← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 49

Sashe 3

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gira daya ya daga"laifi ne ɗan na maki tayin abin arziƙi,waya faɗa maki yanzun akwai budurwa Virgin,duk yawancin ku ba in da baku leka ba,ni shawara na baƙi ko kwali nawa kike so zan saida maki,kuma zan maki ragi sosai "

Tsabar baƙin ciki bata masan sanda tace"na leka harda dakin ubanka"ta faɗa tare da rarumo wani katon dutse dake gaban zata buga masu,

Ai da mugun gudu mai Adaidaitan yaja Keken shi ya bar wurin,yayin da daga shi har me Keken suke kwasar dariya,

Bakin cikin wannan abinda sukai mata ne yasa taji gabaɗaya ta tsani fitar da tayi,dan haka tare wani keken tayi wanda zai dawo da ita gida,in da anan ta zo ta tarad da Mama da Baba suna jiranta da wata masifar.

Tana shigowa gida a tsakar gida ta iske su zaune har da Kannanta yayin da kwanukan abinci daga gefe alamun yanzun Baba ya gama cin abinci,

Dukawa tayi ta na gaishe shi,tunda tasan irin wannan ranar baya jimawa yake dawowa "barka da dawowa"

"Daga ina kika fito"

"Baba naje gidan Anty Amina ne taya ta gyaran daki"

"Da izinin wa"

Kallon inda Mama ke zaune tayi,suna haɗa ido ta kauda kai,

"Na faɗa ma Mama"

Kallon Maman yayi"kika ce bata faɗa maki ba"

Kallon Sumayya tayi,ita ma suna haɗa ido ta dukar da kai.

"Oh ta fada min amma na manta ne"

Hararan Sumayya yayi"tashi kiban wuri,ai na kusa maganin wannan yawon naki"

Turo baki tayi tana tashi ta shige daki,tsabar bakin rai a ranar kashe wayar ta tayi,

Sai kuma haɗuwar su ta biyu,wanda shima ba zata manta ba.

Jin kiran da Aisha ke mata ne yasa da sauri ta dawo cikin haiyacinta tana kallon ta,

"Wai Mama ki fito kiyi Sallah lokacin Magariba yayi"

"To " Kawai tace tana mikewa.
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko a mai damin littafi Audio ba tare da izini na ba*
*4*

Washegari da safe misalin ƙarfe takwas na safe,a lokacin ta kammala haɗa masu abin ƙarin safe,tana sharan tsakar gida,sai ga yaro ya shigo da sallamah,amsawa tayi dan lokacin ita kadai ce a tsakar gida sai Aisha dake wanke-wanke,kasancewar ranar sati ce,

"Wai ana sallamah da Sumayya"

"In ji ubanwa da sassafen nan"

"Yace ace Jauro"

"Je kace tace ba zata zo ba,idan kuma ya isa sai yazo ya jani"

Daga bakin kofar Baba taji ance"idan baki fita ba ni kuma a yau zan sa a ɗaura auren in yaso sai yaji daɗin cika umurnin ki,dan ba wanda ya isa ya dakatar dashi idan ya shigo daukar naki,koni nan ubanki ban isa in dakatar dashi ba,wanne kika zaɓa "Baba ya faɗa daga inda yake tsaye a bakin kofar dakin shi.

Ba tare data ce komai ba,ta jawo wani hijabin Mama dake saman igiya,
wuya ma ya mata yawa,har ana iya ganin suman kanta,da yake hijabin roba ne,ƙafarta silifas ne,kamar yanda take daure da zani iya kirji sai riga a sama,dan haka zanin bai gama sauka kasa ba,fuskarta kuwa yanda kasan anyi gobara haka yake,
Kai tsaye kofar gida ta nufa,

Yana tsaye a kofar gidan,sai dai wannan karon riga ce fara a jikin shi,amma daga gani ta gwanjo ce,dan har wani kaba kaba take yi,sai takalmi dai na rannan ne,wando ma dai ya canja,sai wata baƙar leda dake hannun shi,

Cikin bacin rai ta tsaya a gabanci babu sallamar,har wani huci take,gashi har girgiza take,

Kallon ta yake tun daga sama har kasa,yayin daya tsayar da idon shi a kanta,na wani lokaci,sai kuma ya dawo da kallon shi kirjinta,nan ma na wasu yan daƙiƙai,tabe baki yayi "Assalamu'alaikum" Ya mata sallamah.

Abu ɗaya ne yasa kawai ta amsa mai sallamah shine sanin muhimmancin ta,shima a ciki_ciki ta amsa,

"Me ya kawoka gidan mu da safe"

"Nazo taɗi ne mana"

Wani banzan harara ta zuba mai"a garinku hala da safe ake zuwa taɗi?

Dariya yayi kaɗan "kusan haka,kinsan me?

Hararan shi tayi tana jan tsaki,

" Nifa gaskiya zan faɗa maki,dama kallon ɗan iska kike min,amma maganar gaskiya bai dace kina ɗaurin kirji ba,saboda hakan na zubar da nonon mace,kuma kin ga ni ba zan so haka ta faru dake ba"

Kallon kirjinta tayi ta kalle shi,da sauri ta maida hannun ta cikin hijabi tana karewa"ai ba kallon da nake maka kenan ba,haka din yake kai cikakken ɗan iskan ne,in ba haka ba me yakai idanun ka wurin"

Ɗan shafa kanshi yayi"nifa ba ɗan iska bane,tunda ban taɓa iskanci ba,sai dai lokacin da naje England ne ƴan matan garin suka so lalatani,da kyar dai Allah ya kwace ni kuma....

"Kai dai ɗan iskan ne,a ina ka taɓa zuwa England,kuma ka rantse da Allah baka taɓa iskanci ba,tsakaninka da Allah"ta faɗa tana kafe shi da ido.

" Eh to ai dai iskanci kika ce ba zina ba,kuma in dai iskanci ne,a wannan lokacin ai kowa na ɗan taɓawa,kuma kema zaki iya yi"

Kallon shi take baki buɗe "amma baka da hankali Jauro,yanzun ni zaka ce in zan yi iskanci ina iya taɓawa?

" Na ga kamar bakida suma,kalli suman kankifa yanda kikasan an sude kwallan mangoro,
Ni da naso ace matar da zan aura tana da suma,amma ba komai nayi maneji a haka,sannan zan siya maki wani man suma da naga ana talla a online,"

Baƙin ciki ne yasa tace"ka fara sai ma kanka sutura tukun na kafin ka yi maganar man kai"tana gama fadar haka ta shige gida cikin jin haushi,tana jin kiranta da yake yi mata da sunan data tsana wato Sumy Baby,ko juyowa ba tayi ba,
Tana shiga cikin gida kai tsaye dakin Baba ta shiga da kuka ta tsugunna a gaban shi"Baba ɗan Allah kamin rai ba na son Jauro,bana son na aure shi,dan Allah,na yarda koma waye ka aura min ko da Almajiri ne amma banda Jauro"ta karasa fada tana fashewa da kuka sosai.

Kallon ta yayi cikin Alamun rashin wasa yace"nariga na yanke hukunci a kan haka,kuma shi ɗin ba mutumin banza bane ya cika duk wasu sharuɗɗa irin na wanda ya dace aba mutum aure,dan haka ki saka zuciyar ki a inuwa ki kuma hakura dan aure ba fashi,tashi ki ban wuri"

"Baba dan Allah" Ta faɗa tana ƙoƙarin dafa ƙafar shi,
Wani tsawan ya daka mata"tashi ki ban wuri,mutuniyar banza,ni na haifeki nasan girmanki da burinki har zuwa yanzun,dan haka shi yasa na zaɓa maki wanda naga yafi dacewa dake"

Ganin yanda yayi maganar ne yasa da sauri ta tashi ta bar dakin tana kuka,
A bakin kofa suka ci karo da Mama wacce take tsaye tana jinsu,dan haka jan hannun ta tayi suka shiga dakin ta,
Cikin masifa ta ce "me nace maki?ba nace ki bari zuwa anjima akwai inda zanje ba,wai me yasa Sumayya kike da gajin haƙuri"

Sallamar Aminu yaron makociyarsu ne ya dakatar da su,gaida Mama yayi sannan ya miko mata wani bakin leda "Mama gashi wai aba Sumayya inji Jauro"

Sai da ta yi kamar ba zata karba ba,sai da ya ƙara mai maita abinda yace sannan ta masa,ba tare da tace mai ko mai ba ya wuce,ganin ya tafi ne yasa ta buɗe ledan,
Wani dogon tsaki taja tana wurga ledan ɗakin ta,
"Kai wannan mutumin akwai matsiyaci,yanzun Sumayya ya rasa me zai kawo maki sai ledan Burodi sinki biyu,sai kace wasu Fulani,gaskiya dole in tafi wurin wannan malamin dan ba zan iya gaiyar Fulani ba"kallon yar nata tayi,yanda duk tayi wani sanyi," Kinga tashi kije kiyi wanka ki huta,sannan ki cire komai a ranki banda tunani "

Jinjina kai tayi"to Mama "sannan ta tashi ta wuce,ruwa ta diba tayi wanka sannan ta koma ɗakin ta,ranar anan ta karya,gabaɗaya ta rasa meke mata daɗi,domin a duk lokacin data tuna shi bata taba ganin dacewarsu sai dai ma ta ƙara ganin wani makusa nashi,

Haɗuwar su ta biyu dashi,bayan kusan sati da haɗuwar su a cikin Adaidaita,harma ta manta dashi,amma a duk lokacin data tuna abinda ya mata shida ɗan Adaidaita sai ta tsine mashi,

Ranar Mama ce ta aike ta gidan Aunty Aminatta amso mata wasu kaya,ta je ta amso kayan sai tayi tunanin me zai hana ta shiga kasuwa ta siya Ɗan kunni,tun da gidan da kasuwa babu nisa.

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su ɗaura min littafi a shafin su ko ya mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*5*

A Babban shagon siyayya ta tsaya wanda naga an rubuta B.S Store,dan bata cika son tayi ta zagaya ba,gara ta tsaya wuri ɗaya kawai ta siya,
Shagon babban shago ne sosai wanda ba abinda basu siyarwa,
Cikin yanga da jan aji ta shiga shagon wanda ko yaushe baka raba su da jama'a,
Layin da ake saida ƴan kunnaye ta nufa,cikin natsuwa ta cire wanda take so,sannan taje wurin biyan kuɗi ta biya aka saka mata a leda,
Har ta kusa fita bakin ƙofar shagon sai ji tayi ance "Malama muga ledan dake hannun ki"

Dago kai tayi ta kalleshi sannan ta kalli ledan kayan da Aunty Amina ta ɓata ta kaiwa Mama,

"Ban gane kaga ledan hannu na ba?

" Saboda muna zargin kamar akwai abin mu a ciki"

Daga ɗayan ɓangaren taji ance"Sani caje ta da kyau damun ƴan matan yanzun ɓarayi ne,haka jiya daga gaiyatar wata yarinya shan shayi daki na ta sace min DVD da nake kallo dashi"

Wani Alhaji dake zaune ne ya tuntsire da dariya"kai Jauro in bada kana ɗan iska me ya kaika gaiyatar mace dakin ka wai shan shayi,dan ka mai da mu ƴan iska"

Jin sunan da aka kirashi dashi yasa nan take ta tuna shi,domin ba zata taba mantawa da mutumin da ya mata tayin siyan Condom ba,

Shafa kai yayi yana dan dariya "ai wato Alhaji in faɗa maka jiya ne an dan yi sanyi shi yasa na gai yace ta,ban san ashe yarinyar nan barauniya bace,ko yanzun inda zan ganta wlh sai ta biya ni Sidi na"
Chapter 3 · 0% Book details