← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 49

Sashe 31

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ita ta tashi barci ba sai kusan goma na safe,
Wanke bakin ta tayi ta fito falo in da ta samu lafiyayyen kunun gyada da kosai mai zafi acikin kula karama,
Ko ina ya samo shi ohho,ita sai ya mata daɗi sosai,
Sai dai kunun ba wani yawa ne da shi ba.

Ko kammalawa bata yi ba sai gashi ya shigo rike da babban leda a hannun shi,

Zama yayi kusan da ita"hala baki ji ina amsa sallamah?

Jinjina kai tayi tana jin daɗin kosan wanda akwai nama a ciki,"gaskiya kosan nan yana da daɗi "

"Ga kaya nan ki shirya anjima zamu fita zuwa sha ɗaya"

"Babu inda zanje dan ba zan fita da wanda bai amsa sunan shi namiji ba"

Shiru yayi yana kallon,harya ya buɗe baƙi zai yi magana,sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi,"ki dai shirya domin yau za'a bani takardar shaida zama na young professor a matsayi na na wanda bai gama cika shekara talatin ba,idan mun dawo zamu shiga kasuwa dan gobe insha Allah zamu koma"

"Ai kuwa gara mu koma ka bidar ma kanka magani"

Bai bata amsa ba ya tashi ya shige ɗaki,dan yasan idan da ace tasan menene matsar da zama zatayi ta dinga rusa ihu tana niman taimako,
Amma babu komai koma menene ke shirin tun karo rayuwar su Allah zai sa sufi karfin shi,amma maganar gaskiya jiya ba karamin tashi hankalin shi yayi ba da daddare.........

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*40*

*Wannan littafin nawa mai suna a sama na mai da shi na kuɗi,tare da Yar Tsanar Zinare,wanda yake son guda ɗaya dari uku 300,guda biyu 500 dari biyar, Hauwa Umar,Zenith Bank,2284905309,sai shaidar biyi ta wannan number 08141644865*

Yana ajiye ledar komawa yayi ya zauna kan kushin yayi shiru,idanun shi a lumshe,gabaɗaya ya rasa me ke mai daɗi,ya kuma rasa tunanin me ya kamata yayi,
Dazu moha da suka yi waya yake sanar dashi cewar Matar Baffa sanda an sake ta,wai da safe maza sun fito zasu sallah masallaci suka ganta a daure a iccen kofar gida,gaba ɗaya ta rame ta fita hankalin ta,yanzun haka tana asibiti a kwance,
Su kuma ƴan kidnapping din sun ce sai an cika masu kuɗin su sannan zasu sako Baffa sanda.

Jin motsi ne yasa ya buɗe ido yana kallon in da take tsaye,
Ba tare da wata shakka ko damuwa ba ta cire zoguwar rigar data saka dazu,ya rage daga ita sai bireziya da dogon wanda a jikin ta,

Tsabaragen mugunta irin na Sumayya sai da ta juyo suna fuskantar juna ita dashi sai dai ko kadan bata kalli inda yake ba,ta sa hannu ta ballle maɓallan bireziyar ta,

Lumshe idanunshi yayi da karfi yana buɗewa,ji yayi maƙoshin shi ya bushe,da kyar ya tattato miyon bakinshi ya haɗiye "Sun.... Sumy Baby me haka kike yi"

Juyowa tayi da kyau cikin salon iskanci ta shiga kaɗa kirji,wadanda suke a tsaye suka kallon shi "name fa?

Kauda kai yayi yana kyara zama da kyau dan ji yake tamkar ana jawoshi ƙasa daga inda yake zaune" Ki suturta jikin ki mana, baƙi ganin akwai mutum a dakin?

Kalle_kalle ta fara "ai ni banga wani mutum aciki ba face mijina" Sai kuma ta tabe baki tana wani shagwabe fuska "ko da yake mijin ma bashi da amfani tunda jiya har tayi akai masa amma ya gaza tabuka komai" Ta faɗa tana saka wata bireziyar data ɗauko,ta jawo leda kayan daya bata ta fito dashi,
Ita karan kanta ta yaba domin jallabiya ce doguwa ruwan madara ta haɗu sosai,dan ba karamin shan duwatsu yayi ba,
Tana sakawa kuwa sai gashi ya zauna a jikinta tsaf yanda ake so, shi baiyi yawa sosai ba shi bai matse ba,sannan ta nada madaidaicin gyalan a kanta,

"Anaki tunanin kenan ko?humm,Gara dai ki dinga suturtawa dan baki san sanda Damo zai waiwaye harawa ba"

"Koda ma ya waiwaye harawar sai dai ya tumurmusa baki,amma fa ada kenan,balle yanzun da ko yaje babu abinda zai iya yi balle haryaci harawar"

Daga inda yake zaune yana kallon ta ya tsince kanshi da sakin murmushi,shi mutum ne da sam baya ɓoye abinda ke ranshi ko ya kauda kai"kin yi kyau sosai Sumy Baby,yanda kikasan kin haɗa jini dasu"ya faɗa yana basar da maganar ta dan shi san baya ganin laifin ta,

Ba tare data juyo ba tace"tubarakallah,masha Allah,karka cinyeni"

Mikewa yayi tsaye yana murmushi,ya zame rigar dake jikin shi,yana ƙoƙarin cire wando ne ta juyo ta kalle shi,
"Me kake yi haka?

" Kaya zan cire"

Zama tayi bakin gado tana kallon shi ba tare data bashi amsa ba.

Ba tare da tayi tunanin zai iya ba sai gani tayi kawai ya zame dogon wandon dake jikin shi yana ƙoƙarin cire gajerin,

Zabura tayi ta mike "lallai baka da kunya yanzun kai haka kawai sai ka tube a gaba ba"

"Ba laifi bane indan miji ya tube a gaban matar shi kamar yanda matar ta tube a gaban shi,"

Turo baki tayi ta mike tana barin dakin tare da fadin "ni dai ba yar iska bace"

Cire kayan jikinshi yayi ya canja zuwa faran shadda kar da hula,sai takalmi,

Tunda take dashi wannan ne karo na farko a rayuwar ta dashi data taɓa ganin shi da kayan daya mai kyau kuma ya zauna a jikin shi,

"Tubarakallah masha Allah,hakan ya kamata ki faɗa"

Kauda kai tayi daga zuba mai idon da tayi"ai dai ko kyau ba kayi ba"

Gwalo ya mata "na dai kamaki kina kallon na ba,"

Yamutse fuska tayi tana mikewa tsaye"banga abin kallo ba anan"

Bude mata kofa yayi suka fito ya maida kofar ya kulle,
A hankali suke takawa har suka iso Bus Stop,na layin inda suka shiga,
Ita dai sai kalle kalle take yi har Bus din ya tsaya,suka sauka,nan ma basuyi wani tafiya mai nisa ba suka iso wani babban ɗakin taro wanda yake cike da mutane,
Domin su komai akan lokaci suke yi,
Suna shigowa wani Bature ne ya taso da sauri yazo in da suke,gani tayi sun rungume juna su,sai kuma taji nan take ya juya harshe cikin kwarewa yake magana da Turanci,
Abinda bata taba zata ba,har yanzu ba zata iya cewa waye asalin mijin da take aure ba,ta dai san sunan shi,amma wasu abubuwa nashi baza ta iya kararwa ba,

Wani kujera na musamman taga an nuna masu inda zasu zauna,

Suna zaune sai ji tayi an kira sunan shi,sai kuma taga mutane sun shiga tafa mashi,
Ita kallon su kawai take tamkar wata wawuya domin in tace tana fahimtar duka abinda suke fada tama Allah ƙarya,sai dai abinda ba'a rasa ba,

Taga kuma wani dattijon Bature ya bashi wasu takardu da kuma wani abu kamar a Glass anyi rubutu aciki,sai ɗaukarsu hotuna ake yi ta ko ina,
Daga karshe kuma JAURO yayi godeya da bayani sosai a harshen Turanci,

Ji tayi jikinta yayi sanyi,ta raina kanta,kalli irin hadaddun matar dake ta zuwa suna tayashi murna,basu damu da kalar shi ba ko shigar shi,

Shi yasa bai da kyau ka kyamace mutum saboda bai da wani abu,domin ta iya yuwa kai ma akwai abinda baka dashi amma shi Allah ya bashi,

Gani tayi ya mata alama da hannu alamun ta zo,

Tasowa tayi tazo inda yake tsaye tare da wadanda aka basu shaida tare,hotuna sosai aka shiga dauka,sannan yana ta nuna ma abokin shi ita amatsayin mata,

Dole dai tayi masu yake,sannan ta gaisa dasu da ɗan Turanci da take ji.

Sun dan jima sosai a wurin kafin su fito,
Tayi tunanin gida zasu koma,sai dai kasuwar garin taga sun nufa dashi inda anan tayi kallon abuwa iri-iri,

Kallon ta yayi"Albarkacin farin cikin da nake ciki a wannan ranar,ki ɗauka duk abinda ya maki zan biya kuɗin "

Zaro ido tayi "kana nufin da gaske?

" In baki so mu tafi"

Tsabar farin ciki yasa bata san sanda tayi tsalle ta rungume shi ba"waiyo Jauro na gode "

Gani tayi da sauri ya cire ta a jikin shi yana matsawa baya kaɗan, "ba sai kin taɓa ni ba "

Dakatawa tayi tana kallon shi har ya shiga fiffita da hannun shi kamar mai jin zafi,

"Me yasa baka son in taɓa ka"

Da sauri ya sake murmushi "is that necessary?

Sake fuska tayi tana jawo wani doguwar riga " Wow,gaskiya wannan zai ma Mama kyau sosai,
Ba karamin yawo suka yi ba,ta zaɓar ma Aisha da Aunty Amina kaya,harma da Salma,
Har zasu wuce ta hango shagon da ake sai da kayan maza,"Jauro muje shan shagon "

Kallon kwalayen dake hannun shi yayi"kinga lokacin sallah har tayi baki gama ba"

"Ɗan Allah mana,wannan ne na karshe"

Tsaki yayi,yasan dai bai wuce Babanta zata daukar ma tsaraba,suna shiga ya samu wuri ya zauna,"kiyi ki gama mu tafi"

"Ok " Ta fada tana ƙarama shiga cikin shagon sosai,
Bai san kalan kayan data siya ba sai da ya je biyan kuɗi yaji kudi masu yawa ga kuma kwalaye sun kai biyar,"Sumy Baby gaskiya ki rage kayan nan kudi yayi yawa"

Bata fuska tayi "kaifa kace na dauki duk abinda nake so,zaka biya,me yasa zaka canja maganarka yanzun?

Kauda kai yayi yana sauke numfashi,tare da basu umurnin su cire kuɗin.

Haka suka dawo gida da kaya niki_niki,haka ta dinga cirowa tana dubawa,tana kuma ninkewa tana jerawa a babban jakkan da suka siya.

__________Nigeria.

Dariya take ta fama tuntsira yanda kasan wacce ta ga wawan zama,

Matar dake gefen ta ne tace"wai daga magana ke kuma sai ki hau dariya kamar kin samu shashashai "

Tsagaitawa tayi"ke kuwa ya za'ayi ba zan yi dariya ba,kin taba ganin shashashar uwa da batasan in da ƴar ta ke aure ba,"

"Naji tace a Tunga aka kai ta,ko ba haka kika ce ba Maman Aisha" Matar ta faɗa tana kallon inda Mama ke zaune.

"Haka ne Goggon su"

"Kensan ni ban samu naje bikin bane shi yasa nake son naje naga gidan a matsayina na kanwar mahaifinta"
Chapter 31 · 0% Book details