← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 49

Sashe 21

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru kawai tayi riƙe da waya a hannun ta,wannan wani irin mutum ne shi haka mara imani,haba sai kace ba yar shi ba,
Komawa tayi kusa da su Aunty Rahima ta zauna wacce ke tambayarta ya suka yi dashi,nan ta kwashe yanda suka yi ta faɗa mata,sai cewa tayi"ni da ban fito da kuɗi ba,sai dai in zamu kira Wasila ta turo kuɗin "

"Ke ma dai kinsan fitowar dubu biyar daga Aljihunta ba abu me sauki bane,tunda ba wai tana da shi ba ne"

"To kuɗin da muka haɗa mata fa,naga dai ba wani abun da aka siya da shi"

"To abincin da kika ci fa,ai dashi akayo cefane a kayi girki"

Tsaki taja tana turo baki"Allah ya rabumu haɗa jini da zuri'ar tsiya "

Wata Nus ce suka ga ta taho wurin yayin da wasu Maza su uku ke biye da ita,"gasu nan "Nus din ta faɗa tana nuna su.

Daya daga cikin su wanda yake haɗaɗɗe a cikin su,kai daka ganshi kaga kalan ƴan gayu,ya matso in da suke" Mama ina wunin ku"

Cikin sakin fuska suka amsa,yayin da sauran ma suka gaida su,sai dai su din kam ba laifi,duk da ba kamar ɗayan ba a wurin wayewa.

"Mama ni sunana Muntaz,abonki Jauro,sai wannan shi kuma Muhammad,da Abdullahi,dukkanin mu abokai ne,dama mun je gida ne daukar Amarya shine Baba ya sanar da mu abinda ya faru,Ya jikin nata?

" Jiki da sauƙi,an samu ma ta farka,ta dan samu barci ne amma yanzun zan tada ita sai mu je"cewar Aunty Rahima.

"No just live her,idan ta tashi sai mu dawo"

"Ku dai ku jira mu a waje"

Amsawa suka yi suna fita don su jira su ɗin,

"Aunty ga dubu biyu dake hannu na sai a haɗa a bada kudin maganin"Amina ta faɗa.

Harara Yaya Babba ta zuba mata" To a cikin mu wa kika ga ni da kudi,gara in ki nada sauran ma ki fito dashi mu tafi"

"Wallahi Aunty ba ni da shi,iyakar kuɗin kenan"

Kafin ta bata amsa ne Nus ta katse su tana ajeye masu Ledojin magani a gaban su"ga magungunan ta,an rubuta yanda zata sha kowannensu a ciki,Allah ya kara sauki"ta fada tana juyawa.

Da sauri Aunty Rahima ta tsare ta"To ai ba mu biya kuɗin maganin ba naga kin kawo mana magani "

"Ai waɗannan samar dazu sun biya kuɗin komai,dan haka kuna iya tafiya,sai dai ita mara lafiya ta yi ƙoƙari ta ci abinci kafin tasha magani"

"To mun gude"

"Kai Alhamdulillah komai yazo mana da sauƙi,Allah mun gode maka" Cewar Amina cikin farin ciki,dan dama har ta fara tunanin ta ina maman su zata fara.

Ta da ita Aunty Babba tayi,ba dan taso ba haka ta tashi da taimakon Amina,dama kuma ba barci take yi ba tunda ta farka duk abinda suke yi tana jinsu,
Suna fitowa a harabar Asibitin suka same su a tsaye jikin wasu lafiyayyun mota,Muntaz (ɗan Alhaji) shi ya nuna masu motar da zasu saka Amarya,suna ƙoƙarin shiga ne sai ga Salma ta shigo Asibitin wacce ta sauka saman abin hawa,
Amina ce ta kwalla mata kira,dan haka tare da ita aka tafi,

Kamar yanda Jauro ya masu kwatancen gida haka suka bi kwatancen har ƙofar gidan wanda da su Amina sun san gidan tunda jiya sun zo sun kawo kaya,

Gidan ƙaramin Flat ne mai dauke da babban falo sai daki daya da bayi sai kuma tsakar gida da kicin a tsakar gidan,
Ba laifi sun samu tarba daga yan gidan su Muha da Malam Liman,
Abinci kuwa mai rai da lafiya aka basu wanda daga ganin shi kasan basu suka girka ba,yaji Manya-manyan kifaye da naman kaji,sunci sun ƙoshin dan su Yaya Babba har da kullawa a leda,sai bayan sallar magariba suka tashi zasu tafi,nan kuwa ta saka kuka ta riƙe Amina da Salma,suma kuma kukan suka saka dan ba ƙaramin tausayi ta basu ba,dan har yanzun jikinta da ɗan zafi,kuka take sosai tana roƙonsu akan kar su tafi su barta,
Yaya Babba ce ta fisgesu"ke bansan Iskanci,kowa da kika gani haka aka masa,kuma yana ji yana gani yake rabuwa da dangin sa,yanda naga kina da wannan taurin kan wallahi ki kama kan ki,idan ki kaje kika yi abinda zai saƙo ki gida to wallahi kinsan halin uban ki, Gara ki kama kan ki,kai ku tashi mu tafi mana munafukai "

Duk tashi suka yi suka fita sumi_sumi suna waiwayenta har suka bar gidan.

Su Muha ne suka kai mai da su har sai
Kofar gida,yayin da Ɗan Alhaji ya ba Yaya Babba dubu goma,Aunty Rahima dubu goma,Aunty Amina dubu goma,sai Salman da take kawar Amarya basu ma san ko nawa aka bata ba,
Ko kofin ma su gama juya kudin harsun ja mota sun wuce,
Ikon Allah,ba karamin mamaki da jin daɗin suka yi ba,haka suka rinka faɗa wai Abokin mijin Sumayya ya basu kuɗi,yaya Babba har da cewa Ohh dama ace shi ta aura ai da sun haye,

Su kuma yan tarbar Amarya su Yaya Babba na wucewa suka kara share gidan tas suka kintsa komai kafin su tafi,dan mota biyu manya aka masu haya wanda zai kai su har cikin Ruga,suma kuma Ɗan Alhaji ya masu abin arziki sosai wanda yasa ba karamin daɗi suka ji ba,dan ko da suka zo sun tadda manyan kulolin abinci ne daga cidan su ɗan Alhaji.

Bayan tafiyar su ne taji gidan ya mata shiru sosai,yaye lullubin dake kanta tayi tare da share hawayen fuskarta tana kare ma dakin kallo,
Dakin gabaɗaya yaji tais sai katifar da take zaune a kai,sai Aƙwatin ta dake gefe,babu durowar saka kaya balle gado,kai koda ɗakinta na gida gadon sun tsufa amma dakin yafi wannan kyau,dan wannan yanda kasan dakin Tazuro haka yake

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*29*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

*not edit*

A hankali ta sauko daga saman gadon tamkar mai tsoron taka kasa haka ta nufe falon,
Shima dai Babba ne sosai dan zai iya cin kushin saiti daya har da ƙari,sai dai babu komai a cikin shi,ajiyar zuciya ta sauke ta koma cikin dakin dan tana son tayi sallar Isha'i wanda bata samu tayi ba,

Bandakin ma a wanke yake tas,sai dai daga dukkan alamu an saka mashi sabon tas ne,ga kuma botikan wanka harma da ƙaramin famfo a ciki,
Kunna fanfon tayi ta tara buta sannan ta daura Alwalah,tayi sallar,

Bayan ta idar ne ta kwonta a nan saman dardaman,dan yafi mata sauƙi akan ta kwanta kan wannan gadon,
Koda aka zaunar da ita dazu daurewa kawai take yi,domin bala'i zarni yake,ga filo duk warin miyan barci,kai Allah yama Maman Momy yanda taso tayi da ita,

Jin an buɗe ƙofar an shigo da sallamah ne yasa ta kara rufe ido zana lunkumewa gabanta na faɗuwa jin muryar shi,Allah yasa ba zai ce mata komai ba,dan wallahi ba zata taba yarda da mutumin da bata so ba,
Jinshi tsaye a kanta ne yasa ta kara matse ido,

"Ni dai nasan ance idan kayi aure da kashigo dakin matarka zaka ganta zaune saman gado da lulluɓi tana jira ka yaye mata,to ni me yasa na ga tawa a kwance,kenan hakan na nufin a shirye take jira kawai take na fara cire mata kaya"

Wani irin zabura da tayi tana mikewa zauna har tana bangaje shi,domin yana kusa da ita ne a tsaye,
Da sauri ya matsa baya yana kallon ta baki buɗe,

Matsawa baya tayi tana kyara zaman hijabin jikin ta,

Bata fuska yaye"ke me haka,wai ni ya na ganki haka ne Sumi Baby?

Harara ta zuba mai,tana kauda kai,

Ajiye ledan dake hannun shi gefe yayi ya shiga bayi,mintuna kaɗan kuma sai gashi ya fito,kallon ledan daya ajiye yayi,yana nan yanda yake,fita yayi sai gashi kuma ya shigo da plate a hannun shi,ajiyewa yayi ya buɗe ledar tare da fitowa da lafiyayyen gasasshen kaza wanda ya ji kayan lambu,
Ɗaukar plate ɗin yayi ya ajiye mata a gabanta tare da zama ya na fuskantar ta,"ga nama ki ci sai ki sha magani"ya fada yana buɗe mata goran drink.

Duk da tana jin yunwa amma ita ba mahaukacin kare bane ya cije ta da zata ci Kazan Amarci,"ba zan ci ba"

Ɗan shiru yayi na ɗan wani lokacin yana kallon ta kamar mai nazarin ta,sai kuma yace"ki kwantar da hankalin ki ba abinda zan maki,tunda ba kida lafiya,bancin haka na san ma da kanki zaki nime ni in dai ni ne"

Cikin jin haushin maganar shi tace"Allah ya tsare ni in nimeka da kai na"

"Oh haka kike gani?to karki manta na faɗa maki ni bana ra'ayin zama da mace na har abada,da zaran kin haifamin yara biyu zuwa uku zan sallame ki na riƙe ya'ya na"

Wannan karon juyowa tayi da kyau tana fuskantar shi cikin mamaki tace"to me yasa ka aure ni in ba kason zama dani har abada "

"Saboda ya'ya na"

"Wasu Ya'ya?

," Wanda zaki haifar min,kin ga,shi yasa nace ki kwantar da hankalin ki in dai ni ne,duk lokacin da kika shirya bari na,ko kika samu wanda kike so,to ki haifamin ya'ya na biyu ko uku sai na sallame ki"

"Ta yaya zan haifa maka ya'yan?

Ba kunya yace"though sexual mana,kuma ko yaushe kika tuntube ni a shirye nake,dan yanda kika ganni bugu daya zan maki ki dauki dana ko yata,ni ko yanzun kika shirya duk da ba'a shirye nake ba zan iya Kokartawa"

Harara ta zuba mai tana ƙara matsawa tare da matse ƙafarta,

Ganin yanda ta haɗe kafa ta na hararan shine yasa ya saka dariya"kin ga Sumi I am just joking,wasa nake yi babu abin da zan maki,amma maganar gaskiya sai kin nime ni da kanki "

"Har a bada"
Chapter 21 · 0% Book details