← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 49

Sashe 8

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shiga shiyan su da sauri ya karasa inda take kwance yana kiran sunan ta,sai dai wannan karon ko motsin da take yi da ido bai ga tayi ba,
Girgizata ya shiga yi"inna,Inna,ki tashi ga magani na amso maki,gashi ki tashi ki jika,Inna Mari tace kinsan yanda ake amfani dashi,"tashi yayi ya fita tsakar gidan su inda take ajiye kwarya,daya ya dauka ya dawo inda take kwance "Inna ga kwarya na dauko tashi ki jika maganin kisha" Nan ma shiru babu amsa,

Kallon ta ya tsaya yana yi kamar mai tunani,ya dauki lokaci mai tsayi yana kallon ta,kafin a zuciyar shi ya raya mashi ƙila bacce take yi bari ya jira har ta tashi,sai ya bata maganin,nan ya ƙara ɗaukar ƙwaryan ya rungume yana kallon ta,
A wannan lokacin ne kuma wani barci mara daɗi ya ɗauke shi mai tattare da yunwa.

Ana cikin haka ne Baffa Dottiya ya dawo misalin karfe biyar na yamma,

Tunda ya doso cikin gidan gaban shi ke faduwa,sai dai bai kawo komai a rai ba,domin duk kwanan nan abun da yake yawan ji kenan,

Yana ɗaga labulen dakin wani irin karnin jini ne ya daki hancin shi wanda yasa da sauri ya saki labulen ba tare daya shiga ba,dan shi mutum ne mai kyankyami baya shiri da ƙarni,
Halima kuma macce ce mai tsafta sosai ga son kamshi,ko yaya ne ba ka rabata da irin turaren nan na mutanin da wanda suke amfani dashi,

Mamaki ne ya kama shi,dan haka sai bai shigaba ya tsaya a wurin yana kiran sunan ta,wanda hakan ne ya tayar da Jauro,
Missike ido yayi yana kallon ta,har yanzun dai barcin take yi,dan haka zuwa ya ƙara yi inda take yana jijjigata tare da kiran sunan ta,"Inna ki tashi Baffa ya dawo,gashi can yana kiran ki"ganin wannan lokacin ma bata motsa bane yasa kawai ya tashi ya fito,

Kallon shi Baffa yayi "Innar ka fa?

" Baffa tana daki,tun Dazu nake tada ita kuma taki tashi,yunwa nake ji"

Ji yayi gaban shi ya yanke ya ƙara faɗuwa,
Bai ce mashi komai ba ya kutsa kai cikin ɗakin,sai dai a irin halin da ya iske matar tashi a ciki ne yasa saura kaɗan jiri ya yarda shi,
Har ji yake numfashin shi na ƙoƙarin daukewa,gaɓoɓin jikin shi shi sun sake,
A hankali kamar wanda ke tsoron karasawa wurin da take ya isa,
Hannun ta ya ɗaga,sai dai yana sakewa hannun ya faɗi ragaf,
Duk inda yake tunanin zai ji numfashi a jikinta ya taɓa sai dai dip babu alamunsa,wanda dama tun ganin farko daya daura ido a kanta ya tabbatar da cewa yayi rashi babba,
Kallon ɗan nashi yayi,"je ka kira mutanen gidan nan"

Harya juya da sauri ganin Baffa shi na hawaye,sai kuma ya dawo yana kiran sunan shi"Baffa dazu naje na faɗi ma Innar Ɗan Fodiyo tazo Inna ta ba tada lafiya kuma a kwai jini a dakin mu shine taki zuwa kuma harda Marina tayi,na san yanzun ma idan na je dukana zata yi,ita kuma Innar Yabale tace idan ta gama abinci zata zo"

Ji yayi wani irin hawaye masu raɗaɗi sun sauko mai,menene amfanin irin wannan rayuwar,me amfaninta,ace maka mutum na zubar da jini tun ƙarfe daya na rana,yaro yaje ya faɗa maku amma ba wacce ta iya cewa bari in Leko in duba kai koda Akuyar ka akace tana zubar da jini ka je ka gani balle a ce mutum,haba,haba,wannan rashin imani ya ɓaci,
"Ka fada ma Inna Mari kuwa"

"Na faɗa mata tace ba zata iya zuwa ba saboda ƙafarta na ciyo,sai dai ta bani magani na kawo ma inna ta jika,sai dai ina ta tada ita amma bata tashi ba"
Bai san da idon fassaran da zai kalle ahalinsa ba,bai san da wani kalan suna suka dace ya kira suba,sai dai abu ɗaya,shi ne yana masu fatan tarwatsewa tankar yanda suka tarwatsa rayuwar shi,suka ki kula matar shi da danshi alokacin da suke nimam taimako,
Shi kuma insha Allah sai ya basu mamaki,ba zai nima taimakon su ba koda da menene,

Tashi yayi ya dauki fura ya dibo kindirmu a inda suke ajiyewa ya dama na ɗan na shi,
Yana gamawa ya haɗa wuta ya saka ruwan dumi,sannan ya watsa magarya aciki tamkar yanda wani malami ya nuna masu a lokacin da mahaifin su ya rasu,kuma ya masu bayani yanda zasu mace,dan alokacin shine ma ya tambaya in macece ya ake mata,

Sai da ya gusar da duk wani najasa dake dakin dakuma wanda ke jikin ta,sannan ya mata wanka tas,
Ya ce ma Jauro "zauna kusa da Innar ka bari in je in dawo"

Kallon Baffan na shi yayi "Baffa yaushe zata tashi"

Guya kai yayi ya share hawayrn shi"karka tada ita kaga ba tada lafiya bari naje na dawo,

Yana fita gidan limamin dake basu sallah yaje,dama ba'a rasa likafani a wurin shi,dan haka faɗa mashi yayi,abinda ke faruwa dashi har izuwa mutuwar Matar shi ya karasa faɗa yana fashewa da kuka, "kamar yanda suka ki kula ɗana alokacin daya je niman taimakon su,ina fata kar Allah ya taimaka masu a ko wacce hanya,ya bar su da iyawarsa,ya tarwatsa su"

Da sauri malamin ya rufe mai baki"haba Dottiya me yasa kake irin wannan addu'ar ga ahalin ka,kaga irin haka bai da kyau,ko ba komai ƴan uwan ka ne hakan be kama ta ba"

"Malam yanzun damuwa ta daya,shine Jauro,wani irin rayuwa ɗana zai yi,bana son dana ya tashi da irin wannan hali nasu,bana so yayi koyi da dabi'un su,da nasaka raina akan mahaifiyarsa ce,kuma sai gashi ta riga tafiya ta barni"

"Me kake faɗa haka ne Dottiya,insha Allah kana tare da ɗan ka,kai zaka reni abin ka, "

Girgiza kai yayi,yana ƙara zubar da wani hawayen wanda yake jin zafin shi har cikin zuciyar shi,"naso haka,naso ace hakan zai kasan ce,sai dai kuma...... "

Sai yayi shiru ya kasa karasa fada,rike hannun malamin yayi"ɗan Allah ina rukon wata Alfarma a wurin ka"

Cikin tausayawa yace "ina jinka Dottiya"

"Malam dan Allah ina rokan ka dauki Jauro acikin ɗaliban da kake koyarwa,ka tsaya mashi yayi ilimin addini,karya zamo kamar mu dan Allah Malam"

Jinjina kai yayi"na maka Alkawari Dottiya,insha Allah zan tsaya masa ya samu ilimi addini yanda ya kamata,ka kwantar da hankalin ka,kaga mutane har sun taru domin na aika daya daga cikin yarana suje suyi shela za'a sallar gawa a gidan ku,taso muje a samu a kai ta ɗakinta na gaskiya kafin magriba tayi"......
*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*11*

Duk wannan abunda ake yi matan gidan ba su sani ba,har Matan liman su biyu suka zo suka taimaka mai aka saka mata sutura,

Shine fa Ɗan Fodiyo yaje cikin gidan su yake fadama Binta yaga Baffa Dottiya na kuka,
Sai ga Kande ta shigo da gudu tana ihun kira Inna,
"Waiyo jama'a mun shiga uku Halima ta mutu,Inna,Inna"

Da sauri ta fito ɗaki har zanin jikinta na faduwa "ke wata Halima ce ta mutu?

Kuka ta fashe dashi tana zama abakin dakalin wurin tare da daura hannu a kai" Innar Jauro,waiyo Allah kaicona dazu yaron nan ke bina akan na zo na duba Uwar shi tana Zubar da jini,amma ban kula shi ba nace ya bari sai na gama girki,ashe dai mutuwa zata yi "ta karasa faɗa tana fashewa da wani sabon kukan" Gashi can yanzun za'a fitar da ita,saboda bakin hali irin namu ko sanar damu abinda ke faruwa Dottiya bai yi ba,sai makota ya gaiyato suka taimaka mashi"

Inna Mari da sauri ta doshi hanyar waje har tana tuntuɓe,
Koda ta shiga shiyan Halima har an fito da gawar,
Kuka ta saka tana rike makaran"yanzun shikenan Halima tafiya zaki yi ki barmu,Allah sarki mutuniyar Arziki dana sani dazu ai koda rarrafe ne dana gangaro,ashe bamuda rabon ƙara ganin juna ne"

Dottiya ne ya kalle wadanda suka taya shi daukar makaran"kai mu tafi dare na yi "
Ai kuwa cire hannun ta daya yayi daga jikin makaran sukayi gaba da ita, zama tayi a wurin ta dafe kai domin ba karamin sanyi jikinta yayi ba yau,har balle irin kallon da taga Dottiya na mata,tabbas tasan bata kyauta mai ba a matsayin ta na uwa,bai dace ta tsaya a bangare daya ba,bai dace a lokacin da yaro yazo mata da maganar mamar shi na zubar da jini taki sauraren shiba,yanzun wani irin kallo mutane zasu mata,ita kan da tasan mutuwa Halima za tayi wallahi da taje ta ganta.

A waje kuwa cikin aminci aka yiwa Halima sallah sannan aka kaita gidan ta na gaskiya,
Allah sarki Dottiya sai da aka daga shi daga jikin kabarin ta,

Kwana uku akayi zaman makoki wanda duk lokacin yana manne da ɗan shi,duk zaman da akayi ba laifi yana tare dasu Bube suna karɓar tare,sai dai matan duk wacce ta mai gaisuwa idan ya amsa so daya baya kuma amsawa har ta da Inna,
Sai dai abin mamaki duk wannan abinda ya faru Binta ko sau daya bata taɓa lekawa da sunan gaisuwar rasuwar Halima ba,har ta su Badejo dake aure wani gari sun zo gaisuwa amma ita ko kofar shiyan Halima bata leka ba har yanzun da nake magana.

Bayan sadakan uku ne shanayen Baffa Dottiya suka iso da daddare,
Fita yayi ya same su,dan lokaci kusan ƙarfe ɗaya da rabi ne na dare,
Zama yayi kusa dasu yana masu bangayi,
ɗayan ne mai suna Manu yake tambayar shi "ina uwar ɗaki na"dan sunan da yake kiran Halima dashi kenan,yana dariya yace" Yanzun nasan ta kusa haihuwa,Jauro ya samu kani ko ƙanwa"

Daya daga cikin su ne yace"to na dai rigaka Manu in dai mace ce ni za'a ba auren ta"

Su biyun dariya suka yi,dama kuma su huɗu ne masu masa kiyo to biyu sun kwanta dan lokacin biyu tayi,

Ganin ya dukar da kai yayi shiru ne Manu ya ce"Uban daki na ni kam ba kada lafiya ne naga wallahi duk kayi wani irin rama kayi baki,"
Chapter 8 · 0% Book details