa ne"
"In dai har da gaske na shi ne,ba damuwa,sai dai ina son kibi mijinki a hankali domin ki gano da wani irin mutum kike zaune,bawai sai kin fara tara iyali dashi ba,sannan ki fahimce waye shi,a lokacin kuma lokaci ya kure maki,dan haka cikin sanyi,dubara,sakin fuska,zaki iya fahimtar shi,ku kwantar da kanki,na tabbata cikin sauki zaki gano komai dangane dashi saboda na hango soyayyar ki sosai a idanun shi,idan har kika ci nasara akan komai Sumayya,na tabbatar hakan tamkar narasan mu ne ni da Mama,domin zaki taimaka mata,"
Cikin damuwa tace "Aunty Amina bana son shi ko kaɗan,har yanzu bana jin son shi"