← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 49

Sashe 19

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baffa bada waɗannan kudin abu mai sauƙi ne,dan haka a dauki shanaye na dake wurinka guda uku a sai da shi sai a bada nawa kuɗin"

Abin mamaki nan take sai ga fuskar Baffa Bube ya hade kamar hadarin gabas,cikin bacin rai yace"wannan wani irin maganar banza ne haka kake faɗa Jauro,to in dai Shanayen ka na wurina ka saka ma ido to sun kare tun tuni "

"Sun fa kare,ni da ko daya ban taba amsa ba a wurunku,ba mutuwa su kayi ba sannan yanzun ace sun kare?

Cikin inda_inda yace" To me kake son in ce maka,lokacin kana makaranta wannan mutumin yazo wai kana buƙatar kuɗi,to shine na keta saidawa ina bashi kudin yana tura maka"

"To na wurin Baffa Sanda fa?

" Kai ina ga da wuya in za'a samu abin da ya rage a hannun shi,"

"Yanzun kenan ni dai ne a gidan nan ba ni da ko ƴar kaza,?
Ya faɗa yana jin zafin abin a zuciyar shi,duk da dama ya riga ya saka a ranshi ba samu zai yi ba,amma kuma jin haka daga gare su ya fi mashi zafi,idan yayi duba da ko yaro ƙarami in dai a gidan aka haifeshi to yana da abin kiyo,
Girgiza kai kawai yayi " In dai haka ne Baffa sai dai ince Allah ya kyauta,dan ba ni da ko dubu hamsin din da zan bada balle dubu dari biyar,"

"To shi kuma auren da kace zaka yi fa,da wani kuɗi zaka yi su? Baffa ya tambaya cikin yanayi na rashin damuwa,dama fargabanshi daya kar Jauro ya tada rigima akan bai yarda ba sai sun fito mai da dabbobin shi,
To ya gode Allah tunda yaron bai dau abin da zafi ba,

"Dama akan dabbobina na saka rai,amma tunda abun ya kasance haka,kuma ina son yarinyar,zan roki mahaifinta akan ya Bani bashin aurenta in yaso daga baya na bata kuɗin Sadakinta"

"Yanzun kai Auren bashi zaka yi,wai duk ina kuɗin aikin kwamnatin da kace kana yi a cikin gari?

" Baffa ko zaka aramin ne?

Tsaki yaja ya tashi "kaje dai ka sami Malam Liman na tabbatar idan yana da shi zai baka"ya faɗa yana barin wurin.

Girgiza kai kawai yayi ya nufi gidan Malam Liman domin sanar dashi yanda suka yi da Baffa Bube......

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*26*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Duk da cewar lokaci ya ja bakaman da ba,amma Malam liman bai bar zama yana koyar da ɗaliban shi ba,
Dan haka samun wuri yayi ya zauna a cikin Almajirai har aka idar karatu suka yi Addu'a suka watse,

Sake sabon gaisuwa suka yi da Liman,inda yake faɗa mashi yanda suka yi da Baffa Bube,

"Hakan da kayi shine daidai Jauro,domin shi Gado ba abin fitina ba ne,yau ina asalin wadanda suka tare dukiyar suke?sun tafi sun bar ta ba dan suna so ba,to kamar yanda suka tafi suka bar ta muma haka zamu tafi mu barka,ko kuma ita ta tafi ta bar mu,na gode ma Allah da baka tada hankalin ka ba akan haka,Allah kuma ya ƙara hore maka naka,"

"Amin Malam"

"Batun niman Auren ka kuma,In Allah ya yarda jibi Laraba zamu je akai kudin sadakin,"

"Amma Malam kana ganin babu matsala idan akayi komai bayan ba'a sake Baffa Sanda ba,ba zasu kullace ni ba"

"Ina ce a gabanka ya faɗa kayi auren ka kawai,kuma in dai ba kayi karya ba ai inaga ba matsala,ko za ku wani wasa ne?

Da sauri ya girgiza kai" A'a dan yanzun ba ni da wasu kuɗi a kasa saboda na kashe kuɗi sosai wurin turo takardu na UK,"

"To ba damuwa,hakan yayi Allah ya taimaka"

"Amin" Ya fada ya na yi mashi sallahma.

_______kamar yanda Malam liman ya tsara haka kuwa aka yi,domin an kawo sadakin Sumayya wanda Baba ya karba dubu dari,sai dukiyar aure kuma suka bada dubu dari uku,
Ranar Baba bakin shi har kunne,domin bai ɗauka zai samu koda rabin haka ba,dan su sun bashi dukiyar aure ne bisa Al'adun su na Fulani,
An kuma saka biki nan da sati ɗaya,wanda ya kama ranar Juma'a.

Kamar yanda bai ba Sumayya ko sisi ba haka ita ma Mama bata ga kudin ba,illa dai faɗa mata da yayi ga kudin da suka bada,amma ya ba maman Momy ta siyo mata wasu yan kayayyaki na mata na buƙata,dan tace a kwai in da zata siyo komai cikin sauki,a rahusa mai kyau.

Ita dai Mama har ya gama magana ba tace masa ci kanka ba,har ya kammala fada ya juya zai tafi,sai kuma ya juyo ya kalle ta ganin yanda tayi ko in kula da shi"to ke baza kice komai ba ne?

"Allah ya sanya Alkhairi"

Waro ido yayi"kawai,"

Cigaba da ninke kayan Aisha da aka wanke tayi,

"Abinda kawai zaki ce kenan,"

Murmushi mai sanyi ta sakar mai,"me kake son in ce bayan addu'ar da nayi,so kake kaga ina tashin hankali ina hauka,shin koda nayi hakan zai sa ka fasa yin abinda kayi niya ne?A'a fa,dan haka ni na barma Allah komai,duk abinda yayi a kansu daidai ne,na tabbatar da ba zai bari nataɓa jin kunya in sha Allahu tunda nayi imani dashi,kuma ya'ya na ba zasu taɓa wulakanta ba,in dai Aure ne a je ayi,ko gobe kaga dama a dauro ma Sumayya aure,Allah ya basu zaman lafiya"tana gama faɗar haka ta tashi ta bar mai dakin,

Jikin shi ne yayi sanyi domin bai taɓa tsammanin haka daga gare ta ba,a tunanin shi idan ya faɗa mata zata kusa haukace mashi,sai gashi ta bashi mamaki,
Shi kanshi wani lokaci idan ya kalli fuskarta ya kanji a ranshi bai mata adalci ba ita da ya'yanta,a duk lokacin da yayi niyar kure ta,sai ya ga abin mamaki,domin sai ta nuna mai babu komai,koda kuwa ita aka cuta,sai tayi haƙuri,
Ya mata abubuwa da yawa wanda ya kamata ace ta bar shi,sai dai har yau wani abin yana mashi nauyi a zuciya,yana ganin kamar har tana kallon shi dashi taki mashi magana ko ta tuhume shi akan hakan,shi yasa wasu lokutan yake jin haushin ta dan a ganin shi ƙeta ne take mai,ta bar shi na nauyin zuciya,domin tun daga lokacin da ya aure kawarta Aminiyar ta nar suka zauna zaman wata bakwai ba tare data san ƙawarta ce ya aura ba,duk da dama ba gida ɗaya suke ba,sai bayan wata bakwai ne take samun labara abakin iyayen ita Maman momy wanda suma basu san bata sani bas
Har izuwa rana ta yau bata taba buɗe baki ta tuhume shi akan haka ba,
Son zuciyar shi ne ya jawo komai,sai dai gaskiya ba yajin zai iya mata adalci,yasan zata ci gaba da hukuri dashi har zuwa ƙarshe tunda tana son shi(har kaban tausayi Baba) tashi yayi ya karkade rigar shi ya bar gidan.

Kuka tayi sosai a cikin dakin da ta shiga,ji take kamar numfashin ta zai ɗauke saboda yanda ta ji wani abu yazo ya mata tsaye a dai-dai saitin zuciyar ta,baƙin ciki take ji da kunci mai daɗi,ta rasa wanda zata faɗa ma damuwarta ta ji sauƙi,ya'yan ta ne kawai take dasu,ba zata iya faɗa masu ba,saboda ta san ko wannen su na fama da tashi damuwar wanda ba zataso ta ƙara masu da nata ba,sai dai ta san komai lokaci,ita dai fatanta daya ne,shine Allah yaji tausayin ta ya rangwanta mata,ko da takan Sumayya ne,yasa ta samu kwanciyar hankali,domin samun kwanciyar hankalin daya daga cikin su tamkar rage wani bari ne daga cikin damuwarsu.

________zaune take ta rabka uban tagumi tayi zurfi cikin tunani,gabaɗaya ta rasa ne ke mata daɗi a duniya,ji take tamkar duk wani jin daɗi na rayuwar ta ya yanke,duniyar ma juya mata yake,

Jin an sauke mata hannu ne yasa ta sauke ajiyar zuciya ne nauyi,

"Haba mana Sumayya,so kike ki hallaka kanki da tunani,karki manta da komai yayi zafi maganin shi Allah,pls ki rage wannan tunanin da kike yi"

Kara sauke wani ajiyar zuciyar tayi wanda a yanzun ya biye mata jiki,"Salma ba za ki gane bane,amma duk yanda naso na cire abin a zuciya ta na kasa,ba wai auren nan ne bana so ba Salma,ba kuma batun shi ne kaɗai ke damuna da kuma tayarmin da hankali ba face lamarin Baba da Mama,kullum lamarin Baba ƙara yin gaba yake,to ya zan yi,ɗan sana'ar da Mama ke yi sama_sama duk jarin ya kusa karewa,ƴan uwanta har yanzun ba wanda yace komai game da wannan auren,ita kuma ba wai tana da shi bane,ni dai nasan kawai sai yanda Allah yayi da rayuwata"......

Kuyi haƙuri da wannan,in sha Allah zan kara yawan page

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*27*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

"In dai haka ne kam dole ki damu,ba ma ɗan kaɗan ba,amma ki sani damuwa baya maganin komai sai dai ma ya illatar dake,wanda hakan zai ƙara ma Mama damuwa da tashin hankali ne,dan haka Addu'a ne kawai mafita"

"Allah ka fitar dani"ta fada tana mikewa" Salma yaushe zaki shigo?

"Zan shigo amma sai zuwa jibi,dan gobe zamu fita da Inna,amma fa ki faɗa ma Jauro ya ajiye mana kuɗin ƙawaye"

Tsaki taja"in dai wannan ɗan iskan ne dai-dai yake daku ai "

"To ki bani numbar shi,dan wallahi dole mu kwanci wani abu a hannun shi duk makon shi, kuma sai ya mana wasa dan party zamu haɗa"
Chapter 19 · 0% Book details