← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 49

Sashe 10

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffa Bube ne yace shi zai rike gadon Jauro har ya girma,shi kuma Baffa sanda yace sam bai yarda ba sai dai a raba kowa ya rike ɗari ɗari,in yaso in ya girma sai a bashi,in kuma bai yarda ba ya tattaro mai da Jauro da dukiyar shi duka shi zai iya rike su,
Ganin fitina na kokarin kara tashi ne yasa Inna Mari tace su raba kowa ya ɗauki dari su rike mai kafin ya girma,
Sannan idan yayi sati a shiyan Binta yayi Sati a shiyan Kande,yan da aka tsayar da magana kenan,sannan yau zai fara ne da shiyan Binta,tunda dama jiya a dakin Inna Mari ya kwana tare da goggonnin shi,to suma yau zasu wuce....

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*13*

Kamar yanda suka tsara mashi haka suka barshi a shiyan Binta inda zai yi Sati ɗaya,
Bayan wucewar Goggonnin shi ne ya koma dakin Inna Mari ya zauna,dan yaje shiyan su babu kowa kuma shiyan ma a kulle yake,
Da lokacin cin abincin rana yayi kuwa haɗa masu aka yi a babban kwanu shida su Dan Fodiyo,sai dai fa kafin yayi loma ɗaya sunyi uku,dan Innar su tace karasu bari ya cinye ya bar su,su dinga yin ƙaton loma,idan ya kusa karewa su buɗe hannu su kwashe duka,
To abinda ya faru kenan a lokacin da suke cin abinci,yanda kasan da Awaki yake cin abinci haka suka mai,domin kamar basu haɗiye na bakinsu suke saka wani,gashi dama abincin bai da yawa,koda ya duba kwano tuwo ya kafe tas,amma kwata_kwata loma huɗu ya yi,
Tsayawa yayi yana kallon su ya kalli kwanun,ga kuma katon tuwo a hannun su suna gutsura suna ci,suna mashi dariya,

Hannun ya mika "ɗan Allah ɗan Fodiyo danmin tuwonka ka ga ni ban ƙoshin ba"

"Ai ni ma ban ƙoshin ba,ka dauki kwanu ka kai inna ta kara mana"

Baicimusu ba kuwa ya dauki kwanu ya shiga daki inda Binta ke zaune,ɗan rabewa yayi dan Allah ya gani yana matukar tsoron wannan matar,domin ko kaɗan bata mai ragi,

"Inna Binta ban koshi ba a ƙara min abinci"

Wani irin mugun kallo ta bishi dashi"tunda ubanka dake kabari ya kawo uwarka dake kabari ta zo ta dafa ba,ai dole kace baka koshi ba,to na waye kake son a baka,"

Kafin ma ta ƙara ɗaura mai wani zagi yayi waje da sauri ya ajiye kwanun wurin wanke-wanke,dakin Inna Mari ya shiga,a lokacin ita ma tana cin nata abincin,haka ya zauna a gefe yana kallon ta,sai da tace kusan rabi sannan tace zo ka ɗauka,ai kuwa jikin shi har rawa yake da farin ciki ya ɗauka "na gode inna"

Kallon shi tayi"ka gode me,je ka ajiye min abinci a can domin anjima shi zan ci "

Dan bata fuska yaro yayi "inna ba cewa kika yi na ɗauka na ci ba?

" Ni ko me zai sa na dauki abincina na baka bayan kaci tare da yan'uwan ka"

"Inna ban koshi ba,yunwa nake ji"

"To ai ka ga matsalar kenen,shi yasa babu kyau ka sangarta ɗa da ci,saboda halin rayuwa,iyayenka suna ganin kai kaɗai ne a gaban su sun buɗe makarantar ciki da cin abinci yanzun gashi yanda lamari ya kasance,wa zai iya ci da kai,ni dai ba zan iya ɗaukar abinci na ina baka baka ba,dan ma kar ka saka rai a kan haka,a jiyemin kwanun tuwo na a can anjima shi zan ci nima dan ba gama abinci dare da wuri za'a yi ba,in ma taga dama tace ba tayin na daren,gara na ɓoye nawa duk yanda yama to"

Bai ce mata komai ba ya ɗauki tuwon ya ajiye mata a gefe sannan ya fito,

Yana fito ya haɗu da Binta a tsakar gida,
Kallon ci tayi cikin harara wanda ta ya riga ya sani bata taba mai kallon arziki sai dai na harara ko yaushi "kai yan zun Jauro dan baka da kunya ni kake jira ka ci abinci na wanke maka kwanu,to baka isa ba,maza zo ka yi wanke-wanke kafin na canza maka kamanni,idan ka gama ka share tsakar gida,dan ni ba zan iya aiki kana zaune ina kallon ka ba kamar wani mara amfani"

Ba yanda ya iya cikin rawar jiki ya shiga tattara duk kayan da aka ci abinci har na kofar ɗakinta wanda anan ne yaga su Ɗan Fodiyo zaune a cikin dakin da ƙaton malmalan tuwo a gaba suna ci,
Bai ce komai ba dan ya fahimci ko ya roka ba samu zai ba,
Tunda yake bai taɓa yin wanke-wanke ba amma yana ganin yanda Innar shi ke yi,dan haka shima zama yayi ya fara wankewa a hankali,duk da haka wanke-wanken babba da yaro ba ɗaya ba,balle wanda bai taɓa ba ba,dan haka wasu sun wanku wasu basu wanku ba,a haka ya gama wanke-wanke,sannan ya fara shara wanda shima bai sharu da kyau ba,

Ai kuwa a kan wannan wanke-wanke da shara sai da ta zane shi sosai wai dan mugunta ne yasa yaki mata aiki da kyau,sannan tasa ya ƙara dibo ruwa tana tsaye akan shi tasa ya ƙara wanke wa,idan bai fita ba ta sakar mashi rankwashi,da haka ya gama da kuka da hawaye da majina,shara kuwa yana yi tana biye dashi da bulala a hannu,duk inda ya bar datti sai ta zauga mai tace ya koma ya share,da haka dai ya gama sharan,sannan ya lallaba ya bar cikin gidan,dan gani yake kamar kamar yana fita ya rabu da wannan bala'in na binta kenan sannan yana zuwa shiyan su zai tarar da Innar shi da kuma Baffan shi suna jiran shi,
Hakan ne yasa ya koma kofar shiyan su da aka kulle ya zauna,dan yata tura kofar taki buɗewa,zama yayi ya fara kuka yana kiran sunan Mamar shi,dan bai san inda ta je ba,
Yana cikin haka ne har barci ya dauke shi,wanda bai jima ba yaji ana ta da shi,
Bude ido yayi ya kalli me tada shi,daya ne daga cikin yaran Malam Liman,

"Jauro Malam yace kazo lokacin sallah yayi sannan za'a shiga Islamiya idan an fito sallah"

Tashi yayi ya bi ya ban yaron suka je har gidan Liman,a zauren yaron ya ajiye shi ya wuce dan shirin dauro Alwallah,
Yana shiga ya gai da Malam sannan ya zauna a gefe,
Kallon yaron yayi cikin tausayawa domin maraici ba karya bane,dubi cikin kwanaki kalilan yanda ya zube ya lalace,yasan ladan dake tattare wurin renon maraye da kuma azaban dake tattare akan wanda ya azabtar dasu ko kuma wulakansu,koda kuwa kuka mutum ya saka su,

Kwanun abinci dake gefen shi ya jawo ya mika mashi,
"Ɗauka kaci,idan ka gama ka zo ka same ni a masallaci"

Daukan kwanun yayi ya buɗe,lafiyayyen sakwara ce da miyar ganye,
Ai kuwa nan ya fara ci,hannu baka hannu kwarya,
Sai da yaji babu wurin zubawa sannan ya hakura ya ajiye sauran ya sha ruwa,

Yana fitowa ya dauki buta yayi alwalah ya shiga masallaci,in da har an tada sallah,

Suna idarwa kuma aka fara karatun yamma,wanda sai ƙarfe shida suka tashi,
Har ya fito zai koma gida,sai kuma ya koma in da Malam ke zaune yana ƙoƙarin tashi,zama yayi kusa dashi,

"Malam"ya kira sunan shi,

Shima amsawa yayi yana kallon shi,

" Malam ina Inna na da Baffa na suka je,naga shiyanmu a kulle babu kowa,kuma idan naje ina ta bugawa babu me zuwa ya buɗe min,sannan Inna Mari tace sai dai in dinga kwana a shiyan su ɗan Fodiyo,ni yaushe ne su Inna da Baffa zasu dawo,ina son in gan su,ko kuma ka kai ni in da suke"

Jikin shi gaba ɗaya yayi sanyi da kalaman yaron,dole ne ya faɗa mashi gaskiyar menene mutuwa ta yanda zai iya fuskantar gaskiyar duniya da kuma rayuwa,domin yasan ta yanda zai gina rayuwar shi........

*Nagode sosai da Addu'ar ku na ji sauki sosai yanzun kam,sannan masu jiran YAR TSANAR ZINARI zasu samu zuwa anjima insha Allah*

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*14*

Dafa kafadarshi yayi tare da sakar mashi lallausar murmushi,sannan ya kira sunan shi,
"Allah shi ya halicci komai da komai da kake gani a nan duniya,da wanda idon ka ke iya gani da wanda idanun ka ba su iya gani,mutum da Aljani,ice,sama da ƙasa,tsaunuka,rana da wata,zafi da sanyi,iskar da muke shaka,ruwa,abubuwan dake rayuwa a cikin ruwa,Jauro ina nufin komai da komai da kake gani,kuma shine yake amsar su a duk lokacin da yaso,domin ko wani abu da ka gani a duniya kome dadewar shi a duniya yana da nashi iyakar da Allah ya dibar mashi,haka ma mutum yake,duk wanda ka ga ya mutu to ya cika iya wa'adin zaman da Allah ya ɗibar mashi ne a duniya,kuma wanda ya mutu baya taɓa dawowa,"

"Malam yan zun Inna da Baffa ba zasu dawo ba kenen?

" Ba zasu dawo ba Jauro,sai dai abu ɗaya zaka masu wanda zai sa su farin ciki,su san cewa kana son su sosai kana kuma kewar su"

"Me zan yi,?

" Duk abunda zaka yi kada ka bari sallah ya wuce ka,idan ka yi sallah ka ɗaga hannu ka masu Addu'a,domin Allah mai karɓar Addu'ar bayinsa ne,idan ka masu Addu'ar zai isa gare su,kuma zasu ji daɗi su san cewa lallai Jauro na matukar son su,sai kuma ka dage kayi karatu sosai na Boko dana Islamiya,tunda naga kana da son karatun Boko,gashi kwana biyu ma ka ba je ba,gobe idan Allah ya kai mu ka shirya kabi Moha ka tafi makaranta,ina son in ga ka cika burinka,ka kuma cika burin iyayen ka,kaji Jauro ka dage ka mai da hankali,karka damu da komai da za'a yi ko za'a ce"
Chapter 10 · 0% Book details