Sashe 1
Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🍂JAURO🍂
(MAI ANGUWA)
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~
*Ban yarda wani ko wata ya daura min littafi a shafin sa ko ya mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
01
Shigowar ta dakin yayi dai-dai da ɗaga kwalbar da tayi tana ƙoƙarin kaiwa bakin ta,
Cikin matsancin sauri da zafin nama ta fisge kwalbar tayi jifa dashi,wanda yana dakar bangon dakin ya tarwatse ya tafe,
Kallon ta take cikin mamaki da matsanancin tsoro tace"me nake shirin gani haka SUMAYYA,ba dai kashe kanki kike kokarin yi ba?
Fashewa da kuka tayi"me yakawo ki a dai-dai wannan lokacin,me kika zo yi Salma?
"Ki bani amsar tambayar dana maki tukunna,me yasa zaki kashe kanki,Alhalin kin san hukuncin wanda ya aikata haka ko a wurin Allah"
Cikin gunjin kuka tace"eh kin faɗi gaskiya kashe kai na zan yi,mutuwa zan yi,gara na mutu kowa ma ya huta,idan na mutu ai shine nan"
Ganin yanda take kuka ne yasa ta rungume ta "ya isa haka,ba ki bukatar mutuwa,rayuwa ce ta kamace ki ba mutuwa ba, me yayi zafi haka"
Jan majiya tayi suna zama kan gado,
*Salma,da in aure shi Gara na mutu,gara ace na mutu,in yaso Baba in gawata zai sa akai gidan sa sai akai "ta faɗa tana share hawayen idon ta.
Dafe goshi tayi" Ohh My God,pls SUMAYYA not again,ina ce mun riga mun gama maganar nan dake,"
"Bamu gama ba Salma,in dai a kan Jauro ne bazamu taba gamawa ba har sai ranar da aka fasa wannan auren,"
"Wai ɗan Allah me matsalarki da Jauro ne da baƙi kaunar sa har haka,ni banga aibin yaron ba"
Wani dan iskar kallo ta jefeta dashi"wai shin kinsan waye Jauro,?kin taɓa ganin shi ne?
"Eh ko ba shi bane wani dan dogo fari haka ya nada saje"
Wani uban tsaki ta buga,"to Sulaiman ne kika gani ba Jauro ba,nasan cewa Sulaiman yana da ɗan kyau daidai gwargwado,kuma ba Class dina bane shi,domin koyarwa yake a makarantar Secondary,amma wlh Gara na aure shi akan na aure Jauro "
"To yanzun fisabilillahi in banda abinki me aibun shi waccan din"
Ajiyar zuciya ta sauke idanun ta na ƙara taruwa da hawaye,"Salma yanzu ki kalle ni,ga kyau Allah ya bani,har iya kyau,ina da kyaun jiki,na kammala makarantar College of Education,aiki kawai nake jira,ga ni da samari manyan masu kuɗi,masu motoci,ina da burin auren Namiji kyakkyawa sosai,har balle irin na Novel wanda zaki ji su da kwarjini da kyau ga kuɗi,su juya yanda suke so,"ajiyar zuciya ta Kuma saukewa"nasan Baba ba wani mai kuɗi bane,amma yana da rufin Asiri,tunda duk wani bukarmu yana biya mana,amma shine wai ya rasa mijin da zai haɗa ni aure dashi sai wani bakin Fulani"nan take hawaye ya ɓalle mata.
"Ban gane bakin Fulani ba"
"Wallahi Jauro ko a cikin Fulani sai an bincika kafin a samu mai munin sa,baƙi ne shi sosai,gashi ba shida tsaye sosai,kullum cikin kaya daya yake,wata shegiyar bulun riga,wacce haɗuwa ta huɗu dashi amma da ita nake ganin shi,"
"To ai muni ba wani abu bane"
Hararanta tayi"kawai sai na nuna ma ƙawaye na shi nace ga mijina,waiyo Allah,ke kinma San Bala'in Family su Jauro kuwa Salma,wallahi tunda nake ban taba jin fitina da tashin hankali ba irin na Ahalin su,ke ko a littafin Hausa,a haka zan yi fata kutsa kai na,
Ni wallahi bana son shi,gashi ɗan ƙauye sai bakin iskanci ya tara"
"To wai a ina shi Baba ya sanshi,nasan dai ba ɗan uwanku ba ne"
"Haka ne Salma,amma duk yanda za'ayi ba zan taɓa yarda ayi wannan auren ba"
"To ko zaki bani labarin shi,dan wallahi har na matsu naga wannan Jauro"
Tsaki taja"ai kuwa da kin yi dana sanin ganin sa,kuma ni gaskiya ba ni da wani cikakken labarin sa"
Bata fuska tayi "pls mana Sumayya ɗan Allah ki faɗa min"
"Wallahi ban sani ba,sai dai in zaki ni ma da kanki,abu ɗaya kawai na sani a kanshi,shine shi ɗin mugu mugun Ɗan iska ne"
Mikewa tsaye tayi"koma dai menene zan nimo Asalin labarin"
"Da labarin sa da zaki nimo ai gara ki taimaka ki nimo min hanyar da zanbi a fasa wannan auren"
Komawa tayi ta zauna tana kallon kawar nata"Sumayya"ta kira sunan ta,
"Umm" Ta fada tana kallon ta.
"In baki shawara zaki bi?
" Me zai hana in na ƙwarai ne"
"Me zai hana kibi maganar mahaifinki,ƙila wannan auren naki akwai abinda ya hango maki wanda ke baki hango ba,kuma kun san iyayenmu suna matukar sonmu ba zasu taba yi mana abinda zai cutar damu ba,please ki bi shawarata ƙawata"
Sai da ta bari ta kammala tsaf,sannan ta zame hannun ta dake cikin na Salma,
"Ke ƙawata ce wacce muka tashi tare tun muna ƙanana har muka girma,kusan ko wani lokaci muna tare," Lumshe ido tayi ta buɗe "Alhamdulillah,na godewa Allah daya nuna min Asalin wace ke,ashe Salma ba zama amana muke ba,Ashe baki ƙaunata, kina farin ciki da ci baya na,har kike ban shawaran auren Bafullatanin Ƙauye,in Allah ya yarda kamar yanda kike min fatan Auren Jauro sai Baban ki ya aura maki mutumin da ki kafi tsana a duniya,ki ji in da daɗi,"
Kallon mamaki take mata yanzun daga kyara kayanka sai za zamo sauke mu raba,ita da shawara ta bayar ba da wata manufa ba,riko hannun ta take ƙoƙarin yi,da sauri taga ta matsar da hannun ta,
"Haba mana Sumaiya,yanzun kin min adalci kenan da irin wannan fahimtar da ki kai min,"
"Ni ma kin kyauta min kenan,kin ga ni bana son ma wata magana Salma tashi kawai ki tafi"
"Yanzun korata kike Sumayya"
Kauda kai tayi "kamawa yake yi"
Ajiyar zuciya ta sauke, tana mikewa"to zan wuce kamar yanda kike buƙata,"
"Allah ya raka taki gona"
Girgiza kai kawai tayi,ba damuwa,in dai halin Sumayya ce ai sai dai taba wani labari,ta san yanzun bata cikin daɗin zai,amma ta tabbatar da zuwa anjima da kanta zata zo gidansu bata haƙuri,ko kuma ta kirata a waya,shi yasa gara ta barta ta dawo haiyacin ta,
Tana fitowa daga ɗakin Sumayya dakin Mama ta shiga,gaisawa suka yi,
"Ya iyayen naki"
"Suna lafiya Mama"
"Kin ko ga kawar taki"
"Eh Mama,dama kuma ina son in maka magana a kanta"
Zama tayi bakin gado"zauna ina jinki"
Zama tayi a kasa"Mama ɗan Allah kisa Baba ya fasa aurawa Sumayya wannan mutumin tunda bata son shi,Mama kinga kuwa yanda Sumayya ta rame,gabaɗaya ta fita hayyacinta "
Dukar da kai tayi sai kuma ta kalle ta "ni kaina abun na damuna Salma,sai dai na rasa yanda zanyi,daga Sumayya har Mahaifinta taurin kai ne dasu,idan suka kafe akan abu sun kafe kenan,ita tace bata so,shi kuma ya rantse sai anyi,gabaɗaya na rasa yanda zan shawo kansu,ko abincin kirki Sumayya bata ci sai nayi da gaske,bansan ya suke so nayi da rayuwa ta ba"
"Sai dai mu taya ta da addu'a,sannan dazu dana shiga kokarin shan guba take,dan Allah Mama a ƙara saka ido a kanta"
Cikin tsoro ta dafe kirji "guba" Da sauri ta mike ta nufe dakin Sumayya,a zuciyar ta tana rayawa akan lallai duk yanda zata yi dole tayi domin a fasa wannan auren,tana ji tana gani ba zata yarda ta rasa yarta ba,koda kuwa sunan Baban su zata kai wurin Malami.
*🍂JAURO🍂*

~~~~~~~💞💞~~~~~~~
*2*
Salma bata jima da fita ba sai ga Mama ta shigo ɗakin da sauri tana ƙiran Sunan ta,
Zabura tayi daga kwancen da take tana durowa daga saman gado "Na'am Mama"
Tsayawa tayi a gabanta tana ƙare mata kallo,"in jin dai baki sha gubar ba"
"Turo baki tayi ta koma ta zauna" Mama shine zaki ban tsoro da wannan kiran naki"
"Kaniyarki,ina tambayarki kin tsaya min shirme,Ashe Sumaiya bakida hankali,yanzun saboda wani ɗa namiji tsinanne sai ki kashe kanki,yanzun kin min adalci kenan" Sai kuma ta saka kuka,
Ganin mahaifiyar nata na kuka ne yasa da sauri ta taso ta rungume ta "ɗan Allah Mama kiyi haƙuri,ba zan ƙaraba,na ɗauka baki fahince halin da nake ciki bane ke da Baba shi yasa,ni kuma na rasa mafita,zuciyata zafi take min shiyasa na zaɓa wannan hanyar"
"Waya faɗa maki ban fahince ki ba,a duniya a kwai wacce tafi cencenta ta fahimci ɗa sama da uwa,babu,na san komai na kuma san tunanin ki,dan haka kar ki kara yin irin wannan tunanin,dan in dai Jauro ne wannan auren kamar anyi an fasa"
Kallon Mamaki take wa mahaifiyar nata"Mama taya hakan zai faru,bayan Baba yace mutuwa ce kawai zata iya dakatar da wannan auren,kuma naga kema da ki kai mai magana kin yarda yayi"
"Ba ni nace ki kwantar da hankalin ki ba,ai in takamar shi taurin kai,bai fi karfin Malamai ba,mun riga munyi magana Hajiya Rahama,matar kansila na kasan layin nan,akwai in da zata kai ni,sha yanzun magani yanzun"
Ɓata fuska tayi tana kallon mahaifiyar nata"Mama nifa tsoron zuwa irin wannan wurin nake,gaskiya karki je"
Cikin masifa ta hayayyako mata"to shikenan na fasa zuwa,tunda dama ashe son shi kike ai dole ki ce haka,ke kika sani sai ki karata a can,ana mikin gudun wahala kina fadin tsoro kike ji,yanzun ke ko gidan Boka aka ce kije baki zuwa saboda wannan,sam ko tsari ba ku yiba,mutum tamkar wani Almajirin Ƙauye,ke kika sani"ta faɗa tana kokarin juyawa zata bar ɗakin.
Cikin sauri ta riƙo ta"na yarda,in dai har za'a fasa wannan auren na yarda Mama kije,ɗan Allah ki taimaka min"ta faɗa tana zubar da ruwan hawaye daya cika mata ido
Tsaki tayi"ni daɗi na dake saurin kuka,to ya isa,zuwa gobe da yamma zamu je"
Gyaɗa kai tayi tana kara lafewa a jikin Mama.
Ture ta tayi ta mike tsaye"ni ɗaga ni da wannan son jikin naki"
"Mama ɗan Allah mana"
"Ohh lallai yarinyar nan,kinga ni ina da aikin yi bari ma ki gani" Nan tayi waje abinta.
Ajiyar zuciya ta sauke,yayin data koma jikin gado ta jingina bayanta ta lumshe ido,