← Book details Jauro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 49

Sashe 5

Jauro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Asalin Ahalin*
Asalin Kakanshi shine Abdul Aziz,wanda ya kasance Ba'adare Bafullatani ne,wanda ya tara dukiya na Dabbobi daya gada a wurin iyayenshi,
Yana zaune ne a can wani ƙauye tare da Yayanshi guda biyar,maza uku mata biyu,,
Danshi na farko shine,Baffa Sanda,sai Baffa Dottiya,sai Baffa Bube,sannan gwogo Badejo,da kuma gwogo Halira,
Ada iyayensu ma'abota tashi ne daga wannan garin zuwa wannan kafin su tsaya a gari daya,wannan yasa gabaɗaya yaran nasu ba abinda suka sani dangane da Addini daya wuce noma da kiyo,
Haka ma iyayensu,
A tare da yaran babu wani shakuwa ko nuna soyayya irin ta ƴan uwantaka,babu ragi ko kadan a tsakanin su,idan daya daga cikin su yama ɗan uwanshi laifi to uwarsu zata ce lallai sai ɗayan ya rama dan yana dan wanshi bai isa ya masa yaki ramawa ba,da haka tarbiyarsu ta taso babu ragi a tsakanin su,kamar yanda babu sabo ko shakuwa a tsakani,
Ana cikin haka ne Allah ya fara dauke Abdul Aziz wanda suka fi kira da JAURO,daga baya ne suka tashi daga wurin da suke suka yanka tafkeken fili a nan Cancaga,aka kuma raba masu Gabon su kamar yanda suka buƙata,
Kowanne ya samu shanaye da suka kusa tasanma rabin garke a cikin su,Matan ma aka ba kowacce nata tayi gidan mijinta dashi,domin suna shekara goma sha biyu JAURO ya auran da kowacce,

Baffa Sanda ne yafa yin aure inda da ya aure wata Bafullatana mai suna Kande,sai da yayi haihuwa daya kafin Baffa Dottiya wanda yake Mahaifi a wurin Jauro,

Ada kafin auren Baffa Bube suna dan lallaba yanayin zaman nasu,duk da ba kasafai suke kula da lamarin juna ba, amma lamarin nasu da ɗan sauki,
Domin Kande matar Baffa Sanda tana da Yara Biyu,daya ana kiranshi da Dotti,daya kuma Yabbale,
Sai matar Baffa Dottiya wacce a lokacin ɗan ta daya mai suna Abdulaziz suna mashi lakabi da sunan kakanshi Jauro,

Tun daga lokacin da Baffa Bube ya auri matarsa mai suna Jabbi,ta tako cikin gidan da suna matar gidan,tun daga wannan rana duk wani farin ciki da ya ɗanyi saura a cin gidan ya karasa tarwatsewa,duk wani kwanciyar hankali dake gidan ta karasa koranshi,ta maida gidan filin yaƙi da farauta,ta hana kowa zaman lafiya ciki kuwa har da ita karan kanta,ta kara zama wata muguwar shaidaniya..............

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*7*

Zuwan Binta da kwana uku ta haddasa fitinar da tasaka sai da aka raba babban gidan da suke zaune kashi uku,domin kuwa a ranar ne ta je ta samu Baba Mari,mahaifiyarsu da kuka cewar wai tana cikin wanka sai taji ana lekenta tun da tazo,to shine yau Allah ya bata sa'a ta kama wanda yake leken ta,sai dai taji tsoro da ganin wanda bata yi zata ba,wato yayan mijinta Sanda,gaskiya ba zata iya zama ba zata koma gidan su ne ta fada tana kara fashewa da kuka,

Hankalin tsohuwa ya tashi,ranta yayi mugun bace,domin kuwa a garesu abin kunya ne babba ace daga aure amarya ta gudu,kuma dalelin kasancewa wai sai aji yayan mijinta ke lekenta idan tana wanka,dan haka cikin gaggawa tace maza a nimo mata Sanda yanzun nan,
Haka kuwa aka yi,yana zuwa ya duka a gabanta yana gaishe ta da harsher Fullanci,kin amsa shi tayi,wanda hakan ba ƙaramin mamaki ya bashi ba,dan yasan koda safe lafiya suka rabu,

"Inna lafiya" Ya tambaye ta.

Cikin masifa tace"wani irin abin kunya kake kokarin janyowa zuri'a ta,yanzun saboda rashin gode Allah matarka bata isheka ba har sai ka haɗa da na dan uwanka,wacce ko kwana uku bata cika ba a gidan nan,dama haka halinka yake bamu saniba sai yanzun Allah ya toni Asirin ka "

Duk wannan maganganun da take yi kanshi ba ƙaramin kullewa yayi ba,to me kuma ya haɗa shi da matar dan uwan shi,wacce bai ma ko gama tantance fuskarta ba,
Dago kai yayi da zummar yi mata tambaya,sai dai ji yayi an shakoshi anyi wurgi dashi a tsakar gida,an kuma bishi da sanda ana ƙoƙarin rafka mashi akai,wanda da badan yayi sauri cikin zafin nama ya kauce ba daya raba mashi kai biyu,
Cikin mamaki yake kallon dan uwan shi Bube,
"Me haka Bube,me na maka ne haka "

Har wani huci yake fitarwa na bacin rai yana nuna ɗan uwan nashi"yanzun ni zakaci amana Sanda,ni zakaci amana ka dinga labewa kana kallon tsiraicin mata na saboda baka tsoron Allah,to yau sai na ga bayan ka"ya faɗa a zafafe yana nufarshi,

Oh sai yanzun ya fahimci inda maganar ta dusa,shima nan take ranshi ya motsa,ya kalle dakin da Inna ke zaune tana bantalar goronta hankali kwance,yayin da Binta ke kofar inna tana kallon rigimar da suke yi,
Sai matarshi Kande wacce shigowar ta kenan daga dibo ma dabbobi harawa wadanda ba'a fitar dasu kiyoba na mijinta,
Ganin abinda ke faruwa da kuma jin furucin Bube yasa cikin kidima ta zubar da abin dake hannunta tanufe dakin inna da gudu tana kuwa,tsugunnawa tayi a gaban ta "dan Allah inna ki shiga tsakani ki raba wannan fitinar"

Ture ta tayi"ɗan Allah matsa can,ke yazun ba abin kiyi Allah wadai bane da Abinda mijinki ya aikata,matar dan uwansa da ya kalla,"

Cikin kuka take girgiza kai"wallahi ba halinsa bane,ba halin Sanda bane,na tabbata ba zai aikata haka ba"

"Ka jimin munafukar yarinya,har ni zaki faɗa ma halin ɗa na,yaron dana raine shi tun kafin ki haɗu dashi,,to sai kije kiyi duk yanda zaki yi dasu ni dai bani daddakawa daga nan"ta faɗa da masifa,

Cikin tashin hankali ta nufe inda Binta ke zaune tana kuka ta rike hannunta " Dan Allah Binta ki faɗa gaskiya domin nasan hakan ba zai taba faruwa ba,na yarda da mijina na kuma yarda da halinshi,"

Ture hannun ta dake saman nata tayi"kenan kina tunanin karya na ma mijin ki ko me,to bari kiji,ko ki yarda ko karki yarda abinda ya aikata min kenan,kuma sai miji na yau daukar min fansa"

Daga bayanta taji ance "fansar me za a ɗaukar maki"

Duk juyawa suka yi,suna kallon ta,gabaɗaya ta kere su tsayi da girman jiki,macce wacce take a tsaye,ga kazar_kazar,wato Halima kenan matar Baffa Dottiya,

Kallon cikin idanun Jebbi tayi,tana nunata da yatsa"ke daga ganin waɗannan idanun naki akwai munafurci da makirci a tare dasu,da yaushe mutumin da baya zama gida ya leka ki kina wanka"

Cikin tashe rashin kunya da nuna eh ba tsoronki nake ba tace"idan bai lekaba sai akayi ya,ko zaki shigar mashi ne,dan ni ban shigo gidannan da tsoron kowa ba"ta faɗa tana nunata da yatsa,

Ba zato ba tsammani sai ji tayi an kama yatsan an riƙe,sai kuma raji an juya,kafin ta fahimci me take kokarin yi sai jin wani azaba tayi ya ratsa ƙwaƙwalwar ta ya sauko saman ɗan yasan daya bada sautin Kas sannan ta sake,

Dago hannun tayi tana kallon yanda yatsar ya kwanta yana lilo,alamun kashin dake rike shi ya ƙarfe,

Wani ihu ta zunduma tana faduwa kasa tana birgima tare da rike hannun ta,
Jin ihun matar tashi ne ya saka da sauri yayi jifa da sandar dake hannun shi wanda ye kaiwa Baffa Sanda hari dashi,shi kuma yana goshewa domin ba shida abin da zai kare kanshi,har kuma ya samu damar samun shi a hannun wanda wurin tuni ya kumbura,

Dago ta yayi yana riƙe hannun tare da tambayarta lafiya,cikin kuka da ihun azaba take nuna mashi Halima dake tsaye tana masu kallon uku saura kwata"wannan maiyar ce ta karya min hannun,kalla ka gani,waiyo shi kenan zan zama mai yatsu huɗu kenan"

Da sauri Inna Mari ta fito,"ke Halima me ta maki kika karya ma yar mutane hannu"

Sai da ta harari gefe tukunna kafin ta kalli Inna ido cikin ido tace"yatsa ta nuna min,ni kuma naje sauke mata sai aka samu akasi domin ashe kashinta bai da kwari,kinsan Inna ni ban cika son ana nuna min yatsa ba,"

Ganin duk sun tsaya suna kallon ta ne yasa ta kuma cewa"nifa ba da gangan nayi ba,Inna kawo hannun ki in nuna maki yanda na mata,zaki tabbatar da kashinta ne bai da kwari"

Da sauri inna ta mai da hannun ta baya ta juya tana korarin shiga daki tare da faɗin,"dama Awala hakkillo,"ta fada tana karasa shigewa daki tare da sauke labulen dakin ta,dan sarai ta san halin Halima ba cikakken hankali gare ta ba,dan tana tare da mugun iskokai idan ka yi rashin sa'a kuna cikin hayaniya da ita suka tashi to kashiga uku,domin cutar rabkuwa suke saka mata,wato idan ta rike mutum zata ringa rabkashi da kasa ne yanda kasan ana bugun fulawa,kuma ta taba rabka inna Mari wacce sai da aka mata ɗaurin haƙarƙari shi yasa duk cikin sirikanta tafi shakkar Halima....

*Na yi kuskure a sunan matar Baffa Bube mai suna Jabbi,yanzun sunan ta Binta*

*🍂JAURO🍂*
(MAI ANGUWA)

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*8*

Ganin irin kallon da take masu ne yasa bai ce mata komai ba ya kama hannun matar shi dake ihun hannunta ya taimaka mata ta mike sannan suka bar wurin,

Da sauri Kande ta karasa wurin da mijinta ke tsaye tana rike hannun shi,

Daga inda take tsaye tana kallon su amma bata San me suke fada ba,dan haka kaɗa kai kawai tayi ta koma dakin ta,
Chapter 5 · 0% Book details